The Money Never Sleep Music Records #MNS Super Star Olabeewhy Is Back Again With Another Banging Hit Titled Jawabi Feat Arewa Super Star B.O.C Madaki Aka Barde Ogan Chasu.

Downlord mp3

Naijabasic

Olabeewhy – Jawabi Feat Boc Madaki

Wata mata me sana'ar sayar da abinci da ta mutu a kasar Ghana kenan a wannan hoton, ana bikin binne tane sai aka samu kujera aka zaunar da ita aka kawo turmi da tabarya da kuma sakwara, irin dai sana'ar da takeyi lokacin tana da rai.
Irin wannan shagali da akayi wajan binne ta ya dauki hankulan mutane domin ba kasafai aka saba ganin hakan ba.

Kalli wata mata da ta mutu amma sai gata tana daka sakwara a wajan da za'a binneta

 Wani rashin fahimta yaso ya shiga tsakanin taurarin mawakan gambara na Arewa, watau Classiq da Morell, inda har ta kai ga Classiq din ya rubutawa Morell budaddiyar wasika da ya wallafa a dandalinshi na sada zumunta, maganar dai akan wata wakace da sukayi tare me suna 'Ba Wani Bughatti' wadda Morell din ya saki ba tare da sanin Classiq ba.
Classiq ya bayyana cewa yaji dadin kasancewa a cikin wakar da akayi amma abinda ya batamai rai shine yanda aka sauya salon wakar aka kuma sake ta ba tare da sanar dashi ba, ya kuma cewa idan dai ba anyi da wata manufa bace ta daban ya kamata ace yasan da wannan lamari.
A nashi bangaren, Morell ya bayar da amsar cewa wani abokin aikinshine yayi wannan canje-canje a wakar ya kuma sake ta saboda doki, ba tare da saninshi ba, ya kara da cewa bashi da niyyar sakin wakar yanzu dan yana ganin lokaci be yiba.
Amma a karshe yana baiwa Classiq din hakuri akan wannan lamari ba zai taba yin wani abu da zai bata musu sana'a ba, ya kuma kara da cewa, aikinsu yayi magoya bayansu sun nuna soyayya sosai.


Tirkashi Anyi musayar yawu tsakanin Classiq da Morell kukaranta

 Tauraruwar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi ta nuna halin dattaku wajan mayarwa da wata da ta kirata da sunan 'Karuwa' bayan da Nafisar ta saka wasu hotunan ta a dandalinta na sada zumunta.
Baiwar Allan ta cewa Nafisa, 'Karuwar Banza'
Amma sai Nafisar ta danne zuciyarta ta bata amsa da cewa 'Allah ya saka da Alheri'




Kukaranta kuji amsar da nafeesa abdullahi ta baiwa wata data ce mata karuwa

Diyar gwamnan jihar Kano, Fatima Abdullahi Umar Ganduje kenan Amaryar dan gwamnan jihar Oyo, Idris Ajimobi a wannan hoton nata na kwanannan.

Kalli wani hoton Fatima Ganduje na kwanannan

(YOUNG DEES RECORD) presents Sara Ganga the hip hop Famale monster Come with another fire which she had features 2 rappers ( BOC MADAKI king of the North sound music Rappers & ( KAITA HARD CORE RAPPER) TITLE [ANATARE]

Downlord mp3 here

©Asprotech.cf

Lil Pee ANATARE Ft B.O.C Madaki & KAITA

Auta wazirin waka, ya waiwayi fans da wata sabuwa, wannan karan ya hada da hausa and English tare da jarima SIMI (joromi hausa version) kada a barka a baya click download listen and share tnx.

Downlord mp3

©naijabasic.net

Auta waziri ft Simi =Joromi Hausa Version

 Tauraron fina-finan Hausa, Bello Muhammad Bello, General BMB ya mayarwa da wani daya sokeshi da cewa yayi koyi da mata martani, mutumin dai ya cewa Bello ne yayi koyi da mata saboda hujin kunne da ya ke dashi.
Bello ya mayar wa da mutumin martanin cewa wace ayace ko hadisi tace ayi ko kar ayi hujin kunne, shin ya san ma wanene ya fara hujin kunne?, ko kuma wace ayace ko hadisi tace matane kadai zasu yi hujin kunne? Bello ya kara da cewa yawanci anyi gadon musuluncine amma ba'a sanshi a ilimance ba, inda ya shawarci mutumin daya san abu kamin yayi magana akanshi.


