Jarumar fina-finan Hausa, Maiminatu Watayarinya kenan a wannan hoton inda take a gurin motsa jiki, tayi mika aka dauke ta hoto, da alama Maimuna tana son motsa jiki sosai, dan ko a makon da ya gabata munga wani hotonta tare da Sadiq Sani Sadiq suna motsa jiki.

Kukalli maimuna wata yarinya tana motsa jiki

 A dazu ne mukaji labarin cewa, tauraron fina-finan Hausa, Bello Muhammad Bello, General BMB yayi zargin wani da yin Luwadi duk da be kira suna ba amma yayi habaici, inda yake cewa ba za'a kara yi a Jos ba saidai a tafi can, a wancan lokacin Bello yace yana so idan wadanda yawa maganar sunji Haushi su kaishi kotu shi kuma a lokacinne zai bayyanawa Duniya hujjojinshi, to amma yanzu yace an kusa kaishi bango, allura zata tono Garma ba ma sai anje kotu ba yana da hujjoji har guda uku kwarara.
Bello ya kara da cewa baya muna furci kuma daga cikin hujjojin da zai bayyana na bidiyo hadda wanda abin ya faru dashi kuma ya zabi yaji kunyar Duniya maimakon ta lahira, ya fito ya bayyana abinda ya faru.
Bello dai yace a jirashi nan da dan wani lokaci, a koda yaushe zai iya sakin hotunan bidiyon.
Ga abinda yace kamar haka:
"
ALLAH KA CETO BAYINKA DAGA HANNUN WADANDA SUKA BATA TUN KAFIN SUYI NISA.
Idan ni kadai zan rage mai fadin gaskiya, wallahi, zagi daga nesa, jifa, yarfe, tsafi, dauri ba za su iya dakatar dani ba.
Hirarmu da Actor na film din sakata, Bashir
Idris Baba Otu da nayi niyyar daurawa, aka yimin nasiha, nace na bari, daga baya kuma karnuka suka cigaba da haushi. Yanzu anzo gurin!
Duk wanda ke Jos ko yasan Jarumin Sakata yasan komai sai dai kin ALLAH ya hana shi fadin gaskiya.
ALLAH KARA MANA KARFIN GWIWAN FADIN GASKIYA KODA A BAKIN ARMOUR TANK MUKE.
DA ALLAH NA DOGARA!!!"
"Wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! Akwai hujjoji uku wasu daga bakin wadanda suka zabi
su fadi gaskiya suji kunyar duniya da suyi
shiru suji kunyar lahira."


'Da na jira sai an kaini kotu amma yanzu zan bayyana hoton bidiyon hujjata akan Maganar 'yan Luwadi da nayi: Bana magana babu hujja >>General BMB

RAHAMA SADAU TAREDA ZAINAB SADAU
 Tauraruwar fina-finan Hausa da turanci, Rahama Sadau kenan a wadannan hotunan nata da suka kayatar inda take tare da kanwarta, Zainab Sadau, sun Dauki hotonne a can kasar Cyprus jami'ar Eastern Mediterranean inda take karatu.
Sun sha kyau muna musu fatan Alheri




KUKALLI KYAWAWAN HUTUNAN RAHAMA SADAU TAREDA KANWANTA ZAINAB SADAU DASUKA KAYATAR

Wasu hotunan jarumin fina-finan Hausa, Umar Gombe tare da wata abokiyar aikinshi sun bayyana suna rike da juna, saidai abinda be bayyana ba ko zasu yi aurene? Watau wadannan hotunan kamin bikine kokuwa tallace kawai?.
Alamun hotunan dai sun nuna kamar akwai soyayya a tsakaninsu amma su basu bayyana hakan ba. Koma dai menene lokaci zai bayyana.





Umar Gombe zai yi aurene?: Kalli wasu zafafan hotunanshi tare da abokiyar aikinshi

Kannywood actor
Tauraron fina-finan Hausa, Ali Nuhu, Sarki kenan a wannan hoton nashi daya haskaka, muna mishi fatan Alheri.

Ali Nuhu Dan Kwalisa

New kannywood king
Wannan hoton dake nuna alamun cewa an nada tauraron fina-finan Hausa, Adam A. Zango sabon sarkin masana'antar ta Kannywood ya bayyana wanda wasu dake tare da Adamun, Mansur Make-up da Maryam Gidado suka wallafa a shafukansu na sada zumunta da muhawara.
Hoton dai ya fara jawo cece-kuce yayinda masoyan Ali Nuhun suka fara mayar da raddin cewa Ali Nuhu ne kadai sarkin da suka sani domin ba'a sarki biyu a gari daya, a kwanakin bayane dai aka so a samu rashin jituwa tsakanin Ali Nuhu da Adam A. Zango wanda kamin abin yayi kamari akamai tubka aka sasantasu, amma tun bayan wancan lokaci da alama har yanzu abubuwa basu koma daidai ba kamar da.
Bello Muhammad Bello wanda yana bangaren Adam A. Zangone dama yace za'ayi sabon zaben sarkin masana'antar a satin daya gabata inda har shima ya nuna sha'awar tsayawa takara.
Kwana biyu da suka gabata dai Adam A. Zango ya goge duk wani hoto dake dandalinshi na sasa zumuntar Instagram.

