Showing posts with label Bangaren Addini. Show all posts
Showing posts with label Bangaren Addini. Show all posts
Babban malamin addinin musulunci na kasar Masar, Shawki Ibrahim Abdel-Karim Allam, ya fitar da wata fatawa inda ya haramta amfani da kudin intanet na Bitcoin.
A fatawar da a ka wallafa ranar Litinin, Shawki Allam ya ce ba a yarda musulmai su siya ko su siyar ko kuma su biya haya da wannan tsari na Bitcoin ba.
Ya ce amfani da kudin intanet na da hadari domin zai iya haifar da zamba da yaudara, kuma kasancewar tsarin maras tabbas, ya na iya cutar da jama'a da ma kasashe.
Babban malamin ya ce sai da ya nemi taimakon masana tattalin arziki kafin ya yanke wannan hukunci.
Mene ne Bitcoin?
Bitcoin na da abubuwa biyu da suka bambanta shi: kudin intanet ne kuma ana ganinsa a matsayin wani abu da za a iya amfani da shi a madadin kudi.
kan intanet sabanin kudaden takarda ko sulalla da ke aljihunka
Duk da cewa akwai wasu na'urorin bayar da kudi (ATM) na musamman da ke bayar da Bitcoin, ya fi dacewa a yi tunaninsu kamar 'yan kudaden intanet.
Kuma babu gwamnati ko kuma bankin da ke buga Bitcoin.
Wannan na nufin "ba kudin da doka ta amince da shi ba ne, ba za ka iya biyan harajinka ko kuma ka yi amfani da shi wajen biyan bashi ba", in ji Dr Garrick Hileman na fannin koyar da kasuwanci a jami'ar Cambridge.
Ana samar da Bitcoins ne ta wata hanya mai sarkakiya da ake ce wa "haka" (wato "mining, a Ingilishi), sannan wasu komfuntoci da ke hade a fadin duniya za su saka ido kansa.
Ana samar da kimanin Bitcoin 3,600 a ko wace rana - kuma a halin yanzu akwai kimanin kudin miliyan 16.5 da ke yawo.
Sai dai kuma, kamar dukkan kudade, darajarsa ya dangata ne ga iya kudin da mutane suke son saye shi tare da sayar da shi.

bbchausa.

Haramcin Kudin Internet Bitcoin - Fatawa

"Manzon Allah (S.A.W) Ma Ya Roki Allah Ya La'anci Duk Wani Shugaba Mai Kuntatawa Al'ummarsa.

"Zagin Da Ake Yi Min Ba Zai Hana Ni Ci Gaba Da Fadin Gaskiya Ba.

"Duk Malamin Da Zai Yi Amfani Da Kuri'arku Munafiki Ne", Kalaman Sheik Ahmad Gumi

Zagin da ake yi min ba zai hanani ci gaba da fadin gaskiya ba>>Sheikh Gumi

Wani faifan bidiyo da ya fito na tauraron fina-finan Hausa, Nura Hussain inda ya saka wani wa'azin malamin addinin Islama Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya caccaki shugaban kasa, Buhari da ma masu goyon bayanshi.
Anji malamin yana cewa yanzu dai shekara hudu sun tafi, babu abinda ya kara mana saidai talauci, du abinda kake da kadara ka sayar, shekara hudu ta tafi babu abinda suka karu sai yunwa da talauci da kara rarrabuwar mutane da kuma tsoro, to dayan biyu, in mun gayara yanzu ko muyi gyaran shekara takwas ko mu yi gyaaran shekara hudu. Fisabilillahi, barnar da muke ciki yanzu, muna bukatar shekara takwas ko muna bukatar shekara hudu mu gyara?
Malamin ya kara da cewa duk wanda ya jawo mana shekara hudu Allah ya la'aneshi.
Nura Hussain bayan yayi salati ga fiyayyen halitta yace, Ahmad Abubakar Gumi kamar yanda kace Allah ya la'anemu saboda muna yin Buhari to kaine Allah ya la'ana, kaine la'antacce a gurin Allah, ya kara da cewa, manzon Allah (S.A.W) ya ce mana. La'ana tana komawa wanda suka yi ta. Idan kayi la'ana wannan la'anar tana tashi sama sai ta duba taga kaine la'ananne ko kuwa wanda ka yi wa shine la'ananne? Sai ta fadawa wanda i dace, saboda haka la'antar zata koma gareka dan baka da hujjar la'anar mu.
Ya kara da cewa, mun mun yarda da cewa shugaba Muhammadu Buhari shugabane Wanda kace ya karamana talauci wannan karya kake yi, domin talauci dane muka san cewa muna cikin talauci, domin bamu san ina muka dosa ba, domin dibar kudimmu ake ana raba muku, baka da kanti, baka da shago, baka da sana'a, ba yanda za'ayi kaso janar Muhammadu Buhari saboda yace kowa saidai ya ci guminsa.
A karshe dai yace, kamata yayi idan malamin siyasa zai yi ya fito yayi ta karara ya dena boye-boye.

