Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Kannywood Hadiza Gabon ta soma fitowa a fina-finan Nollywood da ake yi a kudancin Najeriya.
Jarumar ta shaida wa kafar bbc hausa cewa ta fara gwada sa’arta a fina-finan Nollywood ne domin ta nuna basirar da take da ita ta yin fina-finai a ɓangarori daban-daban.
A cewarta, “Ba wannan ne karon farko da na soma yin fim da turanci ba. Lokacin da na je Amurka, na fito a gajerun fina-finan turanci, amma wannan ne karon farko da na fito a fina-finan Nollywood.
Fitaccen Jarumi kuma Furodusa a Fina-finan Nollywood Mike Ezuruonye da Jaruma Hadiza Gabon Ayayin Aikin fim ɗin Lagos Real Fake Life.
“Fitaccen jarumin Nollywood Mike Ezuruonye ne ya gayyace ni na fito a wani fim dinsa mai suna ‘Lagos real fake life’.
“Shi ne furodusan fim din kuma na fito ne a matsayin ‘yar arewa. Zan rika yin shiga irin ta bahaushiya don haka kayan da nake sa wa a fina-finan Kannywood irinsu nake sa wa a wannan fim”.
Hadiza Gabon ta ƙara da cewa “Tun da ya gaya min cewa zai so na fito a fim ɗinsa, na shaida masa cewa ba kowacce rawa zan taka ba. Ba zan fito a matsayin da zai saɓa da addini da al’adata ba”.
Jarumar ta ce babu wani “bambanci tsakanin yadda ake yin fina-finan Kannywood da na Nollywood idan ban da bamabancin harshe. Don haka na ji daɗin soma fitowa a fina-finan Nollywood”.

Babu Bambamci Tsakanin Fina Finan Kannywood Da Nollywood – Inji Hadiza Gabon

Kamar Yadda Kowa Yasani A Wannan Zamani Damuke Ciki Babu Mawakan Hausa Da Tauraruwarsu Take Haskawa Kamara Wadannan Mawaka Guda Biyu Wato Umar M Sharif Da Nura M Inuwa.
Wannan Daliline Yasa Mukeso Muyi Muhawara Domin Banbance Aya Da Tsakuwa A Tsakanin su Ta Hanyar Jin Ra’ayoyin Masoyansu.
Muhawarar Anan Itace Acikin Wadannan Faishan Mawaka Guda Biyu Wanene Salonsa, Kida, Lafazi, Murya Yafi Burgeka Acikinsu???
Ajiye Ra’ayinku Domin Jin Wanye Zaici Wannan Muhawara

Salo, Kida, Lafazi, Murya: Wani Abu Ne Yafi Bambamta Wakar Nura M Inuwa Data Umar M Sharif?

Sabuwar tauraruwar masana’antar Kannywood tace zata koma makaranta kuma idan Allah yayi ta samu miji zata yi aure.
Sabuwar tauraruwar fina-finan hausan na Kannywood Maryam Yahaya ta bayanar cewa yin fim ba zai hanata yin karatu domin yin karatu yana cikin abubuwan dake gaban ta a rayuwa.
A wata hira ta musamman da tayi da BBC hausa, Maryam wanda ta kammala karatu ba da dadewa tace tana kokarin cigaba da yin karatu.
Jarumar shirin “Mansoor” tace idan Allah ya nufe ta da samun miji yanzu zata yi aure kuma zata cigaba da yin karatun ta.
Sabuwar tauraruwa wanda ta fara haskawa cikin “Mansoor” bayyana cewa idan tayi aure bazata cigaba da yin fim.
Maryam Yahaya ta shigo masana’antar kannywood da kafar dama domin bayan fitowar ta a cikin “Mansoor” ta samu damar fitowa a wasu shiri da dama.
Ko zamu iya cewa wannan matashiyar zata sauya jarumtakar manyan yan wasan masana’antar kamar su Rahama sadau, Nafisa Abdullahi, Halima Atete, Hadiza Gabon da dai sauransu?

Zan Koma Makaranta Kuma Idan Nasamu Miji Zanyi Aure – inji jaruma Maryam Yahaya

Mesut Ozil na shirin kin yadda ya tsawaita yarjejeniyar ci gaba da zama a Arsenal, bayan da dan kwallon ke son komawa Manchester United in ji jaridar Daily Mirror.
Sunday Express ta wallafa cewar Liverpool ta bukaci Barcelona da ta daina matsawa Philippe Coutinho a lokacin da ta yi kokarin sayen dan kwallo, inda Liverpool ta ki sayar da shi.
The Sun kuwa cewa ta yi Manchester City ta damu matuka cewar Paris St-Germain za ta bai wa Arsenal makudan kudi domin ta dauki Alexis Sanchez.
An shaidawa Manchester United ta biya fam miliyan 75 idan tana son daukar dan wasan Lazio, Sergej Milinkovic-Savic, itya ma Manchester City na son sayen dan kwallon in ji Daily Express.
Everton za ta taya dan wasan Arsenal Olivier Giroud a watan Janairun 2018, har ma ta tanadi fam miliyan 40 in ji Daily Mirror.
Daily Mail kuwa ta wallafa cewar ran Arsene Wenger ya baci matuka da ya sayar da Kieran Gibbs ga West Brom, fiye da barin Alex Oxlade-Chamberlain da ya koma Liverpool.
Tura wannan labarin

