Mun samu cewa shugabar kasar Jamus, Angela Merkel, a ranar Larabar mako mai gabatowa za ta karade wasu kasashe uku dake nahiyyar Afirka inda z at ziyarci kasar Senegal, Ghana da kuma Najeriya.
Angela za ta shafe tun daga ranar Laraba zuwa Juma'a cikin kasashen uku tare da tawagarta ta tattalin arziki kamar yadda kakakin fadar gwamnatin ta, Ulrike Demmer ya bayyana cikin birnin Berlin a ranar Juma'ar da ta gabata.
Kamar yadda shafin jaridar Premium Times ya ruwaito, ana sa ran Merkel za ta gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a safiyar ranar Juma'a ta mako mai gabatowa a fadar sa ta Villa dake babban birnin kasar nan na Abuja.
Shugaban kasar za ta fara ganawa da shugaban kasar Senegal, Macky Sall a ranar Laraba inda za su tattauna kan al'amurran da suka shafi habakar tattalin arziki na kasar.
Kazalika Angela za ta gana da shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo, a babban birnin kasar na Acca a ranar Alhamis inda za su tattauna kan al'amurran tattalin arziki da kuma tsare-tsaren kasashen ketare.
Daga karshe Shugabar ta Jamus za ta kama hanyar Najeriya a ranar Juma'a inda za ta gana da shugaban kungiyar kasashen Afirka ta Yamma, Jean-Claude Brou.
Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito, shugaba Buhari zai gana da Angela a wannan rana ta Juma'a inda za su tattauna al'amurran da suka shafi ta'addanci da kuma matsalolin tururuwar yawan bakin haure zuwa nahiyyar Turai.
Naija.ng

Shugabar Jamus, Angela Merkel zata kawo ziyara Najeriya

Jikan Sheik Ja'afar Mahmud
 Wannan shine Ja'afar Ibrahim Abdullahi Rijiyar Lemo, jikan marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud Adam, dan wajen Zainab Ja'afar Mahmud Adam babbar 'yar Marigayin.
Muna addu'ar Allah ya raya shi, ya kuma sa ya gado kakansa da mahaifinsa.
Rariya.


Jikan Sheik Ja'afar Mahmud

Dalilin da ya sa na tsunduma a harkar fim din Hausa>>Jamila Nagudu
Daya daga cikin fitattun fuskoki a masana'antar shirya fina-finan Hausa da ake yi wa lakani da Kannywood watau Jaruma Jamila Umar da aka fi sani da Jamila Nagudu ta bayyana dalilin da ya sa ta tsunduma a cikin harkar fim.
Jarumar dai ta bayyana hakan ne a lokacin da take fira da majiyar mu ta Muryar Amurka a watannin baya a cikin shirin su na duniyar Kannywood inda ta ce ta fara sha'awar yin fim ne bayan da ta kalli wani fim a shekarun baya inda a ciki aka nuna halin wata mata maras kyau da ke kama da na wata makwaficiyar ta da kuma irin yadda karshen ta ya kasance.
Jarumar wadda yanzu haka tana cikin 'yan fim masu tsada da kuma aji ta bayyana cewa daga wannan lokacin ne ta fahimci cewar lallai masu yin fim fadakarwa suke yi shine ma ita ta shigo domin ta bada gudummuwar ta.
Yan fim din Hausa dai a lokuta da dama suna fuskantar kyama da tsangwama daga al'ummar da suke cikin su sakamakon kallon da ake yi masu na masu bata tarbiyyar mutane, zargin da a kullum suke karyatawa.
Naija.ng.

Dalilin da ya sa na tsunduma a harkar fim din Hausa>>Jamila Nagudu

Me Yasa Yanzu Bana Ganin Posting Din Wasu Shafuka Da Mutane A Facebook Dina?
www.sharfadi.com
Tun bayan zarge-zargen da ake yiwa kamfanin facebook dangane da batun yaduwar labarai na kanzon kurege, da kuma labaran tayar da hankali da kawo hargitsi da tarzoma a tsakanin al’umma ya sanya kamfanin facebook daukan mataki na dakile yaduwar labarai akan shafukan nasu, wanda hakan ya jawo rashin ganin posting din mutane da kuma shafukan da kayi like.
UNFOLLOW: Wasu kuma baka ganin posting dinsu saboda kayi unfollow dinsu, to koda suna cikin abokanan k aba zaka dinga ganin posting dinsu ba.
YADDA ZAKA MAGANCE MATSALAR:
Akwai tsarin “See First” da facebook suke dashi wanda idan ka sanya mutum acikinsa to zaka dinga ganin duk posting din da yayi akan lokaci.
YADDA AKE SAKA SEE FIRST:
Hanya Ta Farko:
Idan ka shiga profile din wanda kake so kayi adding a matsayin see first, sai ka danna alamar “follow” zai baka “unfollow” da “default” da kuma “see first” sai ka zabi “see first”.
Hanya Ta Biyu Kuma Itace idan ka danna alamar “menu” a facebook sai ka nemi “News Feed Preferences” idan kashiga zai baka “prioritize who to see first”.
A wani application din kuma a profile ko page zai baka dama “add to interest list” da kuma “Get Notification”.
Note: akwai iya adadin “see first” da ake sakawa don haka kada ka cika in ka cike ko ka saka ba zai yiwu ba.
Domin shawarwari ko gyara ko aiko da wani batu da kake so a tattauna akai sai a tuntubi:
Email: info@sharfadi.com
Call & WhastApp: 09035830253
#BasheerSharfadi #Facebook

Me Yasa Yanzu Bana Ganin Posting Din Wasu Shafuka Da Mutane A Facebook Dina?