#arewamini

Kaine la'ananne Ba Mu Ba - Inji Nura Hussain ya mayarwa da Dr. Ahmad Gumi martani

1. Tun Bashi Da Komi Na Aure Shi.
Amsa: Ke Me Kike Da Shi Sanda Kuka Yi Auren?
2. Ko Rigar Kirki Ba Shi Da Shi, Ni Nake Rufa Masa Asiri, Ba Shi Da Ko Sisi.
Amsa: Ke Kika Yi Masa Arzikin, Idan Ke Kika Yi Masa Karbe Abinki.
3. Namiji Ba Shi Da Amana!
Amsa: Karin Aure Ma Rashin Amana Ne? To A Faranta Maki A Sabawa Allah Kenan!
Rariya.

Ga Karatun Mata Idan Mijin Su Zai Kara Aure!!!

Wannan hoton wata tsohuwace tukuf dake karatun Qur'ani, hoton ya yadu a shafukan sada zumunta inda mutane da dama suka ta saka mata Albarka.

Tsufan Kirki

"idan kaga musulmi dan arewa me hankali yana zagin buhari to matsiyaci munafukine, da zaka tambyi mutum akan me yasa yake zagin buhari ? ze ce maka buhari ya kawo yunwa fatara da talauci to kawai ka samasa kaulasan domin baisan Allah ba bashi kuma tauhidi" a cewar malamin

Zagin Buhari Sifface Ta Munafurci - sheik kabiru Gombe

Wata baiwar Allah ta bayar da shawara ga maza da mata idan zasu yi aure da a rika binciken addinin mutum da akidarshi saboda rarrabuwar akidu kala-kala da ake dasu.
Ga shawararta kamar haka:

Shawara: A rika bincike Akidar mutum kamin a yi aure

Tazarar haihuwa
Masana kiwon lafiya sun baiwa matan dake tsakanin shekara 30 zuwa 40 dake bukatar daukar juna biyu shawara kan tazarar da ya dace a samu domin kare lafiyar su.
Rahotan wani bincike da masanan suka yi wanda aka wallafa shi a Mujallar kula da lafiya ta Amurka tace ana bukatar akalla shekara guda ko kuma biyu wajen daukar cikin, duk da yake daukar juna biyu ga masu shekarun da suke da yawa na tattare da hadura.
Laura Schummers ta Jami’ar British Columbia dake Amurka da ta jagoranci binciken da aka gudanar, tace binciken ya nuna hadari wajen daukar ciki ga matan da suka wuce shekaru 35, sabanin masu kasa da wadanan shekarun.
A kasar Amurka likitoci kan baiwa mata shawarar samun tazarar akalla watanni 18 kafin sake samun ciki.
RFIhausa.

