Download Psiphon handler Apk v108 : You wish to access
the internet? It is on the street and has no WiFi
around? Here is the solution of your problems! Now you can
browse unlimited and without paying anything for it, using
the VPN app Psiphon handler. It will give a proxy setting so
that you are ready to use it quickly and easily on any carrier,
such as: Sure, HI, TIM, Globe , Airtel and Vivo. But, psiphon
108 handler ui settings varies from one network to others.
psiphon handler apk latest version
More than one million people around the world are already
using this tool to access websites and services that are
blocked on the Internet or not available through your normal
service provider. To access sites that your ISP is blocking,
or to add a layer of protection when using open Wi-Fi
services, Psiphon is the best tool to access the open
Internet. You can download psiphon handler apk from here.
Download Psiphon Handler Apk 2017
Package name: Psiphon handler v108
Size: 5.17 MB
Operating system: Android
Psiphon Handler Apk is a navigation tool open source which
aims to circumvent censorship suffered by millions of users
in several countries around the world, where freedom of
expression is restricted and can not access freely to all
Internet content.
once we execute the application servers connect to psiphon
, which will guarantee us access through a network of
proxies to any website in the world we want to visit, without
danger that we discovered in the process. That is, we can
freely browse the Internet anonymously. This version of
psiphon handler 108 ui is developed by Dzebb.
Once connected to this secure network of Proxies, the
application will allow us to navigate from their own built-in
browser, which can add pages to favorites, set up
homepages and in short, do everything that we could do
with any normal browser. The benefits of this browser, of
course, can not compete with other applications, but still
perfectly fulfills its mission. Psiphon is a very interesting tool
for users of Android terminals with censorship problems as
those mentioned in the first paragraph. Thanks to this
application may freely browse the Internet and visit any site
they want to visit. psiphon
Psiphon handler Settings
This app doesn’t need Root.
To activate this service you need a 3G or 4G
connection.
Download Psiphon Handler v108 apk (link at end of
post)
Install APK and open it.
If you use chip Tim click here to see the Psiphon
already configured for the operator.
Copy and place one of the Hosts below under “Proxy
Server”, according to your service provider.
Select “Start”
When you start the app click on “Tunnel Whole Device”
Click “I trust this application,” and select “OK”
The application will connect to the server
Now just enjoy the free and unlimited internet with high
speed!
If the above method does not work, you can find other
methods on google.


Psiphon handler apk v108 Free download

White house family power vocalist..King of northern entertainment – Adam A. Zango unleashes new music for the end of year festivities. As expected at this time of year, the talented singer serves up something on the commercial spectrum titled – Dance 4 me (lil ameer cover)

Listen & Download “Adam A. Zango – Dance 4 me” below:-

Download mp3 here

Adam A Zango - Dance 4 Me ( Lil Ameer Cover ) mp3 download

Domin sauko da Application din cikin wayanku saiku danna koren rubutu dake kasan nan


SHIGA NAN

Download latest Topup Africa apk here

 kada kusake abaku labari Wannan damace damuzo muku da ita kuchi gaba da kasancewa damu akoda yaushe maza kuyi download an an

Kada Ku manta

Daukoshi anan

Tirkashi yadda zaka samu kyautar sama da 750 da DATA acikin layin wayanka duk ranan duniya ta hanyar anfani da wayar android

Fitacciyar jarumar finafinan Hausa Rahama Sadau ta fito ta bayyanawa Duniya cewa tana son mawaki Umar M. Sharif/ yana birgeta, Saidai abinda be fito filiba shine sone take mai na soyayya irin ta saurayi da budurwa ko kuwa soyayya a matsayinshi na abokin aikinta kuma mawaki daya iya aikinsi? dalilin dayasa baza'a iya bata fassara kaitsayeba shine saboda kalmar turancin da tayi amfani da ita ba wadda take nuna soyayyar saurayi da budurwa bace kai tsaye, zata iya nufin cewa kawai yana birgetane kuma tana son kasancewa tare dashi ko kuma tana son yin aiki tare dashi.
Umar M. Sharif dai shine ya rera wakar fim din Rahama Sadau na Raraiya wanda yanzu shine fim din da Rahamar ta taba shiryawa da kanta kuma ya samu karbuwa a cikin jama'a, yanzu haka fim din ya samu kyautar ftaccen fim na shekarar nan da muke ciki ta 2017.
Umar M. Sharif dai ya mayar mata da amsar cewa ya gode.
Rahama Sadau dai ta taba nuna alamar soyayya ga dan wasan kwallon kafa da ya fi kowane dan wasa tsada a Duniya watau Neymar, ta kuma taba rokon fitaccen dan wasan kasar Indiya Hrithik Roshan da yazo ya Aureta.

"Umar M. Sharif yana birgeni(ina sonshi)">>Inji Rahama Sadau

I hope you have heard about the recent update made by WhatsApp which is calledWhatsApp Live Location?.
You can't hide anymore, WhatsApp knows your location and there is a new feature called WhatsApp Live Location which allows you share your location with your friends and groups while chatting with them.
It's good to know that location Sharing is not a new feature in mobile apps because apps like Google Maps, Facebook Messenger, and Snapchat all uses it. It is a great way to let people know where you are, for instance, if you have travelled to a country or city that you are not familiar with. So how do you use this new feature? Well, before that, take this important message.
HOW TO GET WHATSAPP LIVE LOCATION FEATURES
Note that this feature has just being announced and could take few days before reaching everywhere. All you need to do now is to keep tabs on the latest Whatsapp update via playstore for Android users and iTunes for iOS users. Once there is a new update, just click on "update" to get it.
Once the WhatsApp live location (location sharing) is available on the app, follow below steps to use it;
1. Open a chat with the person you want to share with
2. Under “Location” in the attach button, there’s a new option to “Share Live Location.”
3. Choose for how long you want to share and tap send.
Wow! By doing this, you have just sent your real-time location on a map to the recipient. Think of it working the same way your Uber driver is able to locate you (and vice-versa).
WhatsApp Location Sharing works for groups as well, so you can share your location with a group you are chatting with and every one in that group will see your location same way. If multiple people in the group share their locations, all those locations will be visible on the same map. Nice.
The most important is WhatsApp Live Location has end-to-end encrypted feature which lets you control who you share with and for how long. You can choose to stop sharing at any time or let the Live Location timer simply expire. Live Location is available for Android smartphones and iPhones.
Meanwhile, if you don't want your location to be tracked by WhatsApp, you just have to simply turn off location services from your phone settings.
What do you have to say about this improvement made by WhatsApp?

