Gwamnatin najeriya da kungiyoyin kwadagon kasar sun cimma yarjejeniyar amincewa da mafi karancin albashi na Naira dubu talatin, lamarin da ya kai ga tada jijiyoyin wuya tsakanin bangaren ma’aikatan da hukumomin Najeriya.
Bangarorin da suka tabbatar da wannan yarjejeniya a kan mafi karancin albashin, sun hada ne da jami’an gwamnatin Najeriya da wakilan gwamnonin jihohi da kuma wakilan ‘yan kwadago, wanda suka yi aiki karkashin kwamiti daya mai alhakin fitar da matsaya a kan albashin ma’aikatan Najeriya.
An samu nasarar cimma yarjejeniyar bayan doguwar muharawa tsakanin sassan uku da hakan ya dakatar da fara yajin aiki a talatar nan.
Jami’in labarun kungiyar kwadago ta ULC Komred Nasiru Kabir ya shaidawa ma na ta zantawar wayar tarho cewa za a mika yarjejeniyar da a ka rantabawa hannu ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da zai turawa majalisa tayi mahawara akai kana ya sanya hannu akai ta zama doka.
Gabanin wannan matsaya, mutane da yawa sun tanadi abinci da shake motocin su da fetur don gudun cikas din da za a samu in an auka yajin aikin.

#VOAhausa.

An Tabbatar Da Naira Dubu 30 A Matsayin Albashi Mafi Karanci A Najeriya

No comments