Jami'an tsaro sun cafke mataimakin shugaban wata jami'a a kasar Zimbabwe Levi Nyagura, bisa zarginsa da hannu a dambarwar da ta kunnu kai kan ba wa matar tsohon shugaban kasar Grace Mugabe, takardar shaidar kammala karatun digirin digirgir.
An dai ba ta wannan digiri ne alhali watanni kalilan ta yi ta na karatu, kuma sai a watan da ya gabata ne aka wallafa kundin binciken da ta yi, a dai-dai lokacin da ake kirayen a karbe digirin ba ta cancance shi ba.
Abin da ba a bayyana ba shi ne ko ita ma Misis Grace Mugaben, za a cafko ta don fuskantar tukumar.
Maimakon yadda aka san masu karatu mai daraja irin wanda aka bata da shafe shekara da shekaru kafin kammalawa da karbar sakamako, ita na ta ya kammala ne cikin dan takaitaccen lokaci.
Wasu bayanai da suka kara fitowa ma shi ne, baki daya tun daga yin rijista a jami'ar da fara daukar karatu, da zana jarrabawa, da rubuta kundin bincike da ma ba ta takardar shaidar digirin digirgir din, lokacin da ta dauka bai wuce watanni biyu zuwa uku ba.
Ita dai Grace Mugabe, ta so ta gaji mijinta Robert Mugabe ne, a matsayin shugabar kasar Zimbabwe, amma hakar ta ba ta cimma ruwa ba inda a watan Nuwambar bara sojin kasar suka hambarar da gwamnatinsa kamar yadda 'yan kasar suka da de su na fata, yayin da ita kuma ta tsere daga kasar tun ma kafin sojojin su kawo karshen gwamnatin mista Mugaben.
bbchausa.

Tirkashi: Ga wata me kwakwalwar Kwamfuta: Ta kammala karatun digirin digirgir a watanni 3 kacal >>bbchausa

No comments