Tirkashi; Shin an nada Adam A. Zango sabon sarkin Kannywood ne?

Tauraron mawakin Hausa, Nura M. Inuwa ya caccaki taurarin fina-finan Hausa, Ali Nuhu da Adam A. Zango akan fadan da sukeyi inda yace basu kyautawa, fadan suna yinshine kawai dan son ransu kuma yana Saka yaransu dake neman na abinci a masana'antar cikin halin kaka nikayi amma duk basu damu ba saboda rashin tausayi irin nasu.
A wani zungureren sako da ya fitar ta dandalinshi na sada zumunta Nura ya kara da cewa fadan na Ali da Adam yana haddasa gaba tsakanin kananan jarumai, wannan yace bazaiyi aiki da wancan ba wancan yace bazai yi aiki da wannan ba, ya kara da cewa me yasa idan sun tashi fadan basu yi tsakaninsu sai su rika saka yaransu a ciki wanda a karshe sune ake bari da wahala, sannan kuma idan suka tashi shiryawa basa kiran yaran nasu a shirya baki daya sai suje suyi isu-isu.
Ya kara da cewa wannan rashin tausayine, kuma maganar waye sarki ko yarima a tsakaninsu babu wanda aka nadawa wata sarauta, kowa shi ya nada kanshi idan kuwa akwai wanda aka nada ya fito ya fada, Nura yace idan sunga dama su shirya su gyara dan cigaban masana'antar tasu idan kuma basu ga dama ba su barta a haka sune zasu ci baya da sauran kananan jarumai da zasu saka a wahala.
Ga abinda Nuran ya bayyana kamar haka:
"Shawara zuwa ga Adam A Zango da kuma
Ali nuhu naga alama kuna wasa da nauyin da ALLAH ya dora muku na jama ar dake karkashinku sannan kuna kokarin raunana imaninku domin kuwa alamomi suna nuni da baku dogara da ALLAH ba duba da tsoran da kuke nunawa junanku sannan duk lokacin da za kuyi rigimar me yasa bakwa barinta a junanku sai kun nemo ma biyanku kun jefasu a bala i sannan in zaku shirya bakwa nemansu hakan yana nunu da sankai da rashin adalci da rashin imani, kawai ku mafitarku kuke dubawa bakwa duba ta wasu? Wanda suke shiga rigimarku su sai da rai suna rasa abinci a cikin masana antar kannywood dalilin rigimar ku wanda da baku sasu a ciki ba za suyi mu amala da kowa kuma su nemi halak dinsu amma in kuna rigima wannan ba zaiyi aiki da wannan ba wannan bazai gaisa da wannan dan kawai bakwa shiri kuna haifar da gaba da tashin hankali
da rashin zaman lafiya shine soyayyar da kukewa kannywood din? Ko shine taimakon nakasan da kuke ikirarin kunayi?ku cire girman kai ku cire rawunan da kuka
dorawa kawunan ku na san girma wane ne sarki wane ne yarima dukanin ku babu wanda aka nadawa wata sarauta duka ku kuka sawa kanku in kuma da wanda aka nadawa wani rawani ya fito ya fadawa duniya wuri da kuma lokacin da akayi nadin babu Sarki sai ALLAH haka kuma babu abin dogaro sai shi daga ALLAH sai ANNABI sune masu girma kowa a kasa yake ba wanda yafi wani sai wanda yafi tsoran ALLAH amma kun kasa gane hakan
in kunga dama ku gyara a zauna lfy idan kuma baza ku gyara ba bakin ciki zaisa kui tayin baya kun cutar da kanku kuma kun cutar da wasu karshen mugunta kenan ra ayi na ba irin na kowa bane kuma banyi dan yabo ko kuma neman wani abu a gun daya daga cikin kuba dama bantayi ba kuma InshaAllah bazanyi ba dan ALLAH nayi kuma inaso na kasa su daina cutuwa bana raina yaro kuma bana raina babba ina son kowa da karuwa ne ba iya kaina ba duk wanda yaji haushi bazan bashi hakuri ba gaskiya ce sai na fada komai dacin daza tayiwa wasu a karshe ina kira ga duk wanda yasan yana tsoran rasa abinci gun wani kada yayi reposting ni dai babu mai bani sai ALLAH Alhamdulillah"

'Ali Nuhu da Adam A. Zango baku tsoron Allah, baku da Imani baku da tausayi'>>Nura M. Inuwa

Tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Booth kenan a wannan hoton nata da ya kayatar, tasha kyau, muna mata fatan Alheri.

