Sabuwar Wakar Hamisu Breaker Me suna Taka Rawa
GA KADAN DAGA CIKIN BAITOCIN WAKAR
– Takarawa x4
– Takarawa Tunda dai Breaker nazo
– Inda rabo se rago yakoma Gworzo
– Mai nema wattarana baicin kanzo
– Kar mu biyewa Wanda Ke tunanin fama
– Mai nutsuwa Ke sanin bayanan kurma

Downlord mp3

©Wakoki

Sabuwar wakar Hamisu Breaker – Taka Rawa

Shugabannin Izala Da Na Darika Zaune Wuri Guda Suna Hira A Yayin Aikin Hajji
HOTO MAI DAUKE DA DARASI
Shugaban Izala na kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau tare da Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi (dan Sheikh Dahiru Bauchi) da Sakatare Janar na Darikar Tijjaniyya Sheikh Tijjani Bala Kalarawiy da Sheikh Kabiru Gombe da kuma Sheikh Yakubu Musa inda suke tattaunawa ta Ilimi cikin wasa da dariya da kuma mutunta juna.
Allah ya kara hada kan musulman Nijeriya.
Rariya.

Shugabannin Izala Da Na Darika Zaune Wuri Guda Suna Hira A Yayin Aikin Hajji

Sanannen abu ne a kusan kowanni kabila ko addini cewa aure muhimmin abu ne, kuma ita cikar kamalar mutum mace ko namiji, hakan ta sanya aure ya fi zama cancanta ga shuwagabanni, don haka zaka ga da zarar wani ya samu mukami sai yayi aure, ba duka aka zama daya ba, inda a Najeriya aka samu wasu manyan sarakuna dake mulkin manyan masarautu amma basu da aure, ku biyo mu.
Wadannan sarakunan basu da aure har yanzu, duk da suna gudanar da mulkin dubunnan al’umma.
Sarkin Gombe
Sarkin Gombe, mai martaba Alhaji Abubakar Shehu na Uku ya dane mukamin Sarki kuma shugaban majalisar sarakunan jihar Gombe ne yana shekaru 39 bayan mutuwar mahafinsa, Alhaji Sheu Abubakar kimanin shekaru uku da suka shude.
Sai dai duk da cewa a yanzu haka yana da shekaru 42, amma Sarki Abubakar bai taba aure ba, kuma bashi da mata a ko ina, a duk fadin jihar Gombe da ma Najeriya gaba daya, wanda hakan na damun al’ummar jihar Gombe.
Majiyoyi sahihai sun tabbatar da cewar a yayin da za’a nada shi sarautar Sarkin Gombe, an so a daura masa guda daga cikin yayan Sarkin Musulmi amma abin bai yiwu ba, haka zalika aurensa da diyar Sarkin Dukku, Gimbiya Aisha Musnan saura kiris, amma abin bai yiwu ba.
Amma duk da wannan nakasu, Sarki Abubakar yana da kyakkyawar alaka da jama’ansa, talakawansa na kaunarsa sakamakon taimakon dayake musu.
Sarkin Ife (Ooni Ife)
Sarkin Ife na daga cikin matasan sarakuna a Najeriya, kuma shine shugaban majalisar sarakunan jihar Osun gaba daya, yayi aure har sau biyu, amma auren bai dade ba, aurensa na karshe a ranar 12 ga watan Maris na shekarar 2016 aka yi, inda ya auri Sarauniya Wuraola Zaynab Otiti Obanor, amma suka rabu a shekarar 2018.
Tun bayan wannan mutuwar aure wanda hatta sadakin daya biya saida aka dawo masa dasu, Ooni mai shekaru 43 bai sake wani auren ba, sai dai ana samun jita jitan cewa ya kusa angwancewa, inda ake danganta shi da Sarauniyar Kyau Tobi Philips.
Sarkin Agbor (Dein Agbor)
Dein na Agbor, Sarkin masarautar Agbor dake jihar Delta, Benjamin Ikechukwu Kiagborekuzi I shine wanda ya zama Sarki tun yana karamin yaro dan shekara 2, 1979 bayan rasuwar mahafinsa, a yanzu yana da shekaru 42 amma shima har yanzu bashi da mata.
Dayake Benjamin ya dade a kasar waje yana karatu, don haka tun bayan dawowarsa Najeriya a shekarar 2001 ake zargin wai buduwarsa baturiya zai aura, amma mambobib majalisarsa sun ce atabau ba zai auri baturiya ba, yar kabilar Agbor zai aura.
Sai dai shima Basaraken yana da girma sosai a idon jama’ansa, suna matukar kaunarsa tare da mutunta shi.
Sarkin Ubulu-Uku (Obi Ubulu-Uku)
Sarkin al’ummar Ubulu Uku dake jihar Delta, Oba Chukwuka Akaeze I ya dare karagar mulki ne a shekarar 2016 yana dan shekara 15 bayan miyagu masu garkuwa da mutane sun kashe mahaifinsa Edward Ofulue III, ma’ana yanzu shekararsa 17, inda ya kwashe shekaru biyu yana mulkar jama’a amma bashi da aure.
Amma a iya cewa karancin shekaru ne suka hana Oba Akaeze aure, don kuwa a yanzu haka yana kasar waje yana karatu, kamar yadda jaridar Aminiya ta ruwaito.
Naij.com