Tutorial On How To Use New WhatsApp Live Location Features

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Bill Gates, ya ce Najeriya tana daya daga cikin kasashen da yake sanya ido kansu sosai.
Bill Gates wanda ya bayyana haka a wata hira da BBC, ya ce kasar tana da muhimmanci ne a wurinsa saboda ita ce ta fi kowace kasa yawan al'umma a nahiyar Afirka.
"Wannan ne ya sa gidauniyata ta Bill & Melinda Gates Foundation take ci gaba da aikace-aikacenta a can," kamar yadda ya ce.
Har ila yau, ya ce akwai babban kalubale a fannin kiwon lafiya a yankin arewacin kasar.
"Akwai matsalar cutar maleriya da kuma batun 'yan gudun hijira. Muna aiki da wadansu daga cikin gwamnatocin jihohi kamar na Kano da Borno a kokarinmu na ganin mun magance kalubalen kiwon lafiya a yankin," in ji shi.
Ya ce ayyukan gidauniyarsa suna taimakawa wajen rage mutuwar mata masu juna biyu da kuma kananan yara a fadin kasar.
Sai dai ya ce suna aiki ne tare da gwamnatin kasar da kungiyoyi masu zaman kansa da kuma attajirin nan da ya fi kowa arziki a nahiyar Afirka, Alhaji Aliko Dangote - wanda dan kasar ne.
Kamar sauran kasashen Afirka, Najeriya na daya daga cikin kasashen da aka fi yawan samun mace-macen mata wajen haihuwa da kuma na kananan yara.
bbchausa.

To kunji fa Nigeria na da muhimmanci a wurina – Bill Gates

Me shirya finafinan Hausa Kawu Kamfa ya zama Ango, an daura aurenshi a yau da sahibarshi, muna mishi fatan alheri da kuma Allah ya basu zaman lafiya.
Kawu Kamfa yayi wani batu akan auren nashi wanda yaja hankulan mutane, cewa yayi" Alhamdulillahi na godewa Allah na rike matata kam kamar yanda baba Buhari ya rike Najeriya.

An daura auren Kawu Kamfa: " Na rike matata kam kamar yanda baba Buhari ya rike Najeriya">>injishi

A yau Lahadi daya ga watan oktoba Najeriya ke cika shekaru hamsin da bakwai da samun 'yancin kai daga turawan mulkin mallakar kasar Ingila, wannan wata baiwar Allahce data saka kaya masu kalar tutar Najeriya wato kore da fari dan murnar wannan rana.
Babban kamfanin yanar gizo na matambayi baya bata wato Google ya taya Najeriya murna.
Haka kungiyar kwallon kafa ta Manchester United itama ta taya Najeriya murnar ranar 'yanci.

Tirkashi Ranar 'Yancin Najeriya: Google da Manchester United sun taya Najeriya murna

Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Kannywood Hadiza Gabon ta soma fitowa a fina-finan Nollywood da ake yi a kudancin Najeriya.
Jarumar ta shaida wa kafar bbc hausa cewa ta fara gwada sa’arta a fina-finan Nollywood ne domin ta nuna basirar da take da ita ta yin fina-finai a ɓangarori daban-daban.
A cewarta, “Ba wannan ne karon farko da na soma yin fim da turanci ba. Lokacin da na je Amurka, na fito a gajerun fina-finan turanci, amma wannan ne karon farko da na fito a fina-finan Nollywood.
Fitaccen Jarumi kuma Furodusa a Fina-finan Nollywood Mike Ezuruonye da Jaruma Hadiza Gabon Ayayin Aikin fim ɗin Lagos Real Fake Life.
“Fitaccen jarumin Nollywood Mike Ezuruonye ne ya gayyace ni na fito a wani fim dinsa mai suna ‘Lagos real fake life’.
“Shi ne furodusan fim din kuma na fito ne a matsayin ‘yar arewa. Zan rika yin shiga irin ta bahaushiya don haka kayan da nake sa wa a fina-finan Kannywood irinsu nake sa wa a wannan fim”.
Hadiza Gabon ta ƙara da cewa “Tun da ya gaya min cewa zai so na fito a fim ɗinsa, na shaida masa cewa ba kowacce rawa zan taka ba. Ba zan fito a matsayin da zai saɓa da addini da al’adata ba”.
Jarumar ta ce babu wani “bambanci tsakanin yadda ake yin fina-finan Kannywood da na Nollywood idan ban da bamabancin harshe. Don haka na ji daɗin soma fitowa a fina-finan Nollywood”.

Babu Bambamci Tsakanin Fina Finan Kannywood Da Nollywood – Inji Hadiza Gabon

Kamar Yadda Kowa Yasani A Wannan Zamani Damuke Ciki Babu Mawakan Hausa Da Tauraruwarsu Take Haskawa Kamara Wadannan Mawaka Guda Biyu Wato Umar M Sharif Da Nura M Inuwa.
Wannan Daliline Yasa Mukeso Muyi Muhawara Domin Banbance Aya Da Tsakuwa A Tsakanin su Ta Hanyar Jin Ra’ayoyin Masoyansu.
Muhawarar Anan Itace Acikin Wadannan Faishan Mawaka Guda Biyu Wanene Salonsa, Kida, Lafazi, Murya Yafi Burgeka Acikinsu???
Ajiye Ra’ayinku Domin Jin Wanye Zaici Wannan Muhawara

Salo, Kida, Lafazi, Murya: Wani Abu Ne Yafi Bambamta Wakar Nura M Inuwa Data Umar M Sharif?

