Kilu ta ja bau, a ranar Litinin, wani dan Najeriya mai suna Itsede Kingley ya maka Shugaba Muhammadu Buhari kara a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Lagos, inda ya nemi kotu ta haramta wa Buhari takarar shugabancin kasa a zaben 2019, saboda ya kasa gabatar wa da INEC takardun kammala jarabawar fita sakandare, watau WAEC da Buhari bai yi ba.
Buhari wanda ke neman yin tazarce a zaben 2019, ko a zaben 2015 ya kasa gabatarwa da INEC takardun jarabawar fita sakandaren sa, kamar yadda yake a bisa sharadi, sai dai ya yi rantsuwa da kwansitushin cewa su na hannun hukumar sojoji.
Itsede ya roki kotu ta haramta takardar rantsuwa da kwamsitushin da Buhari ya mika wa INEC a madadin shaidar cewa ya rubuta jarabawar kammala sakandare, watau WAEC.
Ya kuma roki kotu ta haramta wa Buhari tsayawa takara domin a cewar sa, bai cika sharuddan da INEC ta gindaya wa kowane dan takarar shugaban kasa ba.
Ba a dai sa ranar fara sauraren kara ba tukunna.
Karar an shigar da ita ne ta na mai lamba FHC/U18/1765/18.

#Premiumtimeshausa.

2019: Wani ya maka Buhari kotu saboda kasa gabatar da takardar sakandare

No comments