Manyan sarakunan Najeriya guda 4 da ba su da aure

Adam a zango
 Tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango kenan a wadannan hotunan nashi daya sha kwalliya irin ta gayun zamani, an dan kwana biyu ba'a ji duriyarshi ba a dandalinshi na sada zumunta sai yanzu.

Hotunan Adam A. Zango dan kwalisa

 Kungiyar IZALA mai wa'azin musulunci, wacce ke kafa sunnar Annabi mai tsira da aminci tare da fatattakar bidi'ah, karkashin jagorancin shugaba Sheikh Abdullahi Bala Lau ta bude katafaren ofishi (JIBWIS LIAISON OFFICE, MAKKA) a unguwar KHAKIYYA dake cikin birnin Makkah domin ci gaba da ayyukan Da'awa.
A cikin bayanan sa, shugaban JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau yace an bude wannan office dinne domin ayyukan wa'azi da wa'azantarwa Wanda kungiyar ta dauki shekara da shekaru tana gabatarwa. "Wannan office zai hada kusan dukkan kasashen duniya wadanda suke da alaka da Ahlussunnah, domin Ya zama mahada na tattauna ayyukan Da'awar sunnah a wadannan kasashe" Inji Shi.
Kazalika Za'aci gaba da shirya wa'azuzzuka a unguwannin dake cikin makkah, domin karantar da mutanen mu dake yankin, kuma a ci gaba da bin Alhazai ana musu wa'azi a lokutan aikin Hajji da Umrah.
In ba'a manta ba a baya gwamnatin saudiyya ta baiwa kungiyar IZALA lasisin gabatar da wa'azi a cikin garin makkah da kewaye.
A karshen karshe shugaban ya bude office din da sunan Allah, Wanda kuma nan take ya fara aiki, tare da tabbatar da zai kasance a bude a ko wane lokaci insha Allah.
A karshe Sheikh Lau ya umurci Malaman da sukazo Aikin Hajji da Su sanya kasar Naijeriya, da shugabannin ta cikin addu'oin zaman lafiya, tare da zaba mana shugabanni na gari a lokacin babban zabe. Mai zuwa
An samu halartan Shugabannin kungiyar irin su Sheikh Yakubu Musa, Sheikh Kabiru Gombe, Sheikh Abubakar Giro Argungu, Imam Mustapha Imam Sitti, Dr. Ibrahim R/Lemo, Dr. Ibrahim Idris Darus-sa'ada, Dr. Abdulkadir Kazaure, Sheikh Umar Jega, shugaban IZALA ta jihar Kebbi, Sheikh Isa Aliyu Jen, Alaramma Isma'il Maiduguri, Darakta JIBWIS Project, Eng. Ashiru Babandede da sauran wakilan shugabannin jihohi, wakikan kasa, 'yan agaji da sauran Hariri jama'a.
Allah ya sanyawa wannan office Albarka, ya kuma albarkaci wannan kungiya mai tarun albarka.
Sarauniya.

