Gwamnatin Najeriya ta bukaci jami'an tsaron kasar su soma sanya ido sosai a kan masu amfani da shafukan sada zumunta.Ministan tsaron kasar Mansur Dan-Ali ne ya bayyana hakan bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da manyan jami'an tsaron Najeriya ranar Alhamis.
A cewar ministan, "akwai bukatar jami'an tsaro su magance matsalar kalamai na kiyayya da cin zarafi da ake yada wa a shafukan zumunta cikin gaggawa, musamman wadannan wasu mutane da suka yi suna a Najeriya ke yi".
Ministan ya ce yanzu haka sojojin kasar na hada gwiwa da sauran jami'an tsaron kasar wajen ganin an magance matsalar.
Wasu 'yan kasar dai sun dade suna kira kan a sanya ido a shafukan na sada zumunta, ko da yake wasu sun yi fatali da kiran.
Hakan ne ma ya sa a watan Disambar shekarar 2015, lokacin da majalisar dattawan kasar ta so kawo dokar da za ta sanya ido kan masu amfani da shafukan, aka yi ta kai ruwa rana tsakanin masu fafutika da wasu 'yan majalisar.
bbchausa.

Gwamnatin Buhari ta umarci jami'an tsaro su sa ido a shafukan zumunta

No comments