Kungiyar IZALA mai wa'azin musulunci, wacce ke kafa sunnar Annabi mai tsira da aminci tare da fatattakar bidi'ah, karkashin jagorancin shugaba Sheikh Abdullahi Bala Lau ta bude katafaren ofishi (JIBWIS LIAISON OFFICE, MAKKA) a unguwar KHAKIYYA dake cikin birnin Makkah domin ci gaba da ayyukan Da'awa.
A cikin bayanan sa, shugaban JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau yace an bude wannan office dinne domin ayyukan wa'azi da wa'azantarwa Wanda kungiyar ta dauki shekara da shekaru tana gabatarwa. "Wannan office zai hada kusan dukkan kasashen duniya wadanda suke da alaka da Ahlussunnah, domin Ya zama mahada na tattauna ayyukan Da'awar sunnah a wadannan kasashe" Inji Shi.
Kazalika Za'aci gaba da shirya wa'azuzzuka a unguwannin dake cikin makkah, domin karantar da mutanen mu dake yankin, kuma a ci gaba da bin Alhazai ana musu wa'azi a lokutan aikin Hajji da Umrah.
In ba'a manta ba a baya gwamnatin saudiyya ta baiwa kungiyar IZALA lasisin gabatar da wa'azi a cikin garin makkah da kewaye.
A karshen karshe shugaban ya bude office din da sunan Allah, Wanda kuma nan take ya fara aiki, tare da tabbatar da zai kasance a bude a ko wane lokaci insha Allah.
A karshe Sheikh Lau ya umurci Malaman da sukazo Aikin Hajji da Su sanya kasar Naijeriya, da shugabannin ta cikin addu'oin zaman lafiya, tare da zaba mana shugabanni na gari a lokacin babban zabe. Mai zuwa
An samu halartan Shugabannin kungiyar irin su Sheikh Yakubu Musa, Sheikh Kabiru Gombe, Sheikh Abubakar Giro Argungu, Imam Mustapha Imam Sitti, Dr. Ibrahim R/Lemo, Dr. Ibrahim Idris Darus-sa'ada, Dr. Abdulkadir Kazaure, Sheikh Umar Jega, shugaban IZALA ta jihar Kebbi, Sheikh Isa Aliyu Jen, Alaramma Isma'il Maiduguri, Darakta JIBWIS Project, Eng. Ashiru Babandede da sauran wakilan shugabannin jihohi, wakikan kasa, 'yan agaji da sauran Hariri jama'a.
Allah ya sanyawa wannan office Albarka, ya kuma albarkaci wannan kungiya mai tarun albarka.
Sarauniya.

Kungiyar IZALA ta bude Ofis a birnin Makkah

No comments