Kungiyar IZALA ta bude Ofis a birnin Makkah

Jarumar fina-finan Hausa, Teema Makamashi na murnar zagayowar ranar haihuwarta, muna tayata murna da fatan Allah ya karo shekaru masu Albarka.

Zafafan Hotunan Jaruma Teema Makamashi Dasuka KayatKayatar

Tauraron mawakin Hausa, Aminu Alan Waka kenan tare da shugaban sojojin Najeriya, Tukur Yusuf Buratai a wannan hoton, muna musu fatan Alheri.

Alan Waka ya hadu da Buratai

Kwallon Cristiano Ronaldo da ya ci Juventus da watsiya lokacin yana Real Madrid a wasan kusa dana kusa dana karshe ce tazo ta daya a kwallaye mafi kyawu da akaci a gasar cin kofin zakarun turai da aka kammala.
Bayan sanar da cewa kwallon tashi ce tazo ta daya, Ronaldo ya fito ta dandalinshi na sada zumunta ya godewa masoyanshi da suka zabi kwallon a matsayin ta daya, ya kuma ce bazai taba mantawa da wannan lokaci ba, musamman abinda masoya kwallon sukayi a lokacin.
Bayan cin wannan kwallo dai masoyan kungiyar ta Juventus sun tashi tsaye sannan suka tafawa Ronaldo akan wannan kwallon duk da cewa su akaci.

Kwallon da Ronaldo yaci da watsiya tazo ta daya

Wannan al'amari ya faru ne a garin lokoja. Inda rana ta kwace wa wani Malamin coci. Wanda ya yi kaurin suna wajen haÉ—a baki da mutane su yi haukan karya, shi kuma ya warkar da su, a ba shi kuÉ—i.
Sai dai a ranar sa'a ta kwace masa inda ya yi arangama da wani mahaukaci tuburan. Ko da faston ya zo kusa da shi don karanta masa adu'o'in kirista, kawai sai ya tasam masa da duka ya yi masa lillis. A hoton za mu iya ganin mahaukacin sanye da bakar riga.
Sarauniya.

Fasto Ya Ci Na Jaki A Lokacin Da Ya Yi Kokarin Warkar Da Mahaukaci.

 Tauraruwar fina-finan Hausa, Hafsat Idris na daga cikin wadanda sukayi aikin Hajjin Bana na 2018, ta saka wadannan kayatattun hotunan nata da ta dauka a kasa me tsarki a sandalinta na sada zumunta.
Muna fatan Allah ya amsa Ibada ya kuma dawo dasu gida Lafiya.



Hotunan Hajiya Hafsat Idris daga kasa me tsarki

Maryam Gidado tasha ruwan Allah wadai akan wannan hoton
 Tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Gidado kamar kowace jarumar fim din Hausa, takan saka hotuna lokaci zuwa lokaci a dandalinta na sada zumunta kuma masoyanta sukan yaba, saidai a wannan lokacin labari ya sha ban-ban, dan kuwa wannan hoton ya jawo mata surutai daga masoyan nata.
Da dama da suka bayyana ra'ayoyinsu akan wannan hoto sun ce bai dace ba sam musulma ta dauki irin wannan hoto haka kuma har ta nunawa Duniya.
Gadai wasu daga cikin ra'ayoyin mutane akan wannan hoton:





Maryam Gidado tasha ruwan Allah wadai akan wannan hoton

 Yau kwana goma sha hudu kenan da rasuwar mahaifiyar tauraruwar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi, muna fatan Allah ya kai Rahama kabarinta. Nafisar ta saka wadannan hotunan nata a dndalinta na sada zumunta saidai wasu na ganin cewa yayi wuri ace ta fara mantawa da rasuwar mahaifiyartata.
Wani, ya tambayi Nafisa cewa, har kin gama jimamin(mahaifiyar taki) Ko? Allah ya kyauta.
Nafisa ta mayar mai da martanin cewa, na gama nuna muku.
Haka watama ta tambayi Nafisar dan Allah ta taimaka mata ta gaya mata yanda ta yi saurin mancewa da rasuwar mahaifiyartata da wuri haka, domin tana bukatar kwarin gwiwa irin na Nafisar.
Nafisa ta amsa mata da cewa, babu wanda zai iya mantawa da mahaifanshi, har yanzu ina jin kamar zanga ta kirani a waya, nasan tana kallon komai, kuma ba zata so ta ganni a ko da yaushe cikin rashin kwarin gwiwa ba, shiyasa nake kokarin ganin na kasance yanda zata so ganin.
Gadai ci gaban yanda ta kaya tsakanin Nafisa da wasu mabiyanta.