Maryam Booth Yar Kwalisa

SHAWARWARI
1- TSARKAKE NIYYA KA FUSKANCI ALLAH KAWAI DA IKLASI A CIKIN KOMAI.
2- KA KIYAYI ZUGA KANKA DA GANIN KAFI KOWA
3- KA SABAWA KANKA DA KARBAR GASKIYA KO DAGA INA TA FITO.
4- KA SANI SABANI BA ZAI KAREBA HAR ABADA KA TSAYA AKAN ABINDA KA TABBATAR DA GASKIYAR SA.
5- KA SANI BA KOMAI KA SANI BA, DON HAKA KA ZAMA MAI NEMAN SANI A KODA YAUSHE.
6- ABUBUWA SUNA CANGAWA DAGA MUTUM ZUWA GURI LOKACI DA YANA YI MAI HANKALI SHINE ZAIYI KOMAI A LOKACIN DA YA DACE.
7- FAHIMTAR WANI KOMAI KYANTA BA NASSI BACE, ANA SAMUN KUSKURE A FAHIMTA BA.
8- KA KIYAYI YAWAN JAYAYYA, DA MUSU, KOMAI GASKIYAR KA BA ZAKA GAMSAR DA KOWA BA.
9- DA ILMI DA ADALCI AKE AUNA, MAGANGANU NA KIYAYYA DA SOYAYYA, DOMIN SO DA KI SUNA RUFE IDO A KASA ADALCI.
10- KA RIKE DALILI MAI INGANCI DUK ABINDA ZA KAYI, BA YAWAN MASU YI BA KO YAWAN MABIYA.
WANI YANAYI MAKA KALLON MUTUMIN KIRKI, WANI YANA KALLON KA BANZA, AMMA YAYA KAKE TSAKANIN KA DA ALLAH.
ALLAH KA BAMU KARSHE MAI KYAU.

SHAWARWARI>>Daga Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

 Taurarin fina-finan Hausa, Hadiza Gabon da Nura Hussain kenan a wadannan hotunan nasu da suka kayatar da suka dauka a ziyarar da suke yi yanzu haka acan kasar Morocco, sun dauki hotunan ne a cikin wani gari na musamman da aka gina dan fina-finai a kasar ta Morocco, misalin irin wanda aka taba cewa za'a gina a jihar Kano.
Hotunan sunyi kyau sosai, muna musu fatan Alheri.




Kalli kayatattun hotuna da Hadiza Gabon, Nura Hussain da Isma'il Na Abba Afakallhu suka dauka a kasar Morocco

Tauraron fina-finan Hausa da turanci, Sani Musa Danja,, Zaki kenan a wannan hoton naashi tare da wasu masu wasan gargajiya inda ya rike hauya yana wasa da ita.

Kalli Sani Musa Danja Yana Wasa Da Hauya

Wani sabon labari da ya bulla a baya bayan nan ya bada tabbacin cewa dan wasa gaba na PSG mafi tsada a duniya, da ke jiyyar rauni Neymar, ya fara tuntubar jami’an tsohuwar kungiyarsa ta Barcelona da nufin yi mata kome.
Wata jaridar labarin wasanni ta Spain, ' Mundo Deportivo', ta rawaito cewa tuni Neymar ya bayyana nadamar sauyin shekar da ya yi daga tsohuwar kungiyarsa ta Barcelona zuwa PSG, kwanaki kadan bayan fitar da ita daga gasar zakarun turai da kungiyar Real Madrid ta yi da kwallaye 5-2 a jimillar wasanni 2 da suka buga.
Wannan sabon al’amari ya bijiro ne, watanni 7 kacal bayan sauyin shekar da Neymar ya yi daga PSG akan euro miliyan 222.
Sai dai fa ba wai Barcelona Neymar ya ke kallo kadai a matsayin hanyar samun damar raba gari da PSG ba, Real Madrid ma na daga ciki, kasancewar tuni shugabancin Madrid din ya ce a shirye yake ya biya euro miliyan 400 domin sayen dan wasan daga PSG.
Wasu masu sharhi na da ra’ayin Neymar yana neman hujjar komawa ne zuwa Real Madrid kai tsaye cikin sauki, kasancewar akwai yiwuwar Barcelona ta ki amincewa da tayin komensa.

