Wannan hoton wata kiristace da aka kama sanye da Hijabi da Nikabi tayi satar kayayyaki ta boye a ciki, bayan da aka kamata aka cire hijabin da nikabin data saka sai aka ga kros a wuyanta kuma ta tabbatar da cewa ita kiristace.
Lamarin ya farune a jihar Sakkwato kamar yanda wani me shafin Facebook ya bayyana, ya kara da cewa tana hannun 'yan sanda dan daukar hukuncin da ya dace a kanta.

Kalli wata kirista da akama kama tayi sata sanye da Hijabi da Nikabi

A yaune shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da shugaban kasar Amurka, Donald Trump a fadarshi ta Whitehouse, wanan hoton na daya daga cikin hotunan da aka dauka lokacin ganawar shuwagabannin kuma ya dauki hankulan jama'a, tauraruwar fina-finan Hausa, Hadiza Gabon ta bayyana cewa bata taba ganin Trump yayi irin wannan murmushinba, yaga tauraro shugaba Buhari.
Ga abinda ta bayyana kamar haka:

'Shugaban Amurka, Trump yayi murmushin da be taba yiba saboda murnar haduwa da shugaba Buhari'>>Hadiza Gabon

Sheikh Dahiru Usman Bauchi, yama ganin cewa za'a iya yin auren mut'ah, yayin da bukatar ýa mace ta kama mutum, kuma baya kusa da iyalinsa,
"Idan Tafiya Ta Kama Musulmi Yayi Nesa Da Iyalanshi, Sannan Sha'awar Mata Ta Kama Shi, To Da Yayi Zina Gara Yayi Auren Mut'ah" -
Sheikh Dahiru Bauchi ya fadi hakan ne A Karatun Littafin Muwaddah Wanda Ya Saba Gabatarwa A Gidan Rediyon Tarayya Na Kaduna.
Shin ko hakan ya dace da karantarwar addinin musulunci?
Ko kuma menene banbanci tsakanin zina da auren mut'ah????

Matafiyi zai iya yin auren mutua a maimakon zina, -Inji Sheikh Dahiru Bauchi

Albishirin ku yan uwa yau mun sake kawo muku Sabuwar wakar Rarara me suna Buhari 4+4 domin jindadin ku da nishadantar daku gaskiya wakar ya kayatar kada na cika ku da surutu ko sauke wakar kusha sauraro lafiya.

Downlord mp3 here

Sabuwar Wakar Rarara Buhari 4+4 New Song

 Tauraruwar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi ta mayarwa da wani mutum martani me zafi yayin da ya gaya mata cewa 'Gaskiya Nafi kin fara tsufan' , da alama Nafisa bata ji dadin wannan magana ba, ta mayar mishi da martanin cewa dodanniyace ni da bazan tsufa ba?.
Ta kara da cewa ko ta gidama yarinya take har yanzu?, in kuma yarinyace to zanzo ta bani abinda tasha nima insha.
Bayan wannan martani da Nafisa ta mayarwa da wannan bawan Allah be dai kara cewa uffan ba, kuma wasu sun bata shawarar cewa ta daina kula irin masu wadannan maganganun.


'ko ta gidama yarinya take haryanzu?'>>Nafisa Abdullahi ta mayarwa da wani daya ce mata ta fara tsufa martani

Tauraruwar fina-finan Hausa da turanci, Rahama Sadau ta karyata labarin da wasu kafafen sadarwa suka buga na cewa ta yiwa Atiku Abubakar kaca-kaca akan martanin da ya mayarwa da shugaba Buhari kan maganar da shugaba Buharin yayi akan matasa, Rahama tace bata fadi hakaba.
A cikin labarin an ruwaito cewa Rahama ta cewa Atiku sune suka bata Najeriya kuma In Allah ya yarda Shugaba Buhari ne zai ci zaben shekarar 2019.
Amma Rahamar tace bata fadi wannan magana ba kuma tayi Allah ya isa.
Rahama ta kara da cewa inda sun sameta da tana da labarai da dama da zata basu amma ba akan siyasa ko kuma wani dan siyasa ba.
Ga abinda ta rubuta a dandalinta na Facebook kamar haka:
"Who did this pls?!! Now this is one of the disadvantage of MEDIA!!! FAKE NEWS all over!!! I can’t remember when I had this interview with either of you... Dokin Karfe TV and Najeriyarmu A YAU....
You guys should have come to me if you’d ever need any news to carry on me!!! Trust me, I have plenty to share with you but NOT ON ANY POLITICIAN OR POLITICS. Why publish fake!! Meye ribar yin haka?!! Allah ya isa!!!!!"

