Fiye da shekaru 5 kenan dana ko a waya baya kirana amma masu satar mutane suna tunanin yana turomin kudi>>Inji mahifin Mikel Obi

Mahaifin tauraron dan kwallon Najeriya, Mikel Obi, Michael Obi ya bayyana cewa dan nashi fiye da shekaru biyar kenan be kirashi a waya ba amma masu garkuwa da mutane sun kamashi suna tunanin Mikel din na turo mishi makudan kudi.
Micheal yayi hira da jaridar Daily Trust ne inda ya bayyana yanda aka sace shi da kuma irin dangantakar dake tsakaninshi da dan nashi, kwanannan dai masu garkuwa da mutane suka sakeshi, karo na biyu kenan ana garkuwa dashi.
Ya bayyanawa Daily Trust cewa, suna cikin tafiya da direbanshi zuwa wani taron Iyali da zasu yi a Enugu sai kawai suka ji harbin bindiga, direbanshi yayi kokarin komawa da baya amma sai wata motar ta taho daga baya ta tare su.
Sun fitar dasu daga cikin motar inda suka nufi daji dasu sukai ta tafiya har gari ya waye.
Daga baya ya tambayesu me suke so ya basu suka ce mai miliyan dari, sun ji labarin danshi, Mikel yana aikomai miliyan Hamsin duk sati, yace nan ya gaya musu cewa shi miliyan biyu kawai gareshi a asusun ajiyarshi na banki, sukai ta dai ja in ja har takai miliyan goma.
Sun kira danshi, Toni, ya gayamai yaje banki ya amso kudi amma sai manajan bankin bayanan, sai yawa dayan danshi magana, Ebele, shi kuma sai ya kira Mikel, ta yanda aka samu kudin da aka baiwa masu garkuwa da mutanen kenan.
Da aka tambayeshi yaya dangantakar shi da dan nashi Mikel take, sai ya bayyan cewa, shekaru fiye da biyar kenan ko a waya baya kiranshi, yace, yayi iya yinshi dan ganin ya warware wannan matsala amma abu yaci tura, yace amma yana kiran mahaifiyarshi, shi kuma da ya ga haka sai ya sawa ranshi dangana yace indai zai ganshi a talabijin yana koshin lafiya to hakan ya gamsar.
Da aka tambayeshi amma wasu na cewa Mikel din ya kiraka, sai yace, Eh suna waya da mahaifiyarshi, kwanaki kadan bayan gasar cin kodin Duniya, sai ta ce min gashi mu gaisa, anan na amshi wayar muka gaisa na mai addu'a.
Ya kara da cewa lokacin da dan nashi ya zama dan kwallon Chelsea mutanen garinsu sun yi ta tayashi murna da fadin cewa ya warke, nasu ya samu. Akwai lokacin da yazo Abuja, mutanen kauyensu sukai ta murna aka buga fastoci da shiri na musamman akan tunanin cewa Mikel din zai karasa garin amma sai bai jeba, yace wannan abu yasa yaji kunya kamar ya nutse kasa, mahaifin na Mikel ya bayyana cewa, Mikel din na gayawa 'yan uwanshi cewa, wani lokacin sai ya daga waya da niyyar ya kira mahaifin nashi amma sai ya fasa.
Ya kara da cewa ko 'ya'yan na Mikel har yanzi bai taba ganinsu ba

Related Posts

No comments