Tauraron fina-finan Hausa, Adam A. Zango ya kara fitowa fili yayi cikakkaen bayani akan irin matsalolin da yake so ya kawo gyaransu a masana'antar fina-finan Hausa, Adamun yace wasu masu shirya fina-finai suna bautar da jarumai ta yanda zasu yi aiki amma aki biyansu ladan aikinsu.Adamun yace har kara irin wadannan jarumai sun kaiwa hukumar tace fina-finai ta Kano amma babu wani mataki da aka dauka akan lamarin.
Gadai abinda Adamun ya bayyana kamar haka:
"
A Yau wasu daga cikin Jarumai MAZA da MATA tsofaffi da manya da kananan da wani bangare na Maaikata a kannywood. Suka kai kara da kukan wasu manyan producers da kananan su.! Gurin Hukumar tace fina-finai. Kan abin da suke kira danne hakki da mugunta da producers din suke musu.
A cewarsu mafi yawan ayyukan da suke da producers din basa biyansu ko kuma in zaa biya ka a baka kudin da ko na mota bazai kai ba. Ko ayi kwanaki ana aiki da kai, in an gama ace za'a kiraka, shikenan an cinye. Tabbas duk abin da mutum sama da Ashirin Mata da maza suka fada, to lallai yana faruwa. Kuma hakan zalincine .
Allah bazai kyaleba.. Yaku masu wannan dabiar, ku sani an wuce lokacin bauta. Wadanda kuke bautarwa Allah sai ya saka musu. Kuma Wallhi sai kun biya su hakkin su a ranar da baku da komai sai abin da kuka jewa Allah dashi. Ina rokon wasu daga cikin Directors, Actors, Actresses, writers da producers. Mu hadu domin kawo karshen Wannan zalinci. Duk wanda aka samu a karbi hakkin wanda yaci kuma a hukuntashi. Muyi domin Allah bada nufin tozarci ko cin Zarafin juna ba. Sai Dan tsaftace Masana'anta daga hannun baragurbi. Ka fara daga set din da kake. Duk wanda kaji ba'a biya ba, ka dakatar da aikin har sai an biya hakkin mutane sannan a cigaba. Domin ni nasan ba'a film sai da kudi.
The Wallhi duk KABON wanda kaci ka shirya sauraran hukunci tun daga kabari.
Allah ka tsaremu da zalinci da cin dukiyar wadanda suka wahaltamana. Ameen."

"Ana bautar da jarumai a masana'antar fina-finan Hausa">>Adam A. Zango

No comments