Rahama Sadau ta karyata labarin da ake yadawa akan ta na cewa ta yiwa Atiku Kaca-kaca

 Tauraruwar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi kenan a wadannan hotunan nata da ta dauka a kasar Amurka, tasha kyau sosai, a cikin hotunan hadda wanda ta dauka a kafar sadarwar CNN.
Muna mata fatan Alheri.


Kukalli zafafan hotunan jaruma nafeesat abdullahi dasuka burge

Da alama maganar da shugaban kasa yayi akan matasa ta dauki wani sabon salo, musamman tsakanin masu sana'ar a daidaita sahu/keke Napep, inda wasu har sun fara rubutun kalmar 'Cima Zaune' a bayan keken nasu kamar yanda ake iya gani a jikin wannan hoton.

'Yan Adaidaita sahu sun fara rubuta kalmar 'Cima Zaune' a jikin kekensu

Tauraruwar fina-finan Hausa da turanci Rahama Sadau kenan a wannan hoton nata data sha kyau.

Rahama Sadau Yar Kwalisa

 Jarumar fina-finan Hausa, Maryam Yahaya kenan a wadannan hotunan nata da suka kayatar.
Anan me shirya fina-finan Hausa, Abba Maishaddane tare da Maryam.

Kukalli sababbin hotunan maryam yahaya dasuka jawo cece kuce

Lauya kuma malami, Dr. Aminu Gamawa ya bayyana ra'ayinshi akan maganar da shugaban kasa, Muhammadu Buhari yayi dangane da matasan Najeriya kamar haka:
Mutumin namu wani lokaci da Hausa yake tunani shi yasa idan ya furta wasu kalaman da turanci sai kaga sun bada ma’ana wanda ba lalle ne ta gamsar ba. Yanzu lokacin zabe ne. Ya kamata ya iya bakinsa. Ya guji kalamai da za’a iya sauya musu ma’ana ko kuma masu kawo cece-kuce.

'Yanzu lokacin zabene ya kamata ya iya bakinsa'>>Ra'ayin Dr Aminu Gamawa akan maganar shugaba Buhari ga matasa


Sabuwar wakar Saniyo Tare Da Nura M Inuwa A cikin wakarsu mai suna ” Aboki Yafi Budurwa – Budurwa Tafi Aboki ” waka mai dauke da yaro da uban gidansa domin nishadantar daku masoya.
GA KADAN DAGA BAITIN WAKAR:-
– Dawa nafiso zan zauna na zabi abokina
– Nifa budurwatace yar fara gata gaban alfarma
– Abokina nikuma nafi budurwata
– Sanyo Na M Inuwa ne Acikin wakar da mukayo taken budurwa tafi aboki
Allah ka nufa wannan aikin yai mana sauki
– Ni bani musu nasan zaki ya dare gwanki Aboki yafi budurwa
– Soyayya idan da amana tafi karfin komai
– Idan kairashi na budurwa gaske ba a mai mai
– Idan karabe da jamilu tuna akwai dan jummai



Downlord Nura M Inuwa Ft Saniyo M Inuwa Budurwa Tafi Aboki

Saniyo Ft Nura M Inuwa -Aboki Yafi Budurwa

Albishirin ku Maziyarta wannan shafi me albarka
idan baku manta Ba kwanan muka sankamo muku wakokin dauda kahuta rarara wanda yayiwa baba buharai akan har guda 2
To yau kuma naxo muku da wani wakar wanda Muhammad badamasi mani ya rerawa yan PDP me taken Buhari daga hudu ka gama

