Real Madrid ta sha da kyar a hannun Juventus a wasan da suka buga daren jiya, zagaye na biyu na gasar cin kofin zakarun turai, wasan na kusa da na kusa dana karshe, Juventus sun rama irin cin da Madrid ta musu a gida watau 3-0, saidai ana daf da wasan zai kare rafli ya bayar da bugun da ga kai sai me tsaron gida ga Real Madrid din, kwallon da Ronaldo yaci.
Wannan bugun daga kai sai me tsaron gida bewa 'yan wasan Juventus dadi ba inda suka taso haikan kanshi, me tsaron gidansu kuma kyaftin, Buffon yana musu jagora, irin tsagerancin da Buffon din yawa raflin yasa ya bashi jan kati wanda ya fiddashi daga wasan. Wasa dai ya kare madrid na da nasara da ci 4-3.
Bayan kammala wasan Buffon ya shaidawa manema labarai cewa abinda Raflin, Micheal Oliver yayi na bayar da bugun daga kai sai me tsaron gida a yayin da ake daf da kammala wasa, ba halin mutane bane, dabbancine, amma ya kara da cewa yana alfahari da kungiyarshi kuma sunyi abinda ba'a tsammani dan haka rayuwa zata cigaba.
Shi kuwa Ronaldo ya shaidawa manema labarai cewa bega dalilin tada hankalin da 'yan wasan Juventus suka yi ba akan bayar da bugun daga kai sai me tsaron gida da Raflin yayiba, yace abinda raflin yayi daidaine, kuma da ace basu taba Lucas ba da zaici kwallon.
Yace suna farin cikin wucewa zuwa wasan daf dana karshe inda ya kara da cewa wasan na jiya da suka buga ya koya musu darasi.
Bayan kwallon da ya ci Juventus jiya, Ronaldo ya doke abokin hamayyarshi na Barcelona, watau Messi da yawan kwallayen da wani dan wasa yaci kungiyar wasa daya a gasar cin kofin zakarun turai, Messi yaci Arsenal kwallaye tara, kwallon da Ronaldo yaci jiya ta zama ta goma kenan, jumulla da yaci Juventus a gasar cin kofin zakarun turai hakan yasa ya wuce Messin.
Haka kuma Ronaldon ya sake kafa tarihi wanda dama tarihin baya shine yake rike dashi a matsayin wanda yafi cin kwallaye masu yawa a kakar wasan cin kofin zakarun turai.
A gasar da aka buga ta shekarar 2014: Ronaldo ne yafi cin yawan kwallaye inda yake da kwallaye 17.
Haka a gasar da aka buga ta 2016: Ronaldonne dai keda mafi yawan kwallaye inda yaci kwallaye 16.
Sai kuma wannan itama ta shekarar 2018: Ronaldonne dai yafi yawan cin kwallaye inda kwallon da ya ci jiya ta zamo ga 15.
Shine na daya, na biyu kuma na uku a wannan tarihi.
Madrid dai sun bi sahun Liverpool da Roma da Munich a matsayin wanda zaau buga wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin zakarun turai.

Ronaldo ya wuce messi a yawan cin abokan hamayya kwallaye: Ya kuma kafa tarihin wanda yafi yawan kwallaye sau 3 a jere: Buffon yace dabbancine yasa Rafli ya bayar da bugun daga kai sai me tsaron gida: Amma Ronaldo yace hakan daidaine

No comments