Wace aya ko hadisi tace matane kadai zasuyi hujin kunne?>>General BMB ya mayarwa da wani da yace mai yayi koyi da mata martani

 A dazune tauraron fina-finan Hausa, Bello Muhammad Bello, General BMB ya bayyana cewa daga yau ya dena biyewa masu zaginshi a shafinshi na yanar gizo, Bello ya kara da cewa bazai sake mayar da mummunar kalama da mummunar kalma ba, zaiyi koyi da koyarwar Manzon Allah(SAW).
Abokin aikinshi, Adam A. Zango ya jinjinawa Bellon akan wannan shawara da ya yanke inda yace mai, yauzu kake magana, Janaral dina idan ka barsu da fina-finan gidan TV da Album ma ya ishesu.

Adam A. Zango ya jinjinawa General BMB akan shawarar daya yanke ta daina biyewa masu zaginshi

 Taurarin fina-finan Hausa uku, Ali Nuhu da Sani Musa Danja da Hafsat Idris na daga cikin jarumai ashirin da biyar mafi shahara a fina-finan Najeriya, kamar yanda masu shirya bayar da wata kyauta ta karrama jaruman fina-finan Najeriya suka bayyana.
Jaruman uku dai na daga cikin jaruman fina-finan Najeriya ashirin da biyar da za'a tantance dan samun guda daya mafi shahara a cikinsu, kuma wanda yafi yawan kuri'a daga cikinsu shine zai lashe wannan kyauta.
Muna tayasu murna da fatan Allah ya baiwa me rabo sa'a.

Ali Nuhu, Sani Musa Danja da Hafsat Idris sun shiga sahun jaruman fina-finan Najeriya 25 mafiya shahara


A lokacin da Gimbiya da IB ke tinanin sun cimma matsaya game da batun aurensu, har suna tunanin sun kusa zama ma'aurata, a gefe guda kuma Bintu ta siga matsananciyar damuwa game da hukuncin da mahaifinta ya yanke. Domin ganin yanda za ta kaya mu hadu a Dadin kowa sabon salo kashi na 52

Downlord mp4 here

Dadin Kowa Sabon Salo Episode 52 AREWA24

 Wani kamfanin shirya tafiye-tafiye zuwa kasashen waje zai dauki nauyin taurarin fina-finan Hausa, Rahama Sadau da Nafisa Abdullahi zuwa yawon shakatawa kasar Faransa, kamfanin dai na yin hakane dan tallata kanshi sannan kuma ya saukaka farashin tafiyar ga duk wanda ke da aniyar ayi wannan tafiya tare dashi.
Muna tayasu murna da fatan Allah ya kara daukaka:

Wani kamfani zai kai Rahama Sadau da Nafisa Abdullahi yawon shakatawa kasar Faransa

 Hamshakin attajirin dan kasuwa, Muhammad Indimi kenan lokacin da yake gabatar da jawabi a shahararriyar jami'ar kasar Amurka ta Harvard, duk da cewa Muhammad Indimi be yi makarantar Boko ba amma ya kafa kamfanoni da kasuwanci da suka shahara a gida da kasashen waje.
Muhammad Indimi ya taba bayyana cewa a mu'amalar da yakeyi da mutanene ya koyi yaren turanci amma ba a ajiba. Muhammad Indimi shine ke da kamfanin hakarmai na Oriental Energy Resource, kuma ya bayyana cewa duk da beyi karatuba amma yana da masu digirin digir-gir dake aiki a karkashinshi.
Muna mishi fatan alheri da fatan Allah ya kara daukaka.


Muhammad Indimi ya gabatar da jawabi a shahararriyar jami'ar kasar Amurka ta Harvard: Duk da beyi karatun Boko ba

Tauraruwar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi kenan a wannan hoton nata daya kayatar.

Jaruma Nafeesat Abdullahi Yar Kwalisa

Wani ango da amaryarshi kenan da suka sha ado da kudaden Nera dana dalar Amurka a gurin shagalin bikinsu, abin ya dauki hankulan mutane inda wasu suka rika kiran hakan da fariya wasu kuwa suce kauyanci.
Wasu kuwa cewa sukayi suna da shine shiyasa.
Muna fatan Allah ya basu zaman lafiya ya kuma sanya Alheri a auren.