Da wuri haka: har kin manta da rasuwar mahaifiyarki?>>Wasu suka tambayi Nafisa Abdullahi bayan da ta dora wadannan hotunan

Wannan hoton na masu kudin Najeriya ya dauki hankulan mutane
Wannan hoton hamshakan masu kudin Najeriyane da suka hada da Aliko Dangote, Femi Otedola, Sam Iwuajoku da Richie Shittu, ya dauki hankulan mutane sosai inda aka rika bayyana cewa duk da suna da kudi amma basa fariya.
Sun dauki hotonne lokacin shagalin babbar sallah data gabata.

Wannan hoton na masu kudin Najeriya ya dauki hankulan mutane

 Ku tsaya ku amsa in baku Barka da Sallah. Amma fa dubu 1000 daya ce Kacal, ita ma ba kowa ya ke samu ba.
In ba Shugaba Buhari ba, wani Shugaban kasa ne guda zai yi haka. 'Ya'yan Shugaban Protocol na kasa guda fa kenann.
Daga Shafin Magaji Ontop Daura.

Buhari ya bada barka da sallah Naira 1000

MUSULUNCI YA BAYYANA HAKKIN SHUGABANNI DA MABIYA, YA KUMA FADI YADDA MUAMALA ZATA KASANCE DA KOWA,
BAYA DAGA CIKIN KOYARWA TA ADDINI CIN MUTUNCIN SHUGABANNI, DA JIFAR SU, DAYI MUSU IHU DA ATURE, DA WASU ALUMMA SUKEYI, WANNAN YA SABAWA KOYARWAR ADDINI, DA KYAKYAWAR AL'ADARMU, DA MUTINCINMU DA HALAYANMU MASU KYAU.
IDAN SHUGABA BAYI MAKA ABINDA KAKESO BA ,KAYI AMFANI DA DAMAR KA DA AKA BAKA WAJAN ZABE IDAN YA ZO KA CANJA SHI DA WANDA KAKE GANIN YA FISHI.
KU KUMA SHUGANNI YA KAMATA KU SANI LOKACI YA CANJA KAN TALAKAWA YA WAYE, ALKAWURAN KARYA, DA KARYA DA YAUDARA, DA CIN DUKIYAR TALAKAWA DA WAWURA DA RIF DA CIKI DA HAMDUMA DA BABA KERE , YA WUCE .
YANZU KO KAYI DA GASKE KO KA HAKURA DAYIN TAKARA , AMMA MULKI SAI KA SHIRYA.
ALLAH YA BAMU SHUGABANNI NA GARI YA BAMU LAFIYA DA ZAMAN LAFIYA.

HUKUNCIN JIFAN SHUGABANNI DA YI MUSU ATURE>>Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Mata harma da maza sukan yi addu'o'in samun abokan zama na gari, a wasu lokutan mutum yakan ce ga kalar wanda yakenso ya samu a matsayin abokin zama, wata baiwar Allah ta bayyana irin mijin da take son samu wanda ya dauki hankulan mutane akai ta sharhi akai.
Baiwar Allahn ta bayyana a dandalinta na sada zumunta cewa, Allah ka bani miji na gari, me hankali wanda yasan gyaran Gado. Amin.
Kalmar da tayi ta cewa, wanda yasan gyaran Gado ya dauki hankulan mutane inda wasu suka rika tambayarta da me take nufi da haka, wasu kuwa cewa sukayi, ita gyaran gadone matsalarta?