Ana bukatar shekara akalla 1 wajen samun tazarar haihuwa>>Masana

Gwani na dudu wani mutum ne makarancin alqur'ani kuma hafizi Gangaran me gudun duniya da akayi shi acikin birnin kano unguwar koki, sunansa na gaskiya Ibrahim, yana da mata guda biyu masu suna iri daya dudu da dudu, Wanda Dukkaninsu mahaddatan alqur'ani ne.
Yayi yawon Neman ilimin addinin muslinci musan man ilimin alqur'ani da tajwidi da Tafsiri, Dan ana cewa har kasashen larabawa yashiga Dan Neman ilimin Qur'ani. Duk da lokacin ba mota a kafa ya dinga tafiya.
Makarantarsa itace babbar tsangaya wacce Duk wani me asali a alqur'ani a birnin Kano tarihinsa yake komawa gareta.
Ga kadan daga cikin almajiransa:
1_Gwani Rabiu Dan Tunki. ( mahaifin khalifa isyaka Rabiu
2_ Alhaji Alhassan Dan tata.
3_ Gwani Salihu Dan zarga ( mahaifin Gwani yahuza)
4_ Gwani Salihu Dan turaki ( mahaifin Gwani Aliyu limamin koki) Wanda shine kakana.
5- Gwani Abubakar turaki( malam Turaki) kakansu GWANI Lawi da Gwani Muntaqa.
ME AKE NUFI DA QUR'ANI BUGUN GWANI NA DUDU.
Gwani na dudu yakasance yana rubuta Qur'ani da hannu, sabo da lokacin bature be kawo na'ura wacce ake buga alqur'ani da ita ba,
mutanen lokacinsa suna dauka babu wani alqur'ani me daraja da za'ai rantsuwa dashi idan ba Wanda Gwani na dudu yarubuta ba.
a yanzu Gwani na dudu yakai kusan shekara 70 da rasuwa, amma har yanzu ana karatu a inda ya kafa makarantarsa tun wancen lokacin..
Gwani na dudu yana da Yaya da jikoki mahaddatan alqur'ani fiye da dubu.
Wanda yafi shahara a yanzu acikin su shine Gwani yahuza Gwani Dan zarga babban Alqalin musabaqar alqur'ani na Africa.
Gwani Lawi shugaban mahaddatan alqur'ani na Nigeria.
Addu'ar da mukeyi ko yaushe, Ya Allah yanda mutanan nan su ka yi wa Qur'ani hidima Allah Ka kula da bayansu.
Maje El-Hajeej Hotoro.

GWANI NA DUDU: ME KA SANI GAME DA ALKUR'ANIN DA Jaafar Jaafar YA JE DA SHI KANO

Abubuwa basu tafiya yanda ya kamata a kasarnan>>Sarkin Musulmi
Sarkin musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar na III yayi tsokaci akan yanda lamura ke gudana a kasarnan inda yace abubuwa basa tafiya yanda ya kamata.
Sarkin ya bayar da misali da fadan Kaduna wanda yayi sanadin salwantar rayuka sama da 50 wanda yace bafa fadan addini bane, saboda ba'a kona coci ko masallaciba, wasu ne marasa aikinyi da suke fama da yunwa suke neman yanda zasu yi da rayuwarsu suka fasa shaguna suna satar abubuwa da kuma kashe wanda basu ji ba basu gani ba.
Sarkin yayi wannan jawabine a Abuja wajan taron da hukumar sasanta tsakani dan ci gaban dimokradiyya ta gudanar, kamar yanda jaridar Punch ta ruwaito.
Ya kara da cewa yanzu da muke tunkarar zabe za"a rika samun irin wannan matsalar saboda wasu 'yan siyasa zasu yi amfani da wannan damar wajan samun nasara ga abokan hamayyarsu.
Sarkin ya bayyana takaici akan yanda babu tsari me kyau akan gudanar da harkar tsaro ta bangaren gwamnatin tarayya sannan kuma su jami'an tsaron babu hadin kai a aikin nasu dan cimma abinda ake so.

