Sanatan dake wakiltar Kaduna ta Tsakiya Sanata Shehu Sani ya yi tattaki na musamman zuwa garin Daura domin ganawa da shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa babban makasudin kai wa shugaban kasa ziyara shine domin a samu a dinke barakar da ke jam’iyyar a musamman a jihar sa ta Kaduna da kuma yadda jam’iyyar zata tunkari zaben 2019.
Bayan ganawar da suka yi a cikin sirri, Shehu Sani ya bayyana wa manema labarai cewa ya tabbatar wa shugaba Buhari bisa goyon bayan sa da na mazabar sa 100 bisa 100, da kuma tabbatar masa da ci gaba da zama a jam’iyyar APC daram dam.
” Na zo Daura ne domin in shaida wa Buhari cewa ina tare da gwamnatin sa da kuma Jam’iyyar APC sannan sai inda karfi na ya kare wajen ganin ya sake darewa kan karagar mulki a 2019.
” Ina ci gaba da zama a APC ne bawai ko don an gyarota tsakanina da jam’iyyar APC a jihar Kaduna ba, ina APC ne har yanzu don Buhari da kan sa da kuma uwar jam’iyyar ta kasa sun saka baki akai.
” Babu wani dan Adam da bashi da matsala da wani, sai dai kuma idan aka zo maganan ci gaban kasa dole kowa ya mai da wukar sa a bi abu daya.
Da aka tambaye shi ko shi ma an yi mai alkawarin tikitin tazarce, Shehu Sani ya ce, ko a can baya yana da matsala kan wannan batu, sai dai jam’iyya ta ce za ta saka wa wadanda suka yi mata biyayya.
Ya ce duk da akwai alkawarin saka wa ‘ya’yan jam’iyyar da suka yi wa jam’iyya biyayya, dole kuma a tabbata an bi yadda tsarin dokar jam’iyya ta gindaya.
” Yanzu dai ba maganar ba mutum tikitin tazarce bane a gaban mu, a samu ayi zabe lafiya cikin kwanciyar hankali shine ya kamata mu sa a gaba.
” Sannan ina kira ga mutane da su jingine maganar banbance-banbance na kabilanci, addini da na al’ada a gefe, mu sa kasar mu daya a gaba domin samun nasara da ci gaba.” Inji Shehu Sani.
Premiumtimeshausa.

No comments