Bayan watsuwar hotunan bidiyon da gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje inda aka nunashi yana karbar dalolin Amurka wanda ake zargin cewa na cin hanci ne daya karba daga hannun 'yan kwangila, kamar yanda Daily Nigerian ta ruwaito. Jam'iyyar APC ta bayyana matsayinta akan wannan lamari.
Premiumtimes ta ruwaito cewa ta tuntubi jam'iyyar APC dan ta ji me zata ce akan wannan magana kuma me magana da yawun jam'iyyar ya bayyana musu cewa magana na kotu dan haka ba zasu ce komai akan maganar dake gaban Alkali ba har sai an yanke hukunci tukuna.
No comments