Abubuwa basu tafiya yanda ya kamata a kasarnan>>Sarkin Musulmi

Ta Sadaukar Filinta Domin Gina Masallaci A Jihar Sokoto Tare Da Bada Gudummawar Dubu 800
A ranar Litinin din da ta gabata Hukumar Zakkah da Wakafi ta Jihar Sakkwato ta karbi wakafin fili daga hannun Hajiya Fatima Muhammad.
Hajiya Fatima, ta bayar da filin nata dake Unguwar Guiwa layout a matsayin wakafi domin Allah ta da nufin gina masallaci.
Cikin jawabin da ta yi lokacin bada filin ta ce "na yi wannan ne lura da Hadisin Annabi S.A.W dake nuni da idan mutum ya mutu abu uku ne za su amfane shi, ciki har da wanda ya gina masallaci" (Sadakatul Jariya).
Ta kara da cewa "Na zauna na yi tunanin wannan Unguwar babu masallaci, kuma shiyar ta kunshi jama'a, sai na yanke shawarar naba da wannan filin domin a yi masallai, kuma ga bohol dina nan gaban gidana a jawo a yi famfuna a yi wakafi, kuma hukuma na iya sarrfa filin zuwa duk abinda zai amfanar da al'umma".
Hajiya Fatima ta gabatar da taswirar masallacin da kudi naira dubu dari takwas (800,000.) domin fara aiki da su.
Hajiya Fatima ta yi kira ga 'yan uwanta Mata da sauran al'umma da su yi hubbasar shiga cikin irin wadannan ayyuka domin taimakawa musulunci da al'ummar musulmi baki daya.
Shugaban Hukumar Malam Muhammad Lawal Maidoki, kuma mataimakin sakatare mai kula da kasashen yankin Afirika ta yamma, na kasashen Duniya masu sha'anin zakka da wakafi, (Sadaukin Sakkwato) ne ya jagoranci karbar wakafin tare da wasu ma'aikatan hukumar.
A cikin jawabinsa na karba, ya bayyana matar a matsayin mace ta farko da ta taba bada wakafin wuri domin gina wani abin amfani ga bayin Allah, kuma ta biyu a bada wakafin kudi, haka ma ya yi kira ga sauran mutane da su dubi muhimmacin yin wakafi domin Allah da samun tsira gobe Lahira.
Shugaban ya bada tabbacin za su yi kokarin kula da wurin a matsayin su wadanda sharia ta dorawa kula da shi. Sadaukin ya bada tabbacin za a yi duk abinda ya kamata na shari'a, samar da shaidu, sanya hannu da fitar da iyakar wurin dan cika sharudddan wakafi.
A karshe ta zagaya da wakilan hukumar cikin wannan wurin.
Daraktan tsare-tsare na ma'aikatar Malam Murtala Garba Alkali ne ya jagoranci yin addu'a ta musamman ga wannan baiwar Allah.
Daraktan zakka Malam Muhammad Umar Hamma Ali, ta kudi, Hajiya Huraira Isah Illo, Jami'in Hulda da 'yan jarida Malama Abubakar Sadik, na cikin wadanda suka shaidi karbar wannan wakafin tare da sauran ma'aikatan hukumar.
Ko kwanan baya hukumar ta karbi wani gida da ofishi wanda wasu bayin Allah suka bada a matsayin sadaka.
Rariya.

Ta Sadaukar Filinta Domin Gina Masallaci A Jihar Sokoto Tare Da Bada Gudummawar Dubu 800

Muslim ladies are beautifull
 Wannan wata 'yar magana ce da ta faru tsakanin wani me suna Innocent da yace matan musulmi na da kyau a dandalinshi na Twitter, wani ya mayar mishi da cewa saima a lahira zaka sha kallo.

Karanta ka nishadantu.