Allah ka bani miji wanda yasan gyaran Gado>>Inji wannan budurwar

Karanta ka karu: Yanda aka samo asalin kalmar bindiga
A yayin da akayi ranar Hausa a shafukan sada zumunta da muhawara, wani bawan Allah ya bayar da labarin yanda kalmar Bindiga ta samo Asali.
Mutumin yace inda aka samo asalin kalmar bindiga shine a lokacin turawan mulkin mallaka sukan tafi farauta da masu rike musu bindiga, idan suka hangi dabbar da suke so su harba sai su cewa me rike da bindigar, bring the gun, wai shi kuma da ke ba turanci yake ji ba sai yaji kamar ance Bindiga.
Mutumin ya kara da cewa wani farfesa ne a jami'ar Bayero ta Kano ya gaya haka.



Karanta ka karu: Yanda aka samo asalin kalmar bindiga

Fati washa
Tauraruwar fina-finan Hausa, Fati Washa kenan a wadannan kayatattun hotunan nata da tasha kyau, tubarkallah,muna mata fatan Alheri.

SABABBIN HOTUNAN FATI WASHA YAR KWALISA

 Tauraruwar fina-finan Hausa da turanci, Rahama Sadau kenan a wadannan kayatattun hotunan nata da ta dauka a kasa me tsarki inda taje aikin Hajjin bana.
Ta sha kyau, tubarkallah, muna mata fatan Alheri.

Kayatattun Hotunan Rahama Sadau Dasuka Birge

Shugaba Buhari ya gana da abokanshi da sukayi makaranta tare
 Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya gana da abokanshi da sukayi makaranta tare da kungiyar 'yan kasuwan Kano da kungiyar kiristoci ta kasa, CAN reshen jihar Katsina a gidanshi dake Daura.


Shugaba Buhari ya gana da abokanshi da sukayi makaranta tare

Kujerar da shugaba Buhari ke kai ta jawo cece-kuce
 A jiyane wannan hoton na shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya karade shafukan sada zumunta da muhawa inda aka nuna shugaban a hoton zaune kan wata tsohuwar kujera data fara kodewa, wannan lamari ya dauki hankulan mutane inda akai ta bayyana mabanbanta ra'ayoyi akai.
Wasu daga cikin masoya shugaban kasar sun bayyana wannan abu da cewa saukin kaine da kuma alamar cewa shi ba barawon dukiyar kasa bane ko kuma babu burin tara abin Duniya a gabanshi.
Wasu kuwa, musamman 'yan adawa, sun bayyana hakan da cewa zabene ya kusanto shiyasa shugaban yake neman hanyar kasara samun amincewar mutane su sake zabenshi.
Ko da a ranar Babbar Sallah data gabata saida aka samu makamancin wannan lamari inda bayan kammala sallar idi shugaban yayi tattaki a kafa wanda masu magana da yawunshi suka bayyana hakan a matsayin bajinta.
'Yan adawa kuwa sun fito suka soki wannan lamari. Daga baya dai shugaban ya fito yace beyi wannan tattaki dan ya birge kowa ba.

Kujerar da shugaba Buhari ke kai ta jawo cece-kuce

Sati me zuwa kwankwaso zai kaddamar da tsaya takarar shugaban kasa
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso zai kaddamar da tsayawa takarar shugaban kasa a ranar Laraba ta mako me zuwa idan Allah ya kaimu.
Jaridar Rariya ta bayyana haka a wani rahoto da ta wallafa.
Kwankwaso dai ya koma jam'iyyar PDP daga APC a kwanakin baya kuma akwai takun saka tsakaninshi da gwamnan jihar Kano me ci wanda kuma tsohon mataimakinshine, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Tun bayan komawarshi PDP an samu rahotannin yimai ehon sai Buhari a lokuta daban-daban da ya shiga cikin mutane.

Sati me zuwa kwankwaso zai kaddamar da tsaya takarar shugaban kasa

Wata mata da taje shiga banki a jihar Abia dake kudancin kasarnan ta cire takalminta a bakin bankin kamar yanda ake iya gani a wannan hoton na sama, labarinta ya dauki hankulan mutane a shafukan sada zumunta.

Wata mata data je shiga banki ta cire takalminta a bakin kofa