Bayan bankado harkallar karabar cin hancin daloli da gwamnan jihar Kano yayi da dan kwangila, PREMIUM TIMES ta saurari hirar da suka yi wajen da ake jida wa Ganduje daloli.
An dai ji inda dan kwangila ya ke gaya wa Ganduje ya gaggauta saka kudaden a aljuhan sa na babban rigar kafin wani ya shigo.
” Ina ganin ya kamata ka gaggauta cusa kudaden a aljihun babban rigar ka kafin wani ya shigo. Hakan ma zai yi kyau kaga sai ya saje da launin kayan ka.
” MD zai dawo Istanbul ranar Juma’a, daga nan sai a bamu sauran da ya rage.” Haka dan kwangilan ya fadi bayan ya loda dala 230,000 a aljuhan sa.
Abu dai kamar almara sai ga shi an bankado gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje yana karbar cin hancin bandir-badir din daloli ya karkacewa ya na loda wa a aljihun babban rigar sa.
Jaridar Daily Nigerian ne ta bankado wannan badakala inda ta saki wani bidiyo dake nuna Ganduje karara yana buga harka abin sa.
Duk da cewa akwai tabbacin aukuwar wannan harkalla bisa ga bidiyon da jaridar ta fitar, gwamnatin jihar Kano ta fito karara ta barranta kan ta daga wannan badakala.
Sai dai kuma mawallafin jaridar Daily Nigerian, Ja’afar Ja’afar da yanzu haka yana boya bisa ga tsoron farmaki da ake neman kai masa ya tabbatar da aukuwar wannan al’amari.
Ja’afar ya ce ba tun yanzu ya fara bibiyar gwamnan ba domin bankado ire-iren harkallar da yake tafkawa a kwangiloli da gwamnati ke badawa a jihar Kano.
Ya ce an dade ana shirya masa gadar zare inda a karshe ya fada.
Wani daga cikin ‘yan kwangilar da ya nemi a boye sunan sa ya fadi cewa tabbas shine ya rika mika wa Ganduje wadannan kudade kuma ya tona asirin sa ne don a gyara.
” Ni ban tona wa Ganduje asiri don son rai ba ne. Idan da haka ne da na yi amfani da bidiyon da na dauka muna biyan sa cin hanci sun fi 10 wajen azurta kaina ko kuma tilasta masa ya biya kamfanin mu kudaden da muke bin su.
” Ina da yakinin cewa idan ana fallasa jami’an gwamnari haka Najeriya za ta gyaru.
Gwamnatin jihar Kano ta karyata wannan bidiyo sannan ta ce tabbas za su gudanar da bincike akai da idan ya kai ga a shiga kotu ne ma za a shiga don a wanke gwamna Ganduje.

#Premiumtimeshausa.

Hirar Ganduje da dan kwangila wajen karbar daloli

No comments