Sabuwar tauraruwar masana’antar Kannywood tace zata koma makaranta kuma idan Allah yayi ta samu miji zata yi aure.
Sabuwar tauraruwar fina-finan hausan na Kannywood Maryam Yahaya ta bayanar cewa yin fim ba zai hanata yin karatu domin yin karatu yana cikin abubuwan dake gaban ta a rayuwa.
A wata hira ta musamman da tayi da BBC hausa, Maryam wanda ta kammala karatu ba da dadewa tace tana kokarin cigaba da yin karatu.
Jarumar shirin “Mansoor” tace idan Allah ya nufe ta da samun miji yanzu zata yi aure kuma zata cigaba da yin karatun ta.
Sabuwar tauraruwa wanda ta fara haskawa cikin “Mansoor” bayyana cewa idan tayi aure bazata cigaba da yin fim.
Maryam Yahaya ta shigo masana’antar kannywood da kafar dama domin bayan fitowar ta a cikin “Mansoor” ta samu damar fitowa a wasu shiri da dama.
Ko zamu iya cewa wannan matashiyar zata sauya jarumtakar manyan yan wasan masana’antar kamar su Rahama sadau, Nafisa Abdullahi, Halima Atete, Hadiza Gabon da dai sauransu?

Zan Koma Makaranta Kuma Idan Nasamu Miji Zanyi Aure – inji jaruma Maryam Yahaya

Mesut Ozil na shirin kin yadda ya tsawaita yarjejeniyar ci gaba da zama a Arsenal, bayan da dan kwallon ke son komawa Manchester United in ji jaridar Daily Mirror.
Sunday Express ta wallafa cewar Liverpool ta bukaci Barcelona da ta daina matsawa Philippe Coutinho a lokacin da ta yi kokarin sayen dan kwallo, inda Liverpool ta ki sayar da shi.
The Sun kuwa cewa ta yi Manchester City ta damu matuka cewar Paris St-Germain za ta bai wa Arsenal makudan kudi domin ta dauki Alexis Sanchez.
An shaidawa Manchester United ta biya fam miliyan 75 idan tana son daukar dan wasan Lazio, Sergej Milinkovic-Savic, itya ma Manchester City na son sayen dan kwallon in ji Daily Express.
Everton za ta taya dan wasan Arsenal Olivier Giroud a watan Janairun 2018, har ma ta tanadi fam miliyan 40 in ji Daily Mirror.
Daily Mail kuwa ta wallafa cewar ran Arsene Wenger ya baci matuka da ya sayar da Kieran Gibbs ga West Brom, fiye da barin Alex Oxlade-Chamberlain da ya koma Liverpool.
Tura wannan labarin

Tirkashi: ''Ozil na shirin komawa Man United''

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma Abuja bayan da ya yada zango a birnin Landan daga Amurka, inda ya halarci babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 72 a makon jiya.
Fadar shugaban kasar ce ta tabbatar wa BBC komawar shugaban gida.
Sai dai ba ta yi karin haske ba game da abin da shugaban ya yi a Landan ba.
Shugaban ya isa Landan ne ranar Alhamis daga birnin New York na Amurka.
Kafin tafiyarsa, shugaban ya gabatar da jawabi a zauren Majalisar Dinkin Duniya ranar Talata.
Da ma dai fadar shugaban ta ce zai je Birtaniya bayan ya kammala taron.
Sanarwar da kakakin shugaban kasar Femi Adesina ya aikewa manema labarai a makon jiya ta ce shugaban "Zai je birnin Landan a kan hanyarsa ta komawa gida".
Sai dai Mr Adesina bai yi karin bayani kan abin da zai sa Shugaba Buhari zuwa London ba.
A watan jiya ne dai shugaban ya koma gida Najeriya bayan ya yi doguwar jinya a Birtaniya, inda ya shafe fiye da wata uku a can.

Buhari ya koma gida

Duniya kullun kara samun cigaba akeyi ta bangaren kirkiro sabbin kwalliya musamman ta bangaren mata yanda zasu rika jan hankulan mutane da birgewa, wannan wata baiwar Allahce data fito da sabon salon gashin gira, ana iya gani yanda tayi kitso dashi kamar gashin kai a wannan hoton.

Sabon Salo: Gashin gira da kitso

Diyar marigayi tsohon shugaban kasa Hajiya Fatima Gumsu Sani Abacha kenan take taka rawar shoki a gurin shagalin bikin zagayowar ranar haihuwarta, anokai da 'yan uwa sun taru dan tayata murna muma muna kara tayata murna da fatan Allah ya karo shekaru masu albarka.