Download and enjoyed

Downlord mp3 here

Arewatop.com

Sabuwar Wakar Yan Jam Iyar PDP Me Taken Buhari Daga Hudu Ka Gama

Albishirin ku maziyarta wannan shafi me albarka
Yau ma mun sake sake sankamo muku Sabuwar Wakar Rarara wanda yayiwa baba buhari na tsayawa takarar 2019 me sunan ina yan Adawar suke buhari saikai Takwas
Wakar yayai dadi mutuka ku hanzarta ku sauke a wayoyin ku. Arewatop.com

Downlord mp3 here

Sabuwar Wakar Rarara Ina Yan Adawar Suke Buhari Sai Kaiyi Takwas

Tauraruwar fina-finan Hausa da turanci, Rahama Sadau kenan a wannan hoton nata daya kayatar.

Rahama Sadau Yar Kwalisa

Tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Ibrahim Zeezee ta samu mukami daga jam'iyyar adawa ta PDP inda aka bata mukamin shugabar riko ta mata ta kungiyar dake yiwa PDPn kamfe gida-gida ta kasa baki daya.
Ummi da take bayyana wannan labari a dandalinta na sada zumunta da muhawara tace ta godewa Allah da wannan mukami da ta samu yau, kuma tana fatan Allah ya baiwa jam'iyyar ta PDP mulki a zaben shekarar 2019.
Ummi dai tayi suna wajan caccakar gwamnatin shugaba Buhari.
Wani shafi da ya wallafa wannan labari, me suna Authenticnewsdaily yace shugaban kungiyar yiwa PDPn kamfe gida-gida na kasane, Ibrahim Dahiru Danfulani ya tabbatar da wannan mukami na Ummi Zeezee a yau Juma'a.
Muna tayata murna da fatan Allah ya taya riko.

Jam'iyyar PDP ta baiwa Ummi Zeezee babban mukami

 Tauraron mawakin gambara, Musa Morel na murnar zagayowar ranar haihuwarshi, muna tayashi murna da fatan Allah ya karo shekarau masu Albaraka.
Shima mawaki, Ahmad Shanawa na murnar zagayowar ranar haihuwarshi, muna tayashi murna da fatan Allah ya karo shekaru masu Albarka.

Ahmad shanawa tareda morell suna murnar zagayowan ranar haihuwar su


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce maganganun 'yan Najeriya ne suka sa ya bayyana aniyarsa ta sake neman takara karo na biyu a zaben shekara mai zuwa.
Da yake magana a lokacin da ya gana da shugaban mabiyar darikar Anglican Justin Welby, Buhari ya ce yana son ya mayar da hankali wurin bunkasa ayyukan noma da tsaro da tattalin arziki da kuma yaki da cin hanci da rashawa.
Ya kara da cewa "Mafiya yawan 'yan Najeriya sun gamsu da irin ayyukan da mu ke yi, shi ya sa nake so na ci gaba da mulki".
bbchausa.

'Mafi yawan 'yan Najeriya sun gamsu da irin ayyukan da mukeyi: Shiyasa nake so naci gaba da mulki'>>Shugaba Buhari