Tirkashi: ''Ozil na shirin komawa Man United''

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma Abuja bayan da ya yada zango a birnin Landan daga Amurka, inda ya halarci babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 72 a makon jiya.
Fadar shugaban kasar ce ta tabbatar wa BBC komawar shugaban gida.
Sai dai ba ta yi karin haske ba game da abin da shugaban ya yi a Landan ba.
Shugaban ya isa Landan ne ranar Alhamis daga birnin New York na Amurka.
Kafin tafiyarsa, shugaban ya gabatar da jawabi a zauren Majalisar Dinkin Duniya ranar Talata.
Da ma dai fadar shugaban ta ce zai je Birtaniya bayan ya kammala taron.
Sanarwar da kakakin shugaban kasar Femi Adesina ya aikewa manema labarai a makon jiya ta ce shugaban "Zai je birnin Landan a kan hanyarsa ta komawa gida".
Sai dai Mr Adesina bai yi karin bayani kan abin da zai sa Shugaba Buhari zuwa London ba.
A watan jiya ne dai shugaban ya koma gida Najeriya bayan ya yi doguwar jinya a Birtaniya, inda ya shafe fiye da wata uku a can.

Buhari ya koma gida

Duniya kullun kara samun cigaba akeyi ta bangaren kirkiro sabbin kwalliya musamman ta bangaren mata yanda zasu rika jan hankulan mutane da birgewa, wannan wata baiwar Allahce data fito da sabon salon gashin gira, ana iya gani yanda tayi kitso dashi kamar gashin kai a wannan hoton.

Sabon Salo: Gashin gira da kitso

Diyar marigayi tsohon shugaban kasa Hajiya Fatima Gumsu Sani Abacha kenan take taka rawar shoki a gurin shagalin bikin zagayowar ranar haihuwarta, anokai da 'yan uwa sun taru dan tayata murna muma muna kara tayata murna da fatan Allah ya karo shekaru masu albarka.

Ashe rawar shoki hadda manya?: Fatima Sani Abacha na takawa a gurin shagalin zagayowar ranar haihuwarta

