Buhari ya yi tsokaci kan maganar da ya yi kan matasa
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya yi tsokacin kan maganar da ya yi akan matasa wadda ta janyo ce-ce-ku-ce kwanakin baya. Da yake magana da Sashen Hausa na VOA, shugaban ya ce ba a bayyana maganar tasa yadda take ba.
Shugaban ya kuma kara haske kan maganar da ta janyo masa suka a shafukan sada zumunta a Najeriya.
Ya ce: "Toh ka san Najeriya an ce mun kai miliyan 180 ko kuma miliyan maitan.
"Kuma 60 bisa 100 na su duk matasa ne, wato shekara 30 abin da ya yi kasa, mu kamar a Arewa ba su yiu makaranta ba, koko suna yi sun fita.
"Toh, baya ga dai Allah Ya sa damunan bara da ta bana ta yi albarka, yawancin su ba su da aikin yi. Suna zaune.
"Irinsu ko sun je kamar misali kudu, abin da za su samu bai ma isa su biya kudin gidan haya ba, balle abin da za su ci su sha su yi sutura ko kuma su koma gida."
Ya ce miliyoyin matasa ne suka samu aikin yi ta hanyar noma, amma 'yan jarida ba su bayyana wannan ba.
Shugaba Buhari ya kara da cewa : "Su kuma dama 'yan jarida na Najeriya balle na rubutawa a.. kusan abin da suka ga dama suke yi.
"Yanzu kaman nasara da aka ci a noma da bara da bana, miliyoyin mutane sun je gona, sun yi aiki kuma abin ya yi albarka. Amma ka ga ba'a maganar. Miliyoyi! sai kullum a tashi ana zage-zage."
bbchausa.

Wata sabuwa: Buhari ya yi tsokaci kan maganar da ya yi kan matasa

No comments