TIRKASHI: KUKALLI HOTUNAN WANI ANGO DA AMARYARSHI DA SUKA SHA ADO DA KUDI

Buhari ya yi tsokaci kan maganar da ya yi kan matasa
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya yi tsokacin kan maganar da ya yi akan matasa wadda ta janyo ce-ce-ku-ce kwanakin baya. Da yake magana da Sashen Hausa na VOA, shugaban ya ce ba a bayyana maganar tasa yadda take ba.
Shugaban ya kuma kara haske kan maganar da ta janyo masa suka a shafukan sada zumunta a Najeriya.
Ya ce: "Toh ka san Najeriya an ce mun kai miliyan 180 ko kuma miliyan maitan.
"Kuma 60 bisa 100 na su duk matasa ne, wato shekara 30 abin da ya yi kasa, mu kamar a Arewa ba su yiu makaranta ba, koko suna yi sun fita.
"Toh, baya ga dai Allah Ya sa damunan bara da ta bana ta yi albarka, yawancin su ba su da aikin yi. Suna zaune.
"Irinsu ko sun je kamar misali kudu, abin da za su samu bai ma isa su biya kudin gidan haya ba, balle abin da za su ci su sha su yi sutura ko kuma su koma gida."
Ya ce miliyoyin matasa ne suka samu aikin yi ta hanyar noma, amma 'yan jarida ba su bayyana wannan ba.
Shugaba Buhari ya kara da cewa : "Su kuma dama 'yan jarida na Najeriya balle na rubutawa a.. kusan abin da suka ga dama suke yi.
"Yanzu kaman nasara da aka ci a noma da bara da bana, miliyoyin mutane sun je gona, sun yi aiki kuma abin ya yi albarka. Amma ka ga ba'a maganar. Miliyoyi! sai kullum a tashi ana zage-zage."
bbchausa.

Wata sabuwa: Buhari ya yi tsokaci kan maganar da ya yi kan matasa

Sabuwar Wakar Nura M Inuwa Baba Buhari 4+4 Atiku Bagudu 4+4 2019
Assalamu Alaikum Masoyan Wannan Shafi Namu Na Arewatech24.com.ng Munayi Muku Fatan Alkairi Da Sake Saduwa Damu A Dai Dai Wannan Lokaci.
A Yau Ma Muna Dauke Da Wata Sabuwar Waka Ta Shahararen Mawakin Nan Naku Mai Kaunar Ku ( Nura M Inuwa ) Wannan Waka Yayi Tane Ga Gwamnan Jahar Kebbi ( Atiku Bagudu ) Da ( Baba Buhari ).

Download and enjoyed

Downlord mp3 here

Source 4rm arewatop.com

Sabuwar Wakar Nura M Inuwa Baba Buhari 4+4 Atiku Bagudu 4+4 2019

PRE WEDDING PICTURES: BAKANO YA SAKI AMARYARSA KWANA DAYA DA TAREWA.
Wani Sabon Ango Mai Suna Jamilu A Karamar Hukumar Dawakin Tofa Dake Jihar Kano ya Saki Sabuwar Amaryarsa Mai Suna Badariyya Akan Laifin Daukar Hoton Kafin Aure (Pre wedding Pictures). Jamilu Wanda Ya Ki Amincewa Da Manema Labarai Su Dauki Muryarsa, Ya Bayyana Cewa Tun Farko Sai Da Ya Hana Ta Yin Hoton Amma Ta Ki.
A Bangaren Amarya Badariyya, Ta Bayyana Cewa, "Ya Hana Ni Yin Hoto Tun Kafin A Daura Auren, Ni Kuma Sai Muka Yi Da Kanin Mahaifiya Ta, Shi Kuma Ya Sa Hoton A Facebook. Shine Da Ya Gani Sai Ya Sake Ni Saki Daya."
Me Za Ki Ce Akan Wannan Abu Da Ya Faru Gare Ki?
"Ina Ba Wa Mata Shawara Su Daina Yin Abu Idan An Hana Su, Ni Yanzu Ga Abinda Ya Faru Gare Ni".
MAJIYA: Shirin Baba Suda Na Gidan Rediyon Dala FM, Kano.
Sarauniya

BAKANO YA SAKI AMARYARSA KWANA DAYA DA TAREWA SABODA HOTUNAN KAMIN BIKI

Amurka Ba Za Ta Lamunci Zubar Da Jinin Kiristocin Nijeriya Bai>>Donald Trump
Shugaba Muhammad Buhari ya yiwa gwamnatin Amurka alkawarin kawo karshen korafe korafen da ake yi game da yadda jami'an tsaro ke cin zarafin jama'a a yayin gudanar da ayyukansu.
Shugaban ya yi wannan alkawarin ne a lokacin da ya sadu da Shugaban Amurka, Donald Trump inda ya jaddada cewa gwamnatinsa ta dukufa wajen kare 'yancin al'ummarta.
A nasa bangaren Shugaban Amurka Donald Trump ya jaddadawa Shugaba Buhari cewa Amurka ba za ta amince da yadda ake kashe mabiya addinin Kirista a Nijeriya ba sai dai Shugaban ya jinjinawa Shugaba Buhari kan kokarin d yake yi wajen yaki da cin hanci d rashawa.
rariya.

Amurka Ba Za Ta Lamunci Zubar Da Jinin Kiristocin Nijeriya Bai>>Donald Trump