rfihausa

Na yi nadamar barin Barcelona>>Neymar

Jin labarin za'a mata kishiya yasa wata mata ta kona gidan mijinta kurmus a jihar Kebbi kamar yanda jaridar The Sun ta ruwaito, Yunus ya rasa tsohuwar matarshi wanda haka yasa yayi sabon aure a watan fabrairun wannan shekarar, indaya auri A'isha, amma shima dai babu alamar zaman lafiya tsakaninshi da matar wannan yasa ya fara shirin yin sabon aure.
Jin labarin haka ya hasala A'isha, cewa wai wata biyu kawai da yin aure tsakaninsu zai yi mata kishiya, ai kuwa sai ta hau dokin zuciya ta cinnawa gidan mijin nata wuta yaci ya cinye.
Rahotanni dai sun nuna cewa an fitar da wasu kaya daga gidan bayan da makwauta suka kawo dauki amma duk sauran wasu kayan mijin sun kone kurmus.
Jaridar ta The Sun ta tuntubi hukumar yansanda akan lamarin amma sun shaida mata cewa babu wani koke da aka kawo musu akan lamarin

Jin labarin za'a mata kishiya, bayan wata biyu da yin aurensu: yasa wata mata ta kona gidan mijinta kurmus

Tauraron fina-finan Hausa Adam A. Zango kenan yake zukar taba a cikin wani shirin fim da yakeyi.

Kalli Adam A Zango Yana Zukar Taba Sigari

Kungiyar Barcelona na daridarin cewa tauraron dan kwallonsu Lionel Messi zai iya komawa wata kungiyar kwallon kafa idan sukayi sake, me kula da harkar kudade da tsare-tsare na kungiyar Schroda ne ya bayyanawa kafar Skysport haka a wata zantawa da yayi dasu.
Ya bayyana cewa duk da yake Messin a shekarar data gabata ya sanya hannu akan kwantirakin tsayawa a kungiyar har zuwa shekarar 2021, kuma a wancan lokacin yana da damar komawa wata kungiyar amma ya jaddada kaunarshi ga Barcelona, sannan kuma suma kungiyar dan su tabbata cewa babu wata kungiya da zata iya kawo harin siyanshi suka saka tsabar kudi har Euro miliyan dari bakwai akan cewa duk kungiyar da zata sayi messin zata biya, amma yanzu suna ganin cewa yanda abubuwa ke canjawa za'a iya samun wata kungiya ta biya wadannan damman kudin dan sayen Messin.
Schroda yace, abinda ya faru kenan lokacin Neymar, suka saka mai kudi har Euro Miliyan dari biyu da ashirin da biyu dan su tabbata cewa ya zauna a kungiyar tasu har tsawon lokacin da zaiyi ritaya daga kwallo amma sai gashi an samu PSG ta biya wadannan kudi.
Schroda yace gaskiya zasu sake tunanin kara yawan kudin da suka sawa Messi domin ga dukkan alamu idan suka barsu a haka wata kungiya zata iya zuwa ta sayeshi a haka, a barsu da buda baki.

Barcelona na tsoron cewa Messi zai iya canja kungiyar kwallon kafa akan kudi mafi tsada da a Duniya

Maryam Sanda
Bayan wata kotu a Abuja ta bayar da belin Maryam sanda wacce ta kashe mijinta Bilyamin Bello, bayan kwana daya da dawowarta daga gidan yari ta shirya wa 'yarta zagayowar haihuwarta.
Anya kuwa Maryam ta yi nadamar abin da ta aikata?

Kwanaki biyu bayan sakin ta daga gidan yari, Maryam Sanda ta shiryawa diyarta bikin zagayowar ranar haihuwarta

Dadin kowa sabon salo episode 44 arewa24
Tashin hankali ya kara Kamari a Gidan Malam Musa, inda hakurin Baraka ya kare, ta dauki mataki mafi zafi yayinda a bangaran Nazir da alawiyya suke ganin nesa tazo kusa, amman hakan bai tabbata ba, don ganin yanda zata kaya ku kalli shirin dadin kowa kashi na 44

DADIN KOWA SABON SALO EPISODE 44 DOWNLORD

DADIN KOWA SABON SALO EPISODE 44 >>Arewa24

Video da anka dade ana tala tamuku ita wato video best of ranar aurena wanda nura m inuwa ya rera wakokinsa akan bukin da yayi wato na aurensa inda ankayi fim mai suna haka.
Kuma ankayi video best of ranar aurena wanda Fitaccen jarumin kannywood ya hau wakokin wato ali nuhu video yayi kyau sosai karka bari a baka labari.

Downlord video mp4

SAUKAR DA VIDEON NURA M INUWA RANAR AURENA FT ALI NUHU

Tauraruwar fina-finan Hausa da turanci, Rahama Sadau kenan a wannan hoton nata da ta sha kwalliyar zamani.

Jaruma Rahama Sadau Yar Kwalisa