A wata hira da tayi da jaridar Daily Nigerian, tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Zeezee ta amsa tambayoyin da wakilin jaridar ya mata akan rayuwarta, ciki hadda soyayyar da tayi da mawaki Timaya ta kuma bayyana cewa ta siyawa dukkan masu aiki a karkashinta gidaje da motoci.
Ummi ta bayyana cewa tuni ta daina harkar fim saboda duka-duka nawa za'a biyata a aikin fim?.
Da take amsa tambaya akan gashin kanta da take yawan nunawa, kamar yanda wakilin jaridar ya tambayeta, ta bayyana cewa, ba gaskiya bane, duk da yake cewa ita Kanuri ce kuma suna da gashi kuma tana alfahari da hakan shiyasa take nunashi ga Duniya amma ba koda yaushe take yin hakan ba.
Ummi ta kara da cewa ita mutumce me riko da addini kuma takan karanta Qur'ani da Hadisi kuma tana kokarin bin dokokin addini daidai gwargwado. Ta kara da cewa shiyasa da zata mutu a dawo da ita zata so a dawo da ita a matsayin Ummi Ibrahim, musulma, 'yar Najeriya.
Da take amsa tambaya akan cewa mutane na ganin kudin da ake cewa tana dashi na karyane, Ummi ta bayyana cewa, Wallahi tana da kudi ta yanda koda za'a mata kyautar miliyoyin kudi bawai wani farin ciki zata yi sosai ba kamar yanda sauran mutane suke tunani, Ummi ta kara da cewa ta saiwa dukkan masu aiki a karkashinta gidaje da motocin hawa.
Da take amsa tambayar ko tana da wani abu data taba yi a rayuwarta wanda yanzu take danasanin yinshi?, Ummi ta bayyana cewa a kwanakin baya lokacin da tayi soyayya da mawakin Najeriya Timaya wasu sun rika cewa wai ta bar musulunci saboda Timayan, to wanna abu ba karamin bata mata rai yake ba duk lokacin da ta tunashi. Tace bata ga abinda zai sanya ta bar addinin musulunci ba.

Ni me arzikice sosai: Na saiwa dukkan masu aiki karkashina motocin hawa da gidaje: Nayi nadamar yin soyayya da Timaya>>Ummi Zeezee

No comments