Tauraruwar fina-finan Hausa da kwanannan muka ji cewa tana kwance a gadon asibiti ba lafiya, Maryam Gidado ta nuna alamun samun sauki.
Maryam din ta saka hotuna a baya inda take kwance a gadon asibiti tana rokon addu'ar masoyanta.
Saidai kuma yanzu Maryam din ta saka wannan hoton inda tace, Alhamdulillahi, wanda haka ke nuna ta fara samun sauki.
Muna fatan Allah ya bada lafiya ya sa kuma kaffarane.

Maryam Gidado ta warware

Chelsea Ada Ezerioha popularly known as Chelsea Eze was born on 15th November. She is a talented Nigerian actress.
Chelsea Eze hails from Umuahia in Abia State, in the Eastern part of Nigeria but was born and bred in Kano State. Her parents were both Bankers.
She had her secondary school Education at Federal Government Girls College Minjibir and St.Louis Secondary School both in Kano State. She proceeded to study English and linguistics at the University of Maiduguri.
She came into limelight in her first Nollywood film Silent Scandals where she acted alongside Genevieve Nnaji and Majid Michel. This breakthrough in her acting career came about as a result of being invited by producer Vivian Ejike to audition for a supporting role in Silent Scandals, and she was chosen to appear in the film.
It is worthy to note that Prior to her role in Silent Scandals, she was a model and her only acting experience was in stage plays in church. She has featured in several other popular films like Two Brides and a Baby (2011), Hoodrush (2012) and Murder at Prime Suites (2013).
Chelsea Eze within a short time in her career has been nominated and has won several awards including the Most Promising Actress award for her role in silent scandals, Best upcoming Actress and several others.

Biography Of Chelsea Eze, Actress, Abia State Celebrity

 Hafsat Idiris wadda wasu ke kira da Barauniya ko kuma 'yar fim na daya daga cikin taurarin fina-finan Hausa dake jan zarensu a wannan zamani, wani kishin-kishin din labari da abokin aikinta ya labarta na nuna alamar cewa jarumar ta kusa yin aure.
Nuhu Abdullahi wanda shima taurarone a masana'antar fim din Hausa ya saka hotunan Hafsat tare da me shirya fim din Hausa, Shazali Kamfa a shafinshi na sada zumunta inda ya kira su Ango da Amarya da kuma masoyan Kannywood har ma yayi addu'ar cewa Allah ya kaimu ranar.
Koma dai menene gaskiyar lamari, lokaci be bar komai ba.



Hafsat Idris zata yi aurene? Kalli wanda zata aura

A lokacin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya ke karbar sakamakon jarabawarshi daga mahukuntan WAEC ya bayyana cewa tare su kayi karatu da marigayi, janar Shehu Musa 'Yaradua.
Wannan hoton Shehu Musa 'Yaradua ne tare da shugaba Buhari a lokacin da suke a makarantar sakandire.
Shehu Musa ne na biyu a zaune daga hannun dama sai Shugaba Buhari na zaune kusa dashi.

Kalli tsohon hoton Marigayi Shehu Musa 'Yaradua da Buhari a makarantar sakandire

Hoton General BMB da Rahama Sadau da ya jawo cece-kuce
 Taurarin fina--finan Hausa, Bello Muhammad Bello, General BMB kenan tare da Rahama Sadau a wannan hoton inda ya dora hannu a kafadar Rahamar, sun dauki hotonne a lokacin da Bello ya ziyarci gurin daukar shiri Mati a Zazzau.
Bello ya saka hoton a dandalinshi na sada zumunta inda yace yasan wasu zasu yi kushe akan hoton amma su sani ko wane aiki ya dangantane da irin niyyar da aka nufeshi da ita.
Ya kara da cewa fim din Mati a Zazzau na musamman ne wanda zai nishadantar da 'yan kallo sosai.
Saidai da dama wanda suka bayyana ra'ayoyinsu akan wannan hoton sun ce be dace ba.
Ga wasu daga cikin ra'ayoyin mutane akan hoton:





Hoton General BMB da Rahama Sadau da ya jawo cece-kuce

A jiyane muka ga hoton taurarin fina-finan Hausa, Bello Muhammad Bello, General BMB da Rahama Sadau inda Bellon ya dafa kafadarta, hoton ya dauki hankula ya kuma jawo cece-kuce sosai inda wase suka ta sukar yanda Bellon ya dora hannu a kan Rahamar, tun a jiyan Bello ya ta mayar da martani amma ya sake mayar da martani na musamman.
A wani bidiyo da ya fitar ta dandalinshi na sada zumunta, Bello ya kare dafawar da yawa Rahama Sadau inda yace' yana da dangantaka ta jini da kowace musulma, sannan kuma yana da dangantaka ta mutuntaka da duk wani dan Adam, dan haka Rahama Sadau 'yar uwarshi ce ta jini kuma dan na dafata mun dauki hoto, ba shafata na yi ba, kai kamin ma in dafata inada alwala a jikina kuma abinda ke karya alwala sune, maniyi, maziyi, bawali gahidi, suma maye, shafar mace, shafar alkalami, bacci, ridda, saboda haka dan Allah dan Annabi hadisai kuke kawo min kuma nima hadisi na kawo muku dan Allah dan Annabi ku yi hakuri kowa ya rike ra'ayinshi, Allah, ubangiji shi kadai yasan karatun bebe kuma Allah shi kadai yasan daidai, Allah ne mafi sani, nagode Allah ya muku albarka'

Ina da Alwala lokacin dana dafa Rahama Sadau kuma ba shafata na yi ba>>General BMB

 A jiyane Sani Musa Danja, Zaki da matarshi, Mansurah Isah suka yi murnar cikar diyarsu, Khadijatul Iman shekaru 10 da haihuwa, 'yan uwa da abokan arziki sun taru inda suka tayasu murna.
An kuma yiwa Khadija kek na musamman masu kayatarwa dan wannan shagali.
Muna taya su murna.



Kalli kek masu kayatarwa da akawa diyar Sani Danja da Mansurah Isah dan cikarta shekaru 10

Kalli wasu kayatattun hotunan Maryam Yahaya
 Jarumar fina-finan Hausa, Maryam Yahaya kenan a wadannan kayatattun hotunan nata da ta haskaka, ta sha kyau, tubarkallah, muna mata fatan Alheri.






Kalli wasu kayatattun hotunan Maryam Yahaya