Ashe rawar shoki hadda manya?: Fatima Sani Abacha na takawa a gurin shagalin zagayowar ranar haihuwarta

Tsohuwar jarumar finafinan Hausa matar Sani Musa Danja Zaki, Mansurah Isah taja hankulan wasu mutane da suke yiwa jaruman finafinan Hausa kudin goro a duk lokacin da aka samu wata ko wani jarumi da yin ba daidaiba, Mansurah tace suma fa mutanene kuma musulmai kuma masu zagin nasu basusan irin ayyukan alherin da suke aikatawa na farantawa Allah a boyeba.
Ta kara da cewa akwai jarumai da dama da take samu akan nemawa wasu bayain Allah da suke cikin halin kaka nikayi taimako kuma haka wadannan jaruman zasu bayar da taimako su kuma bukaceta da kada ta bayyanawa Duniya.
Gadai cikakken bayanin da Mansurah tayi:
"Assalamu alaikum. Yan uwana musulmai, wallahi wallahi kuji tsoron Allah. Ku tuna akwai hisabi, Duk abinda yan film sukayi, sai kunyi suka. Kar ku shiga tsakani BAWA da UBANGIJIN sa, domin bakusan abinda yake yi a boye dan farantawa ubangiji rai ba. Mun kawo case din UMMASALAMA domin a ceto ranta, wacce take bukatan taimako cikin gaggawa, wassu suka fara zagin yan film, wai mai sukeyi, Ina duk kudin da suke tarawa? Ku kusan abinda yan film din sukeyi? Ko halin da suke ciki? Shi yasa duk Sanda wani ko wata yar film ta kirani dan taimakawa, nakan so, na rubuta ba dan komai ba, dan asan abinda sukewa jamaan gari. Akwai case din yara da aka haifa da #diabeties, a nan na rubuta cewa duk wata suna bukatan #insulin domin Karin lafiyan su, waya tuna dasu a watan nan? Babu sai Yan film. Case da muke dashi bana ummasalama kadai bane, muna da case irin na ummasalama sunfi thousands ( dubu ), ko kusan guda nawa yan film suka biya musu kudin asibiti ko magani? Ko aika musu da kayan abinci? Kuma mutanen nan ba yan film bane. @adam_a_zango @officialsanidanja @yakubu_mohd @realalinuhu musha case dasu, duk Sanda na kai musu case din wassu dan su taimaka. Sai nayi musu alkawari cewa banzan fadawa kowa ba ko na rubuta a page Dina. Nasha nuna musu cewa gara duniya tasan abinda kukayi, domin wassu mutane jakuna ne, basu tauna magana kafin su fada, yan film suna iya kokarin su na taimakawa al'ummah Wanda ba yan film ba, Amma da zarran case na yar film ta taso, sai ku fara zagi kamar su ba musulmai bane, kamar in kun taimaka haram ne, kai kayi aikin ladan ka mana, tsakanin ka da ubangijin ka in kana da hali. Ka barwa Allah komai. Nasha kawo case page Dina, wallahi Christians sun sha min dm na bada gudunmowa, har mamaki suke bani, Amma wai musulmi ne zai fara zagi da zarra kace ya taimaka, ko waya kayi musu, zasuyi alkawari bazasu cika ba. Ina mai bada hakuri ga mijina da sauran yanfilm da ake zagi a dalilina, suyi hakuri su kuma ci gaba da aikin lada. Kuma neman taimako ta kowacce iri ne, banzan daina neman wa mutane ba, in har naji labari ko an kawo min case dinsu. Allah ya shige mana gaba ameen. Allah ka bani ikon ci gaba da taba rayuwan al'umman ka domin shine farin cikina."
"Ni tambaya ta a nan, kudin yan film ne kadai ake taimako dashi? Ko kuwa su kadai Allah yace suyi taimako? Ina laifin Wanda yace, wa mai son aikin lada gashi yayi? Ba'ace dole a taimaka ba, duk mai so ko mai hali bisimillah. Kai a matsayin ka na musulmi ai ya kamata kasan cewa duk abinda bawa zaiyi, sai Allah ya yarda mishi, aure, haihuwa, shiriya, arziki, taimako, lafia, mutuwa duk sai da yardan ubangiji. Kar ku bari bakin ciki da jahilci yaci gallaba azuciyan ku. Shikenan in dan film yayi sallah sai yace Allah kayiwa yan film albarka su kadai? Ko Wanda ba dan film ba, sai yace Allah yayiwa mutane albarka Amma banda dan film? Duk daya muke a gaban ubangiji. Wallahi taimakon da yanfilm sukeyiwa a waje, ba kadan bane. Amma baku gani. Daga anyi magana sai kuce dan film. Why? Menene dan film ne? Wata hallita ce daban ko yaya? Ba uwace ta haife su ba ko ba bayin Allah bane? Ko akwai inda aka fada acikin alqurani cewa kayi taimako Amma banda dan film ? Allah ubangiji ya saka da alheri ga dukanni masu taimako, Wanda suke taimakawa a boye dana fili ameen. Allah ya shirye mu gabaki daya. Masu taimako Allah ka Kara musu budi ameen, masu niya kuma Allah kada iko ameen."
Sai muce Allah shi kyauta.

"Jama'a Ku daina yiwa 'yan fim kudin goro bakusan aikin alherin da sukeyi a boyeba">>Mansurah Isah

WACECE MACE TA GARI? //5
ITACE MAI NEMAN ILIMI
Ilimi da aiki dashi shima yana daga cikin matakin farko ga dukkan macen da take son zama ta gari. Ya zama dole ta yi aiki da hadisin Manzon Allah (SAW) cewa: "Neman ilimi wajibi ne akan dukkan musulmi da musulma". Wannan yana nuna babba da yaro, mace ko namiji, tsoho da matashi.
Duk macen da ba ta da ilimi kuma bata neman sa to hakika zaman ta na gari zayyi mata wahala. Saboda bata da fitilar da zai rinqa haska mata hanyar ta (rayuwarta).
Kuma kada ki ce wai kin yi sauka shikenan kin bar neman ilimi a'a ki cigaba da zuwa in da za a  rinqa tunatar dake Allah, In da za a koya miki hanyoyin shiga Aljannah, in da za'a rinqa koya miki zamantakewar magabata don ke ma ki yi koyi dasu. In da za a koya miki yanda zaki tarbiyyantar da 'ya'yanki.
Kin ga in a gida kike dukkan wainnan garabasar zasu rinqa wuce ki, kuma a hankali sai shaidan yayi galaba a kanki ki zama kamar ba ke ce mahaddaciyar nan ba mai bin Allah.
Sannan shi ilimi kogi ne yana dayawa, cigaba da nema shine zai sanya miki son addini da son ibada, kuma za'a rinqa miki wa'azi a hankali kina gyara halin ki.
Da sauraren wa'azin malaman Sunnah, ko a radio ko a TV kada dai ki zauna baki da wata kafa da zata rinqa koyar dake addini.
Da koyan Qur'ani da karanta shi domin samun lada da koran shaidanu a gidan auren ki.
Sannan uwa uba ilimi zai taimaka ma 'ya'yanki, domin zaki taya su tilawa a gida, zaki musu assignment. Kin ga kuwa dole mace ta gari ta nemi ilimi.
Ba na addini kadai ba har da na zamani, don ki san me duniya take ciki, saboda idan kina tunani ta bangare daya zai iya kawo naqasu ga 'ya'yanki.
Yar'uwar ku Sadeeya Lawal Abubaka

