Dan tsohon shugaban Libiya Muammar Gaddafi, Saiful Islam ya fasa kwai game da batun wafatin gyatuminsa.
Kamar yadda wasu kafafan labaran kasar Ivory Coat suka rawaito,a watan da ya gabata, wata mata mai suna Zayraf Aya hafaffiyar kauyen Gaddafi ta bayyana cewa,tsohon shugaban kasar Libiya wanda aka ce an kashe a shekarar 2011, mahaifi ne na 'yarta, kuma da ransa,bai mutu.
Matar mai shekaru 35 da haifuwa ta ce Gaddafi na nan da ransa amma ya rasa kafa daya sakamakon hare-haren bama-baman da aka kai masa, a lokacin aka nemi hambarar da mulkinsa.
Ta kara da cewa, a yanzu Gaddafi yana jinya amma da zaran ya samu lafiya zai koma kasarsa don ceto al'umarsa.
Da maneman labaran jaridun na Ivory Coast suka nemi ganawa da Saiful Islam sai ya ce da su,
"A hakikannin gaskiya a shekarar 2011, mahaifina ya jikkata, amma bai mutu ba,yanzu haka yana ci gaba da jinya.Ba zan taba gaya muku takaimaime inda yake ba,don gudun kar a cutar da shi.An mika mana mahaifinmu yayin da zuciyarsa ke ci gaba da bugawa,sai muka garzaya da shi asibiti a wani wuri na sirri, inda kawo yanzu yake ci gaba da jinya".
Milyoyin mutane daga sassa daban-daban na duniya, sun kalli bidiyon yadda aka yi wa Muammar Gaddafi kisan wulakanci.An yada bidiyon a shafukan intanet da na sada zumunta.Amma da yawa daga cikin 'yan adawan tsohon shugaban kasar Libiya,sun tabbatar da cewa wannan ba komai ba ne face farfagandar magoya bayan Gaddafi da nufin shafa musu kashin kaji.
Lokaci zuwa Lokaci iren iren wadannan labarai kan Muammar Gaddafi na kunno kai a wasu shafukan farko na jaridun nahiyar Afirka da ma kasashen Yamma,amma kawo yanzu babu wanda ya taba tabbatar da sahihancinsu.
Ayar tambaya a nan ita ce, shin da gaske ne Gaddafi na raye ?
TRThausa.

Ashe tsohon shugaban kasar Libiya, Gaddafi na nan da ranshi be mutuba

No comments