Tsohuwar jarumar finafinan Hausa matar Sani Musa Danja Zaki, Mansurah Isah taja hankulan wasu mutane da suke yiwa jaruman finafinan Hausa kudin goro a duk lokacin da aka samu wata ko wani jarumi da yin ba daidaiba, Mansurah tace suma fa mutanene kuma musulmai kuma masu zagin nasu basusan irin ayyukan alherin da suke aikatawa na farantawa Allah a boyeba.
Ta kara da cewa akwai jarumai da dama da take samu akan nemawa wasu bayain Allah da suke cikin halin kaka nikayi taimako kuma haka wadannan jaruman zasu bayar da taimako su kuma bukaceta da kada ta bayyanawa Duniya.
Gadai cikakken bayanin da Mansurah tayi:
"Assalamu alaikum. Yan uwana musulmai, wallahi wallahi kuji tsoron Allah. Ku tuna akwai hisabi, Duk abinda yan film sukayi, sai kunyi suka. Kar ku shiga tsakani BAWA da UBANGIJIN sa, domin bakusan abinda yake yi a boye dan farantawa ubangiji rai ba. Mun kawo case din UMMASALAMA domin a ceto ranta, wacce take bukatan taimako cikin gaggawa, wassu suka fara zagin yan film, wai mai sukeyi, Ina duk kudin da suke tarawa? Ku kusan abinda yan film din sukeyi? Ko halin da suke ciki? Shi yasa duk Sanda wani ko wata yar film ta kirani dan taimakawa, nakan so, na rubuta ba dan komai ba, dan asan abinda sukewa jamaan gari. Akwai case din yara da aka haifa da #diabeties, a nan na rubuta cewa duk wata suna bukatan #insulin domin Karin lafiyan su, waya tuna dasu a watan nan? Babu sai Yan film. Case da muke dashi bana ummasalama kadai bane, muna da case irin na ummasalama sunfi thousands ( dubu ), ko kusan guda nawa yan film suka biya musu kudin asibiti ko magani? Ko aika musu da kayan abinci? Kuma mutanen nan ba yan film bane. @adam_a_zango @officialsanidanja @yakubu_mohd @realalinuhu musha case dasu, duk Sanda na kai musu case din wassu dan su taimaka. Sai nayi musu alkawari cewa banzan fadawa kowa ba ko na rubuta a page Dina. Nasha nuna musu cewa gara duniya tasan abinda kukayi, domin wassu mutane jakuna ne, basu tauna magana kafin su fada, yan film suna iya kokarin su na taimakawa al'ummah Wanda ba yan film ba, Amma da zarran case na yar film ta taso, sai ku fara zagi kamar su ba musulmai bane, kamar in kun taimaka haram ne, kai kayi aikin ladan ka mana, tsakanin ka da ubangijin ka in kana da hali. Ka barwa Allah komai. Nasha kawo case page Dina, wallahi Christians sun sha min dm na bada gudunmowa, har mamaki suke bani, Amma wai musulmi ne zai fara zagi da zarra kace ya taimaka, ko waya kayi musu, zasuyi alkawari bazasu cika ba. Ina mai bada hakuri ga mijina da sauran yanfilm da ake zagi a dalilina, suyi hakuri su kuma ci gaba da aikin lada. Kuma neman taimako ta kowacce iri ne, banzan daina neman wa mutane ba, in har naji labari ko an kawo min case dinsu. Allah ya shige mana gaba ameen. Allah ka bani ikon ci gaba da taba rayuwan al'umman ka domin shine farin cikina."
"Ni tambaya ta a nan, kudin yan film ne kadai ake taimako dashi? Ko kuwa su kadai Allah yace suyi taimako? Ina laifin Wanda yace, wa mai son aikin lada gashi yayi? Ba'ace dole a taimaka ba, duk mai so ko mai hali bisimillah. Kai a matsayin ka na musulmi ai ya kamata kasan cewa duk abinda bawa zaiyi, sai Allah ya yarda mishi, aure, haihuwa, shiriya, arziki, taimako, lafia, mutuwa duk sai da yardan ubangiji. Kar ku bari bakin ciki da jahilci yaci gallaba azuciyan ku. Shikenan in dan film yayi sallah sai yace Allah kayiwa yan film albarka su kadai? Ko Wanda ba dan film ba, sai yace Allah yayiwa mutane albarka Amma banda dan film? Duk daya muke a gaban ubangiji. Wallahi taimakon da yanfilm sukeyiwa a waje, ba kadan bane. Amma baku gani. Daga anyi magana sai kuce dan film. Why? Menene dan film ne? Wata hallita ce daban ko yaya? Ba uwace ta haife su ba ko ba bayin Allah bane? Ko akwai inda aka fada acikin alqurani cewa kayi taimako Amma banda dan film ? Allah ubangiji ya saka da alheri ga dukanni masu taimako, Wanda suke taimakawa a boye dana fili ameen. Allah ya shirye mu gabaki daya. Masu taimako Allah ka Kara musu budi ameen, masu niya kuma Allah kada iko ameen."
Sai muce Allah shi kyauta.

"Jama'a Ku daina yiwa 'yan fim kudin goro bakusan aikin alherin da sukeyi a boyeba">>Mansurah Isah

WACECE MACE TA GARI? //5
ITACE MAI NEMAN ILIMI
Ilimi da aiki dashi shima yana daga cikin matakin farko ga dukkan macen da take son zama ta gari. Ya zama dole ta yi aiki da hadisin Manzon Allah (SAW) cewa: "Neman ilimi wajibi ne akan dukkan musulmi da musulma". Wannan yana nuna babba da yaro, mace ko namiji, tsoho da matashi.
Duk macen da ba ta da ilimi kuma bata neman sa to hakika zaman ta na gari zayyi mata wahala. Saboda bata da fitilar da zai rinqa haska mata hanyar ta (rayuwarta).
Kuma kada ki ce wai kin yi sauka shikenan kin bar neman ilimi a'a ki cigaba da zuwa in da za a  rinqa tunatar dake Allah, In da za a koya miki hanyoyin shiga Aljannah, in da za'a rinqa koya miki zamantakewar magabata don ke ma ki yi koyi dasu. In da za a koya miki yanda zaki tarbiyyantar da 'ya'yanki.
Kin ga in a gida kike dukkan wainnan garabasar zasu rinqa wuce ki, kuma a hankali sai shaidan yayi galaba a kanki ki zama kamar ba ke ce mahaddaciyar nan ba mai bin Allah.
Sannan shi ilimi kogi ne yana dayawa, cigaba da nema shine zai sanya miki son addini da son ibada, kuma za'a rinqa miki wa'azi a hankali kina gyara halin ki.
Da sauraren wa'azin malaman Sunnah, ko a radio ko a TV kada dai ki zauna baki da wata kafa da zata rinqa koyar dake addini.
Da koyan Qur'ani da karanta shi domin samun lada da koran shaidanu a gidan auren ki.
Sannan uwa uba ilimi zai taimaka ma 'ya'yanki, domin zaki taya su tilawa a gida, zaki musu assignment. Kin ga kuwa dole mace ta gari ta nemi ilimi.
Ba na addini kadai ba har da na zamani, don ki san me duniya take ciki, saboda idan kina tunani ta bangare daya zai iya kawo naqasu ga 'ya'yanki.
Yar'uwar ku Sadeeya Lawal Abubaka

WACECE MACE TA GARI? //5