WACECE MACE TA GARI? //5

WACECE MACE TA GARI? //4
ITACE MAI IBADA
Bauta dai shine dukkan abun da Allah Yake so kuma Ya yarda da shi na daga zance da aiki.
Kuma duk mace ta gari zaka same ta da ibada, wato mai dagewa ce wurin bautar Ubangijinta. Sannan tana tsoron Allah da qanqan da kai garesa.
Kuma ta aminta tun daga farkon auren ta cewa aure ibada ne kuma Sunnah ne mai qarfi zata raya. Kuma duk abun da take yi a cikin gidan ta tun daga zaman auren tana da lada. Idan mace ta sa haka a ranta abubuwa dayawa a rayuwar aure zasu zo mata da sauki.
Itace mai dogaro ga Allah a cikin dukkan al'amuranta, kuma tana komawa gare shi a lokacin yalwa da lokacin tsanani. Kuma tana godiya gare Shi a cikin ko wane hali.
Mace ta gari sam bata wasa da sallolin ta biyar a gidan ta. Kuma ba a barin ta a baya wato tana tashi cikin dare ta roqi alkhairan duniya da lahira.
Tana qoqarin yin azumin nafila tare da izinin mijin ta.
Tana qoqarin yin kyauta da sadaqa.
Tana dagewa wurin yin addu'a. Duk abun da ya same ta na rayuwa to ta kan tsananta roqo.
Mai yawan ambaton Allah ce da Istigfari. Bakin ta danye yake wurin ambaton Allah ba ashar da maganganu marasa amfani ba.
Tana yin biyayya ga mijinta in har umurninsa bai sabawa mahalicci ba.
Kuma tana dagewa da sauran ibadodi na samun lada.
In baku manta ba Annabi (SAW) ya fada a hadisi:
(( ﺇِﺫَﺍ ﺻَﻠَّﺖِ ﺍﻟْﻤَﺮْﺃَﺓُ ﺧَﻤْﺴَﻬَﺎ، ﻭَﺻَﺎﻣَﺖْ ﺷَﻬْﺮَﻫَﺎ، ﻭَﺣَﻔِﻈَﺖْ ﻓَﺮْﺟَﻬَﺎ، ﻭَﺃَﻃَﺎﻋَﺖْ ﺯَﻭْﺟَﻬَﺎ، ﻗِﻴﻞَ ﻟَﻬَﺎ : ﺍﺩْﺧُﻠِﻲ ﺍﻟْﺠَﻨَّﺔَ ﻣِﻦْ ﺃَﻱِّ ﺃَﺑْﻮَﺍﺏِ ﺍﻟْﺠَﻨَّﺔِ ﺷِﺌْﺖِ .(( ‏[ ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺣﻤﺪ ].
" Idan Mace ta yi sallolinta biyar, ta yi azumin Ramadan, ta kuma kiyaye farjinta, sannan ta yi biyayya wa mijinta, Sai ace da ita: "Ki shiga aljannah daga qofar da ki ka gadama daga cikin qofofin Aljannah" [Ahmad ‏] .
Babu yanda za a yi a kira ki ta gari bayan kina tsallake sallah, wato yin sallah yana miki wahala.
Inaa! mace ta gari ta miki nisa, don ita rige-rige take wajen ganin ta kusanci Mahaliccin ta.
Yar'uwar ku Sadeeya Lawal Abubakar

WACECE MACE TA GARI? //4 ITACE MAI IBADA

WACECE MACE TA GARI? //3
ITA CE MUSULMA MU'UMINA
Farkon matakin zama ta gari shine ta kasance musulma. Musulma kuma ita ce wacce ta yi imani da Allah ta kadaita Sa a matsayin abun bautar ta, Kuma ta miqa wuya ga Allah ta hanyar miqa wuya ga umurninSa da dokokinSa.
Kuma ta yi imani da Annabi Muhammad ta hanyar yi masa da'a a umurninsa da gasgatasa a labaransa, da nisantar haninsa, da bautawa Allah kadai ta hanyar da ya shar'anta. Ta tsaida Sallah da haqqoqinta. Ta bada zakka, ta azumci watan Ramadana kuma ta je aikin hajji in ta samu iko. Wannan ce cikakkiyar musulma.
Sannan ta dauki matakin zama Mu'umina, shine imani da Allah da Mala'ikunsa, da Manzannin sa, da Litattafan sa, da Ranar qarshe, da imani da Qaddara mai kyau ko mara kyau.
Ba zaki taba zama ta gari ba har sai kin yi imani da wainnan abubuwan tun daga nan ne zaki fara ginin zama ta gari.
Don wata a dabi'un ta da halayen ta sai ka tambayi kanka anya kuwa wannan matar ta yi imani da waincan abubuwan da na ambata kuwa. Saboda gaba daya ta bar imanin ta da rukunan musulunci sun yi rauni. Kuma ta siyarwa shaidan da imanin ta, tana shirka da Allah tamkar bata yi imani da Shi a matsayin abun bautar ta ba.
Yar'uwar ku Sadeeya Lawal Abubakar

