Ka taba jin labarin nahiyar da ake wata 3 rana bata fito ba? An yi ittifakin cewa nahiyar Antarctica ce guri mafi tsananin sanyi a Duniyar nan tamu, kuma itace nahiya ta 5 mafi girma a cikin nahiyoyin Duniya.
Wasu turawa masu binciken kimiyya sun je wannan nahiya inda suke bincike akan yanda take.
Daya daga cikinsu, idan bashi da aiki sosai yakan fito waje ya gwada girki tare da daukar kayatattun hotuna masu ban mamaki dan kuwa abincin daskarewa yake.
Ya bayyana cewa suna watanni 3 cur basu ga rana ba.
Yace kusan sukan hakura da cin abinci me dumi saidai me sanyi, a wadannan hotunan za'a iya ganin kwai be gama zubowa daga cikin kwansonshi ba ya daskare.
No comments