Tsufa ba ya hana saduwa tsakanin namiji da mace sai dai idan mutum rago ne>>BINCIKE

Sanin kowa ne cewa da zarar shekaru sun ja ko kuma mutum ya fara manyanta ya kan kasa iya yin wasu ayukkan da ya saba.
Mutane da dama sukan ce hakan na da nasaba ne da tsufa.
Wasu masu bincike daga jami’ar Keele dake kasar Britaniya sun bayyana cewa akwai kanshin gaskiya a zancen sai dai kuma ba kowani lokaci bane hakan ke faruwa da mutum.
Jagorar wannan bincike Dana Rosenfeld ta bayyana cewa duk da haka akwai yadda mutum ya gudanar da rayuwar sa alokacin da yake da kuricciya.
Wadannan canfe –canfe sun hada da:
1. Rashin son yin juma’I idan an tsufa
Rosenfeld ta bayyana cewa rashin son yin juma’I idan an tsufa ya danganta da irin halin rayuwar da mutum ya yi amma ba tsufa ne ke kawo hakan ba.
2. Rikicewa da tsofaffi ke yi
Ta ce kwakwalwar mutum na rikicewa ne idan mutum na yawan tunani tun yana da kurucciya wanda koda ya tsufa yake rikicewa.
Sannan ingancin kula da kiwon lafiyar da mutum ya samu yana da nasaba da yanayin rikicewarsa a lokacin da ya tsufa.
3. Tsufa na sa mutum rashin yin magana da walwala
Rosenfeld ta bayyana cewa rashin yin magana ko kuma fara’a da mutane ya danganta da yanayin mutum amma ba tsufa ne ke kawo hakan ba.
Misali wasu tun farkonsu Allah ya yi su ne ba masu son mutane ba ko kuma ba masu son hulda da mutane ba sannan kuma wasu Allah ya yi su masu son mutane.
Shi yasa ake ganin cewa wasu tsofaffin duk da tsufan su suna da kokarin yin zumunci da ‘yan uwa da abokan arziki.
4. Tsufa na kawo rashin karfin garkuwan jiki
Rosenfeld ta ce hakan ya danganta ne da ingancin kiwon lafiyar mutum wanda ya hada da halin rayuwarsa, kula da irin abincin da ke ci.
Misali tafiya ko kuma aikin da wasu tsofaffin dake kauyen mu yara baza mu taba iya yin shi ba duk da cewa mu yara ne.
#Premiumtimeshausa.

No comments