WACECE MACE TA GARI? //3

KU KARANTA TARIHI, DON AKWAI WA'AZI A
CIKINSA!
ﺍﻗﺮﺅﻭﺍ ﺍﻟﺘﺎﺭﻳﺦ ﺇﺫ ﻓﻴﻪ ﺍﻟﻌﺒﺮ *** ﺿﻞ ﻗﻮﻡ ﻟﻴﺲ ﻳﺪﺭﻭﻥ
ﺍﻟﺨﺒﺮ
Shaikhul Islami Ibnu Taimiyya (r) yake cewa:
ﻛﺎﻥ ﺍﻟﻤﺸﻬﻮﺭ ﻣﻦ ﻣﺬﻫﺐ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﺃﻧﻬﻢ ﻻ ﻳﺮﻭﻥ ﺍﻟﺨﺮﻭﺝ
ﻋﻠﻰ ﺍﻷﺋﻤﺔ، ﻭﻗﺘﺎﻟﻬﻢ ﺑﺎﻟﺴﻴﻒ ﻭﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﻓﻴﻬﻢ ﻇﻠﻢ، ﻛﻤﺎ ﺩﻟﺖ
ﻋﻠﻰ ﺫﻟﻚ ﺍﻷﺣﺎﺩﻳﺚ ﺍﻟﺼﺤﻴﺤﺔ ﺍﻟﻤﺴﺘﻔﻴﻀﺔ ﻋﻦ ﺍﻟﻨﺒﻲ -
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ; - ﻷﻥ ﺍﻟﻔﺴﺎﺩ ﻓﻲ ﺍﻟﻘﺘﺎﻝ ﻭﺍﻟﻔﺘﻨﺔ
ﺃﻋﻈﻢ ﻣﻦ ﺍﻟﻔﺴﺎﺩ ﺍﻟﺤﺎﺻﻞ ﺑﻈﻠﻤﻬﻢ ﺑﺪﻭﻥ ﻗﺘﺎﻝ ﻭﻻ ﻓﺘﻨﺔ .
ﻓﺈﻧﻪ ﻳﺪﻓﻊ ﺃﻋﻈﻢ ﺍﻟﻔﺴﺎﺩﻳﻦ ﺑﺎﻟﺘﺰﺍﻡ ﺃﺩﻧﺎﻫﻤﺎ، ﻭﻟﻌﻠﻪ ﻻ ﻳﻜﺎﺩ
ﻳﻌﺮﻑ ﻃﺎﺋﻔﺔ ﺧﺮﺟﺖ ﻋﻠﻰ ﺫﻱ ﺳﻠﻄﺎﻥ، ﺇﻻ ﻭﻛﺎﻥ ﻓﻲ
ﺧﺮﻭﺟﻬﺎ ﻣﻦ ﺍﻟﻔﺴﺎﺩ ﻣﺎ ﻫﻮ ﺃﻋﻈﻢ ﻣﻦ ﺍﻟﻔﺴﺎﺩ ﺍﻟﺬﻱ ﺃﺯﺍﻟﺘﻪ .
"Abin da ya shahara a mazhabar Ahlus Sunna shi
ne; ba sa ganin halaccin tawaye ma shugabanni,
da kuma yakarsu da makami, ko da kuwa suna
da zalunci. Kamar yadda ingantattun Hadisai
masu yawa suka zo daga Annabi (saw). Saboda
barnan da yake cikin yakar nasu, da fitinar da
take cikin hakan, girmanta ya fi barnan da za a
samu a sakamakon zaluncinsu in ba a yakesu ba,
ko ba a tada fitina ba. Saboda ana kawar da
barna mafi girma ne a cikin barna guda 2, ta
hanyar amfani da karamar barnar. Ta yiwu kusan
ba a san wata jama'a da ta yi tawaye ma
shugaba mai iko ba, face barna mafi girma ta
faru a dalilin tawayen fiye da barnar da suka
kawar".
Duba Minhajus Sunna 3/ 391.
* Abin lura:
1. Ma'ana; barnar zubar da jinane da kisan
mutane da shugabanni suke yi in an yi musu
tawaye, ya fi barnar zaluncin da suke yi wa
mutane in aka yi hakura aka bi su. Don haka sai
ayi ta hakuri da zaluncin da suke yi, don gudun
barnar da zai faru na kashe mutane da barnata
dukiya in an yi musu tawayen, kamar yadda yake
faruwa a wasu kasashen musulmi a yau.
2. Sai mun gyara kawukanmu, mun gyara
Addininmu sai Allah ya gyara mana shugabanni.
** WAIWAYE ADON TAFIYA, TARE DA DR. SANI R/
LEMO:

KU KARANTA TARIHI, DON AKWAI WA'AZI A CIKINSA! DR. SANI UMAR R-LEMO (HAFIZAHULLAH)

