Labarin Zion ya taba zukatan mutane da dama domin kuwa duk da kalubalen da ya fuskanta a rayuwarshi be yadda ya zama nauyi akan mutane ba, ya tashi tsaye dan ganin ya zama abin alfahari ga jama'arshi.
Allah me yin yadda yaso, wani sai yayishi da cikakkiyar halitta da lafiya, wani kuma yayishi da kudi amma ya kwace lafiyar, wani kuma yana cikin rayuwar za'a canjamai fasali, wannan bawan Allahn me suna Zion Clark dan kasar Amurkane da aka haifeshi babu kafa saidai kuma wannan be hanashi yin hobbasa dan cimma burin rayuwarshi ba.Bayan kasancewar Zion bashi da kafa, kuma ya tasone a gidan riko, yanzu dai yana makarantar sakan direne kuma yana yin wasan kokawa wanda dama shine burinshi.
No comments