Wasu likitoci a kasar Japan sun gano maganin kawar da cutar shanyewar bangaren jiki.
Likitocin sun bayyana cewa sun gano haka ne a wani bincike da suka gudanar a jikin wasu beraye.
” Mun yi wa wadannan beraye allurar maganin S100A9 inda muka gano cewa maganin na taimaka wa wajen motsawar jinni a jiki.
Jagoran binciken Hironori Nakagami ya bayyana cewa sakamakon da suka samu ya nuna cewa maganin na iya warkar da masu dauke da wannan ciwo sannan maganin na samar da kariya daga kamuwa da cutar.
‘‘Sanin kowa ne cewa shanyewar sashen jikin mutum na iyuwa ne a dalilin rashin motsawar jinni zuwa bangarorin jiki.Sannan sakamakon da muka samu ya nuna cewa maganin S100A9 na hana jikin mutum rashin motsawa kuma yana warkar da masu dauke da cutar’’.
#Premiumtimeshausa.

An gano maganin warkar da ciwon shanyewar bangaren jiki a kasar Japan

No comments