*TAMBAYOYI DARI (100) DA AMSA AKAN MATA:  HAILA, JININ BIKI, SALLAH, AZUMI DA HAJJI.*
Fitowa ta 1
Daga: *_Sheikh Muhammad Saleh al-Uthaimeen, Rahimahullah_*
*TAMBAYA TA 1*
Shin mace me jinin biki zata zauna har kwana arba'in ne ba zatayi sallah ba kuma ba zatayi azumi ba, ko kuma abin lura daga gareta za tayi tsarki, tayi sallah, kuma nawa ne mafi hawan kwanakin da za tayi kafin ta yi tsarki?
*AMSA:*
Mace mai jinin biki bata da kyayyadadden lokaci sai dai duk lokacin da jini ya zo mata zata zauna ba za tayi sallah ba kuma ba za tayi azumi ba kuma mijinta ba zai iya saduwa da ita ba. Amma idan taga jini ya dauke, wato ta tsarkaka ko da ko kafin ta cika kwana arba'in ne ko da jinin iyakacin  kwana goma ne kawai yayi ko kwana biyar kawai sai ya dauke, to sai tayi wanka tayi sallah, tayi azumi kuma mijinta ya sadu da ita babu laifi acikin hakan.
Sai dai abin da yafi muhimmanci shine shi jinin biki al'amari ne kebantacce kuma hukuncinsa yana ratayuwa ne da shi, wato idan jinin yazo to hukuncinsa yana nan ba za tayi sallah da azumi ba. Kuma idan jinin bai zo ba to hukhncinsa baya nan. Duk lokacin da tayi tsarki to ta wofanta daga hukuncinsa.
Sai dai idan jinin ya karu matar ta Zamo mai jinin istihada, wato jinin ciwo ke nan, sai tayi lissafin iya kwanakin al'adarta sai tayi wanka tayi sallah. Sai ta nemi maganin wannan jinin na cuta.
Muhadu a fitowa ta 2 in sha Allahu Ta'ala
✍Tattarawa:
Dan uwanku a Musulunci
*_Umar Shehu Zaria_*
Daga: *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*

TAMBAYOYI DARI (100) DA AMSA AKAN MATA: HAILA, JININ BIKI, SALLAH, AZUMI DA HAJJI

Complete Tafsir Sheikh Abdulmudallib muhd
Auwal Gusau (Hafizahullah)• na daya zuwa na
Ashirin da biyar 1- 25 lakcoci 4 1438/2017
TARE DA : Jibwis Social Media Kano State •
Day 1 DOWNLOAD HERE
Day 2 DOWNLOAD HERE
Day 3 DOWNLOAD HERE
Day 4 DOWNLOAD HERE
Day 5 DOWNLOAD HERE
Day 6 DOWNLOAD HERE
Day 7 DOWNLOAD HERE
Day 8 DOWNLOAD HERE
Day 9 DOWNLOAD HERE
Day 10 DOWNLOAD HERE
Day 11 DOWNLOAD HERE
Day 12 DOWNLOAD HERE
Day 13 DOWNLOAD HERE
Day 14 DOWNLOAD HERE
Day 15 DOWNLOAD HERE
Day 16 DOWNLOAD HERE
Day 17 DOWNLOAD HERE
Day 18 DOWNLOAD HERE
Day 19 DOWNLOAD HERE
Day 20 DOWNLOAD HERE
Day 21 DOWNLOAD HERE
Day 22 DOWNLOAD HERE
Day 23 DOWNLOAD HERE
Day 24 DOWNLOAD HERE
Day 25 DOWNLOAD HERE
# Lakcocin Ramadan#
1- DOWNLOAD HERE
2- DOWNLOAD HERE
3- DOWNLOAD HERE
4- DOWNLOAD HERE
            Kuyi Sauraro lafiya
°°°°°°°°°°°
Ku cigaba da kasan cewa da
www.facebook.com/socialmediakano
JIBWIS SOCIAL MEDIA KANO•
wannan tafseeran sun zo muku ne karkashin kwamitin 
JIBWIS SOCIAL MEDIA KANO

Complete Tafsir Sheikh Abdulmudallib muhd Auwal Gusau (Hafizahullah)• na daya zuwa na Ashirin da biyar 1- 25 lakcoci 4 1438/2017

Complete Tafsir Dr. Sani Umar Rijiyar lemo
(Hafizahullah)• 1438/2017
TARE DA : JIBWIS SOCIAL MEDIA KANO•
Day 1 DOWNLOAD HERE
Day 2 DOWNLOAD HERE
Day 3 DOWNLOAD HERE
Day 4 DOWNLOAD HERE
Day 5 DOWNLOAD HERE
Day 6 DOWNLOAD HERE
Day 7 DOWNLOAD HERE
Day 8 DOWNLOAD HERE
Day 9 DOWNLOAD HERE
Day 10 DOWNLOAD HERE
Day 11 DOWNLOAD HERE
Day 12 DOWNLOAD HERE 
Day 13 DOWNLOAD HERE
Day 14 DOWNLOAD HERE
Day 15 DOWNLOAD HERE
Day 16 DOWNLOAD HERE
Day 17 DOWNLOAD HERE
Day 18 DOWNLOAD HERE
Day 19 DOWNLOAD HERE
Day 20 DOWNLOAD HERE
Day 22 DOWNLOAD HERE
Day 23 DOWNLOAD HERE
Day 24 DOWNLOAD HERE
Day 25 DOWNLOAD HERE
Day 26 DOWNLOAD HERE
Day 27 DOWNLOAD HERE
        Kuyi Sauraro lafiya
°°°°°°°°°°°
Ku cigaba da kasan cewa da
www.facebook.com/socialmediakano
JIBWIS SOCIAL MEDIA KANO

Complete Tafsir Dr. Sani Umar Rijiyar lemo (Hafizahullah)• 1438/2017 TARE DA : JIBWIS SOCIAL MEDIA KANO

Complete Tafsir. Dr. Abdullah Sale pakistan
(Hafizahullah)• 1438/2017
TARE DA : Jibwis Social Media Kano State •
Day 1 DOWNLOAD HERE
Day 2 DOWNLOAD HERE
Day 3 DOWNLOAD HERE
Day 4 DOWNLOAD HERE
Day 5 DOWNLOAD HERE
Day 6 DOWNLOAD HERE
Day 7 DOWNLOAD HERE
Day 8 DOWNLOAD HERE
Day 9 DOWNLOAD HERE
Day 10 DOWNLOAD HERE
Day 11 DOWNLOAD HERE
Day 12 DOWNLOAD HERE
Day 13 DOWNLOAD HERE
Day 12 DOWNLOAD HERE
Day 13 DOWNLOAD HERE
Day 16 DOWNLOAD HERE
Day 17 DOWNLOAD HERE
Day 18 DOWNLOAD HERE
Day 19 DOWNLOAD HERE
Day 20 DOWNLOAD HERE
Day 21 DOWNLOAD HERE
Day 22 DOWNLOAD HERE
Day 23 DOWNLOAD HERE
Day 24 DOWNLOAD HERE
Day 25 DOWNLOAD HERE
Day 26 DOWNLOAD HERE
     Kuyi Sauraro lafiya
        °°°°°°°°°°°
Wannan tafsirai zun zo muku ne karkashin kulawar jibwis social media kano
Ku cigaba da kasan cewa da
JIBWIS SOCIAL MEDIA KANO•