Tsakanin Innocent da yace matan musulmi na da kyau da wani Musulmi

SHARWARWARI>>Daga Malam Aminu Daurawa
🌹= Kafin kayi rubutu kayi nazari akai;
🌹= Kafin kayi magana kayi tunani akai; 🙉
 ðŸŒ¹= Kafin ka yanke hukunci kayi bincike akai;
 ðŸŒ¹= Ba kowacce magana ake yarda da ita ba;
🌹= Kuma ba kowacce ake karyatawa ba;
 ðŸŒ¹= Kafadi Alkairi ko kayi shiru;
🌹= Ka yawaita aikata Alkairi fiye da sharrii;
 ðŸŒ¹= Ka yawaita kyakyawar addu'a fiye da mummuna;
 ðŸŒ¹= Ba kowa bane mutumin kirki kuma Ba kowa bane mutumin banza;
🌹= Kada ka zagi kowa kuma in an zageka kayi hakuri yafi;
🌹= Kafun ka roki wani abu gun Allah ka yimasa godiya akan abunda kake dashi;
🌹= Ka yawaita neman gafara agun Allah kuma kar kacuci kowa;
🌹= Ka yawaita yiwa Annabi muh'd (s.a.w) salati a kullum kuma akoda yaushe saboda bakada kamarshi;
🌹= Kada kaji haushi idan kayi post a whatsapp, face book , instagram, mai ma'ana idan ba'ayi maka comment ba don ba kowa ne keson irin post dinka ba;
🌹= Kada ka fifita kayan shaidan fiye da na Allah ;
🌹= Kada kayi yaudara a soyayya saboda alhaki kyaiwkuyo ne Kaima watarana za'ayi maka ko ayiwa wani naka;
🌹= Idan kaga wani mai mummunar tarbiya Kada kayi saurin la'antarsa kai dai kayi masa addu'a ko kayi shiru;
🌹= Idan kaga mabukaci ka taimakeshi Allah zai biyaka;
🌹= Ka yawaita sadaka saboda tana yaye zunubai;
🌹= Ka taimaki tsoho ko tsohuwa , koda ba naka bane kaima watarana za'a taimaki naka;
🌹= Ka sada zamunci domin yana kara nisan kwana kuma yana kara Arziki;
🌹= Allah yakawo mana dauki ya kuma sa mudace;

SHARWARWARI>>Daga Malam Aminu Daurawa

An hana musulmai yin sallah da ajiye gemu
A wani kauyen kasar India an hana musulmai yin sallar Jam'i da kuma ajiye gemu saboda zargin mutuwar wani dan saniya a hannun wani matashin musulmi na kauyen.
Jaridar Telegraph ta ruwaito cewa, matashin da ya aikata wancan laifi an koreshi daga garin sannan kuma ya jawa sauran musulman garin an hanasu yin sallar jam'i, saidai su yi a gida an kuma hanasu sakawa 'ya'yansu sunan musulmai.
Jaridar ta ruwaito wata kotu na cewa zata tuntubi mahukunta kauye dan daukar matakin da ya dace aka wannan lamari.
Daya daga cikin musulman dake kauyen yace basu iya saka hula ko kuma ajiye gemu tunda wancan lamari ya faru sannan sai sunje wani gari me nisa suke samun yin sallah.

An hana musulmai yin sallah da ajiye gemu

MUHIMMANCIN SHAN TABA GUDA UKU
1- Mai shan taba sigari ba ya tsufa.
2- kare yana tsoron mai shan taba sigari.
3-Barayi raina motsinka ba sa zuwa gidan mai shan taba sigari.
Dalili. Eee mana saboda.
1- mai shan taba sigari yana mutuwa ne da kuruciyarsa kafin ya tsufa, kamar yadda ma'aikatar lafiya ta duniya ta nuna, saboda lalacewar da Huhunsu keyi.
2- Yayinda Huhun mutum ya mutu bazai iya tafiya ba sai yana hutawa kuma yana dogara sanda, kagako ai kare yana tsoron wanda ke rike da sanda.
3- Duk mai shan taba komai dare yana kwana yana tari, kagako bazaiyi dogon bacci ba, don haka barawo bazai je ba tunda da motsin mutum a wannan gida.
IDAN KANA SON CIN MORIYAR WADANNAN, TO KACIGABA DA SHA, IDAN KUMA BAKA GAMSU DA SU BA TO KA DAI NA....... (Kukan kurciya).
Rariya.

MUHIMMANCIN SHAN TABA GUDA UKU