Kamaye ya shiga cikin tashin hankali, bayan da masu garkuwa da mutane suka bukaci ya bayar da Naira Miliyan daya a cikin awoyi uku, idan har yana so a saki 'yarsa Zaliha sukayi garkuwa da ita. Sai dai Kamaye ya zagaye garin Dadin Kowa kaf, bai samu dubu daya. Shin ya zata kasance kenan?

Downlord now

Watch And Downlord Dadin Kowa Sabon Salo Episode 39


Tauraron fina-finan Hausa, Adam A. Zango ya musanta labarin da ake yadawa cewa, wai matar tauraron mawakin Hausace, Nura M. Inuwa ta haihu a wannan hoton, Adamun yace wani masoyinshine, saboda tsabar son da yake mishi ya sakawa danshi sunan Adamu.
Shine shi da Carki da Nuran suka je har gida suka taya mutumin murna.
Muna fatan Allah ya raya Adamu.

Matar Nura M. Inuwa bata haihuba: Wani masoyin Adam A. Zango ne ya sakawa danshi suna Adamu

Tauraron fina-finan Hausa, Adam A. Zango ya kara fitowa fili yayi cikakkaen bayani akan irin matsalolin da yake so ya kawo gyaransu a masana'antar fina-finan Hausa, Adamun yace wasu masu shirya fina-finai suna bautar da jarumai ta yanda zasu yi aiki amma aki biyansu ladan aikinsu.Adamun yace har kara irin wadannan jarumai sun kaiwa hukumar tace fina-finai ta Kano amma babu wani mataki da aka dauka akan lamarin.
Gadai abinda Adamun ya bayyana kamar haka:
"
A Yau wasu daga cikin Jarumai MAZA da MATA tsofaffi da manya da kananan da wani bangare na Maaikata a kannywood. Suka kai kara da kukan wasu manyan producers da kananan su.! Gurin Hukumar tace fina-finai. Kan abin da suke kira danne hakki da mugunta da producers din suke musu.
A cewarsu mafi yawan ayyukan da suke da producers din basa biyansu ko kuma in zaa biya ka a baka kudin da ko na mota bazai kai ba. Ko ayi kwanaki ana aiki da kai, in an gama ace za'a kiraka, shikenan an cinye. Tabbas duk abin da mutum sama da Ashirin Mata da maza suka fada, to lallai yana faruwa. Kuma hakan zalincine .
Allah bazai kyaleba.. Yaku masu wannan dabiar, ku sani an wuce lokacin bauta. Wadanda kuke bautarwa Allah sai ya saka musu. Kuma Wallhi sai kun biya su hakkin su a ranar da baku da komai sai abin da kuka jewa Allah dashi. Ina rokon wasu daga cikin Directors, Actors, Actresses, writers da producers. Mu hadu domin kawo karshen Wannan zalinci. Duk wanda aka samu a karbi hakkin wanda yaci kuma a hukuntashi. Muyi domin Allah bada nufin tozarci ko cin Zarafin juna ba. Sai Dan tsaftace Masana'anta daga hannun baragurbi. Ka fara daga set din da kake. Duk wanda kaji ba'a biya ba, ka dakatar da aikin har sai an biya hakkin mutane sannan a cigaba. Domin ni nasan ba'a film sai da kudi.
The Wallhi duk KABON wanda kaci ka shirya sauraran hukunci tun daga kabari.
Allah ka tsaremu da zalinci da cin dukiyar wadanda suka wahaltamana. Ameen."

"Ana bautar da jarumai a masana'antar fina-finan Hausa">>Adam A. Zango

Tauraruwar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi kenan a wadannan hotunan nata da suka dauki hankula, Nafisar ta dauki hotunanne akwance kai babu dankwali.


Kalli wasu hotunan jaruma nafisa abdullahi dasuka birge

Tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango ya fito ya roki masoyanshi a cikin masana'antarsu da cewa su fito su nuna irin soyayyar da suke mishi a fili, kuma duk wan yasan cewa ya taba mai alheri to shima ya fito ya fada hadda ma sharrinsa. Jaruma Sa'adiya Kabala ta fito ta bayyana cewa tana tare da Adam A. Zango.

"Idan na tashi yin aure: Adam A. Zango ne Waliyyina">>Sa'adiya Kabala

Tauraruwar fina-finan Hausa, Fati Shu'uma ta fito ta bayyana iri halaccin da Adam A. Zango ya mata kamar yanda ya bukata, Fati tace ta sanadiyyar Adamun ne aka santa domin shine ya fara sakata a fim har tayi suna.Fati ta kara da cewa abinda kuma Adamun ya mata wanda ba zata taba mantawa dashi ba shine, lokacin da mahaifiyarta ta rasu, Adamun yazo ya zauna aka rika karbar gaisuwa dashi, tace wannan abu ba karamin dadi ya mata ba, hatta 'yan gidansu sunji dadin hakan kuma ba zata taba mantawa dashiba.
A karshe tace bata ma san da wace irin kalma data godewa Adam A. Zango ba.

Adam A. Zango ne ya fara sakani a fim Duniya ta sanni:Yamin abinda bazan taba mantawa dashiba>>Fati Shu'uma

A wata hira da yayi da manema labarai, tauraron fina-finan Hausa da turanci kuma mawaki, Sani Musa Danja, Zaki, an tambayeshi me zaice dangane da irin yanda wasu mutane ke kallon harkar fim dacewa ana abubuwan da basu kamataba a ciki, Sani yace abinda yasa ake yawan ganin laifin 'yan fim, mutane sun saka musu ido da yawane.Ya kara da cewa, zakaga idan aka ce za'a buga wata muhimmiyar kwallo, matasa, maza da mata zasuyi tururuwa su shiga gurin kallon wasan kuma za'a gauraya ba'a damu ba, ba'a magana. Amma idan akazo kan maganar harkar fim, saboda mutane sun zuba ido, dama jira suke suga laifin dan fim sai ayi ta surutai, ya kara da cewa, saboda haka shi baiga damuwa ba a haduwar maza da mata ayi harkar fim ba tunda a sauran al'amura na rayuwa ma mutane maza da mata suna haduwa suyi.

"Banga aibun haduwar maza da mata wajan yin fim ba">>Sani Musa Danja

 Wannan wasu hotunan kamin bikine da saurayi dabudurwar da zai aura suka dauka, hotunan sun dauki hankulan mutane sosai, muna fatan Allah ya kaimu yasa ayi lafiya.

Kalli Hotunan kamun biki dasuka ja hankullan mutane