Complete Tafsir. Dr. Abdullah Sale pakistan (Hafizahullah)• 1438/2017

SHUGABAN YAN KOGO GOGAGGEN
MAKARYACI NE
ABUN YA BANI MAMAKI KAMAR YADDA AUDU YAKE* *KIRARIN CEWA SHINE SHUGABAN MASU WA'AZI
TO TA TABBA SHINE
SHI TACECCEN MAKARYA CI NE.
Ga yadda Abun ya ke
Abduljabbar Nasiru kabara ya bude baki baya jin kunya baya jin tsoran Allah yace babu inda annabi (s a w) yace a dage tufafi (wando).
      *Ga Audion* *Yadda ya fada daga bakin sa*
DOWNLOAD HERE
Yace  duk wanda ya fada to karya yake,
To anan zaku kara gane karyar sa kamar yadda ya gada  a wajan waliyiya…
1- To kamar yarda yace babu inda Annabi yafada to yanzu zan nuna masa wajan,
Malaman musulunci sun fitar da Hadisai a cikin littafan su
Gasu kamar haka
[Bukhari, Abu dawud, Ibn Majah da Ahmad suka fitar dashi.
Hadisin yana cewa Annabi (saw) yace
"Duk abinda ya wuce idon
sawu na tufafi (Riga, gwado/kwarjalle) to yana cikin wuta.
A wani hadisin kuma daga Abu
hurairah (ra) Yace Annabi (saw) yace: "Allah ba zai kalli wanda ya ja tufafinsa akasa ba saboda girman kai".
Acikin wani Hadisi kuma
Annabi (saw) ya ce: "Mutum uku Allah ba zai yi magana dasu ba a ranar Al- Qiyamah kuma ba zai dube su ba (kallo na rahma)
kuma zai tsarkake su ba kuma suna da azaba mai girma; na farko daga cikinsu shi ne mai sakin tufafinsa ya wuce idon sawu".   [Imam Muslim da Abu dawud, da Nisa'i da Ibn Majah da Ahmad da Darimi].
2- Abu na Gaba   shine rashin sanin Qur'ani da yayi
Shi gogagge wato idan yana Karatun Qur'ani Anan zaka gane wallahi anyi Asarar Kudin tara,
Amma idan waka ce to abun zai baka mamaki, ga yadda Abun yake.
A cikin Surah Maryam 59
Inda Allah yake cewa:-
فَخَلَفَ مِنۢ بَعْدِهِمْ خَلْفٌ أَضَاعُوا الصَّلٰوةَ وَاتَّبَعُوا الشَّهَوٰتِ ۖ فَسَوْفَ يَلْقَوْنَ غَيًّا
To kuma  Gogaggen Mai wa'azi Sai yace 
وخلفة في خلف أضا عوا الصلوة واتبعوا الشهوت فسوف يلقون غيا
Ga Audion daga bakin sa
              *Karatun Sarkin Kogo*
----------
*Gyaran daga bakin Sheikh ja'afar Mahmud adam*
Allah Sarki Abun A zubar da hawaye amma  su yan kogo sun kasa gyara masa irin wannan tabar gazaka da yayi.
Ga audion kaji yadda ya sassara wannan aya
Sannan ka saurari gyaran daga bakin gangaran kafi gwani wane gwani ciki fal shakku wato sheikh ja'afar Mahmud adam, Allah yayi masa rahma
Mai sauraro kayi Alkalanci na gaskiya idan kaji...
3- Abu na gaba shine abu na uku
shima dai tabar gaza ce akan Qira'ar gogaggen makaryaci.
A cikin surah Al-Ahzaab : aya ta 58.  Allah yana cewa
وَالَّذِينَ يُؤْذُونَ الْمُؤْمِنِينَ وَالْمُؤْمِنٰتِ بِغَيْرِ مَا اكْتَسَبُوا فَقَدِ احْتَمَلُوا بُهْتٰنًا وَإِثْمًا مُّبِينًا
Shi kuma gogagge tacaccan makarya ci sai ya ce
الذير مون المو منين بغير مااكتسبو فقد احتملوا بهتنا واثما مبينا.
Allah sarki Amma Abun mamaki an rasa wanda zai gyara masa.
shima ga Audion ka saura -
*karatun Sarkin kogo*
*Shima Gyaran daga bakin Sheikh ja'afar Mahmud adam*
Sannan ka saurari gyaran daga bakin gangaran kafi gwani wane gwani ciki fal shakku wato sheikh ja'afar Mahmud adam, Allah yayi masa rahma.
   
Mai Sauraro Kaine Alkhali kana da hankalin da zaka fahinci yadda Abun yake
°°°°°°°°°°°°°°°°
Wannan shine fita ta daga cikin jerangiyar abubuwan da zan kawo muku na karerayin Audu wazirin Shi'a
nan gaba insha Allah har video zan haska yadda Abubuwan suke gudana .

SHUGABAN YAN KOGO GOGAGGEN MAKARYACI NE ABUN YA BANI MAMAKI KAMAR YADDA AUDU YAKE* *KIRARIN CEWA SHINE SHUGABAN MASU WA'AZI TO TA TABBA SHINE SHI TACECCEN MAKARYA CI NE.