Sun gabatar da Sallar Idi tare da yankan layya 'karkashin wani Amir É—insu a yankin Tafkin Chadi.
Sarauniya.
'Yan Boko Haram Sun Gabatar Da Bikin Babbar Sallah A Yankin Tafkin Chadi>>DAILY NIGERIA
 Jaridar DAILY NIGERIAN ta fitar da wasu hotuna da ke nuna yadda 'yan 'kungiyar Boko Haram suka gabatar da bikin Babbar Sallah a ranar Talata.


'Yan Boko Haram Sun Gabatar Da Bikin Babbar Sallah A Yankin Tafkin Chadi>>DAILY NIGERIA

Kalli Kwalliyar Sallah ta Rahama Sadau
Tauraruqar fina-finan Hausa da turanci, Rahama Sadau kenan a wannan kayataccen hoton nata da ta saka tana yiwa masoyanta barka da Sallah, tasha kyau, tubarkallah, muna mata fatan Alheri.

Kalli Kwalliyar Sallah ta Rahama Sadau

Sheikh Dahiru Bauchi, Dr. Isah Aliyu Pantami da gwamnonin Yobe da na Bauchi a kasa me tsarki
 Babban malamin addini Islama, Sheikh Dahiru Usman Bauchi da mukarramabanshi da gwamnan jihar Bauchi, Barista Muhammad Abubakar, Sheikh Dr. Aliyu Isa Pantami, gwamna Ibrahim Geidam na jihar Yobe na daga cikin wanda sukayi hajjin bana, a wadannan hotunan shuwagabanninne da al-ummarsu a kasa me tsarki.
Muna fatan Allah ya amsa Ibada.





Sheikh Dahiru Bauchi, Dr. Isah Aliyu Pantami da gwamnonin Yobe da na Bauchi a kasa me tsarki

Kalli wasu kayatattun hotunan Rahama Sadau
 Tauraruwar fina-finan Hausa da turanci, Rahama Sadau kenan a wadannan kayatattun hotunan nata da suka dau hankula, kwanannan ne jarumar ta kaddamar da wani sabon jan baki me dauke da sunanta.


Kalli wasu kayatattun hotunan Rahama Sadau

Fatima Ganduje tayi amfani da jan bakin Rahama Sadau
A kwanannan ne mukaji labarin tauraruwar fina-finan Hausa da turanci, Rahama Sadau ta fito da wani jan baki me dauke da sunan ta, bayan fitowar jan bakin, wasu daga cikin abokan aikinta mata sun rika nuna goyon baya ta hanyar saye da amfani da jan bakin, a wannan karin kuma diyar gwamnan jihar Kano ce itama tayi amfani da jan bakin.
Fatima Abdullahi Umar Ganduje dake auren dan gwamnan jihar Oyo, Idris Ajimobi ta fito ta bayyana cewa itama tana amfani da wannan janbaki.
Rahamar ta nuna farin cikinta da wannan labari inda ta saka hoton a shafinta na sada zumunta.

Fatima Ganduje tayi amfani da jan bakin Rahama Sadau

Alhajin Najeriya ya mayar da makudan kudaden daya tsinta a Makka
Wani alhaji daga Najeriya dake gudanar da aikin hajjin bana a kasar Saudiyyya ya mayar da fiye da N1.4 da ya tsinta a Makkah.
An bayyana sunan alhajin, Musa Mohammed Edotsu, daga jihar Neja kuma ya tsinci kudin ne a sansanin alhazai na jihar Neja a Makkah.
Wani dan jarida daga jihar Neja ,Alhaji Abdul Isa, ya bayyana a shafinsa na dandalin sada zumunta na Whattsapp cewar alhajin ya mayar da kudin da ya tsinta ga wakilan hukumar alhazai ta jihar Neja domin a mayarwa da mai su.
A cewar Isa, daga baya an gano cewsar kudin mallakar shugaban hukumar kula da jin dadin alhazai na jihar Enugu ne, Alhaji Zukalraini Saeed.
Da yake mayar da makudan kudaden gam ai su, shugaban hukumar jin dadin alhazai ta jihar Neja, Alhaji Abubakar Magaji, ya bayyana cewar sun gano mai kudin ne bayan ganin wasu kayansa cikin kudin da suka hada da fasfo dinsa.
Wanda ya zubar da kudin, Alhaji Zulkalraini, ya bayyana jin dadinsa tare yin godiya ga hukumar alhazai ta jihar Neja bisa wannan hali na tsoron Allah da suka nuna. Kazalika ya yi kira ga ragowar alhazai dake aikin hajji da suyi koyi da kyawawan halaye irin na wanda ya dawo da kudin, Alhaji Edotsu.
Naija.ng.

Alhajin Najeriya ya mayar da makudan kudaden daya tsinta a Makka