Masana Kimiya a Burtaniya sun gano cewa matan da ke tashi daga baccin safe da wuri ba kasaifa suke kamuwa da ciwon kansar mama ba.
Bayan shafe shekara 80 na nazari, masu bincike a Jami'ar Bristol sun karkare cewa tsakanin matan da ke tashi da wuri da safe, kashi 1 cikin 100 ne kawai ke kamuwa da Kansar mama.
Sai dai an samu karin kashi 2 cikin 100 tsakanin matan da ke bacci a makare su kuma tashi da wuri.
Batun da masanan suka ce har yanzu babu cikakken bayani a kan dalilin faruwar hakan.
Amma sun ce binciken nasu ya basu karin tabbacin cewa yanayin tsarin bacci na tasiri sosai ga jikin dan Adam.
Masana sun ce binciken da aka gabatar da shi a wani taro kan cutar daji a birnin Glasgow na kasar Skotland ya fadada fahimtar da ake da ita kan tasirin barci da lafiyar jiki.
Agogon jikin dan Adam
Kowa na da wani agogo a jikinsa wanda ke sanar da jikin yadda ya kamata ya yi rayuwa. Sunansa circadium rhythm.
Ya kan shafi dukkan sassan jiki daga lokacin da muka fara barci, zuwa yadda muke ji a jikinmu da ma hatsarin kamuwarmu da ciwon zuciya.
Amma ba agogon kowa ne ke sanar da lokaci iri daya ba.
Yaya girman matsalar ta ke?
Mace daya cikin bakwai a Birtaniya na kamuwa fa cutar dajin mama a lokacin rayuwarsu.
Wata likita mai suna Rebecca Raymond wadda kuma ke aiki a jami'ar Bristol ta Birtaniya ta fada wa BBC cewa binciken na da muhimmanci sosai.
"Binciken da aka yi a baya ya duba tasirin aikin da mutane ke yi na karba-karba, amma yana nuna cewa akwai alamar hatsari ga dukkan mata."
Shin ko samun isasshen barci zai kare ni daga kamuwa da cutar daji?
Batun na da sarkakiya.
Likita Richmond ta ce da sauran binciken da za a gudanar kafin a sanar da mata matakin da ya kamata su dauka.
Ta sanar da BBC: "Muna bukatar gano dalilin da ya sa masu yin barci da rana ke fuskantar hatsarin kamuwa da cututtuka fiye da masu yin barcin dare."
BBChausa

No comments