Tauraron dan kwallon kasar Faransa me bugawa kungiyar PSG wasa, Kylian Mbappe ya zama dan wasa mafi tsada a Duniya bayan wata sabuwar kididdiga da ta fito.
Rahoton wanda CIES dake kula da harkar wasan kwallon kafa ta fitar ya bayyana cewa, Mbappe ne dan wasa mafi tsada a Duniya inda darajarshi takai Yuro miliyan 189.3, sai Harry Kane, wanda da shine na daya, ke biye mishi sannan kuma sai Neymar yazo na uku.
Mohamed Salah, dan kasar Egypt ne yazo na hudu, sai kuma Messi yazo na shida, babu Ronaldo a cikin goman farko na 'yan wasan da suka fi tsada a Duniyar.
An yi amfani da alkaluman shekaru, tsawon kwantiragin dan wasa a kungiyarshi, kwazon dan wasa da kuma darajarshi a kasuwar kwallo dadai sauransu wajan fitar da wannan sunaye.
Ga sunayen goma na farko kamar haka:
Kylain Mbappe 189.3m
Harry Kane 172.5m
Neymar 172.2m
Mohamed Salah 151.2m
Philippe Coutinho 149.8m
Lionel Messi 149.2m
Raheem Sterling 143.9m
Romelu Lukaku 143.7m
Dele Alli 142.9m
Antoine Griezmann 137.9m

Mbappe ya zama dan kwallo mafi tsada a Duniya

No comments