Real Madrid ta sha da kyar a hannun Juventus a wasan da suka buga daren jiya, zagaye na biyu na gasar cin kofin zakarun turai, wasan na kusa da na kusa dana karshe, Juventus sun rama irin cin da Madrid ta musu a gida watau 3-0, saidai ana daf da wasan zai kare rafli ya bayar da bugun da ga kai sai me tsaron gida ga Real Madrid din, kwallon da Ronaldo yaci.
Wannan bugun daga kai sai me tsaron gida bewa 'yan wasan Juventus dadi ba inda suka taso haikan kanshi, me tsaron gidansu kuma kyaftin, Buffon yana musu jagora, irin tsagerancin da Buffon din yawa raflin yasa ya bashi jan kati wanda ya fiddashi daga wasan. Wasa dai ya kare madrid na da nasara da ci 4-3.
Bayan kammala wasan Buffon ya shaidawa manema labarai cewa abinda Raflin, Micheal Oliver yayi na bayar da bugun daga kai sai me tsaron gida a yayin da ake daf da kammala wasa, ba halin mutane bane, dabbancine, amma ya kara da cewa yana alfahari da kungiyarshi kuma sunyi abinda ba'a tsammani dan haka rayuwa zata cigaba.
Shi kuwa Ronaldo ya shaidawa manema labarai cewa bega dalilin tada hankalin da 'yan wasan Juventus suka yi ba akan bayar da bugun daga kai sai me tsaron gida da Raflin yayiba, yace abinda raflin yayi daidaine, kuma da ace basu taba Lucas ba da zaici kwallon.
Yace suna farin cikin wucewa zuwa wasan daf dana karshe inda ya kara da cewa wasan na jiya da suka buga ya koya musu darasi.
Bayan kwallon da ya ci Juventus jiya, Ronaldo ya doke abokin hamayyarshi na Barcelona, watau Messi da yawan kwallayen da wani dan wasa yaci kungiyar wasa daya a gasar cin kofin zakarun turai, Messi yaci Arsenal kwallaye tara, kwallon da Ronaldo yaci jiya ta zama ta goma kenan, jumulla da yaci Juventus a gasar cin kofin zakarun turai hakan yasa ya wuce Messin.
Haka kuma Ronaldon ya sake kafa tarihi wanda dama tarihin baya shine yake rike dashi a matsayin wanda yafi cin kwallaye masu yawa a kakar wasan cin kofin zakarun turai.
A gasar da aka buga ta shekarar 2014: Ronaldo ne yafi cin yawan kwallaye inda yake da kwallaye 17.
Haka a gasar da aka buga ta 2016: Ronaldonne dai keda mafi yawan kwallaye inda yaci kwallaye 16.
Sai kuma wannan itama ta shekarar 2018: Ronaldonne dai yafi yawan cin kwallaye inda kwallon da ya ci jiya ta zamo ga 15.
Shine na daya, na biyu kuma na uku a wannan tarihi.
Madrid dai sun bi sahun Liverpool da Roma da Munich a matsayin wanda zaau buga wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin zakarun turai.

Ronaldo ya wuce messi a yawan cin abokan hamayya kwallaye: Ya kuma kafa tarihin wanda yafi yawan kwallaye sau 3 a jere: Buffon yace dabbancine yasa Rafli ya bayar da bugun daga kai sai me tsaron gida: Amma Ronaldo yace hakan daidaine

Liverpool ta kai zagayen dab da na karshe a gasar cin kofin zakarun Turai a karon farko cikin shekara 10 bayan da ta doke Manchester City da 2-1 wato 5-1 jumulla bayan wasa biyu.
City ce ta fara zura kwallo ta hannun Gabriel Jesus bayan sakan 116 bayan da Raheem Sterling ya ba shi kwallo.
Bernardo Silva ya daki turke kafin Sane ya ci kwallo amma aka hana saboda zargin satar gida duk da cewa James Milner ne ya taba kwallon.
Mohamed Salah ne ya rama wa Liverpool kafin Roberto Firmino ya ci ta biyu.
Liverpool za ta san kulob din da za ta kara da shi a ranar Juma'a lokacin da za a raba kungiyoyin a Nyon, na kasar Switzerland.
City ce ta mamaye kashin farko na wasan inda ta zubar da damarmaki, kafin Liverpool ta farfado a zagaye na biyu.
Alkalin wasa ya kora Pep Guardiola cikin 'yan kallo bayan da ya yi korafi kan hana kwallon da Sani ya ci a lokacin da aka ta fi hutun rabin lokaci.
bbchausa.
Wadannan kwallaye biyu da Liverpool taci jiya sun bata damar goge tarihin da Manchester United ta kafa, Shekaru goma sha biyar da suka gabata, inda yanzu Liverpool din take kan gaba a matsayin kungiyar kwallo daga Ingila dake da mafi yawan kwallaye a kakar wasan cin kofin zakarun turai da kwallaye talatin da uku.
Haka shima Muhammad Salah yaci kwallonshi ta talatin da tara a kakar wasa ta bana inda hakan ya bashi damar zuwa kankankan da tsohon tauraron kwallon kafa, Samuel Eto'o wanda shine dan Afrika da yafi yawan kwallaye a kakar wasan cin kofin zakarun turai da kwallaye takwas, yanzu Salah shima kwallayenshi takwas, idan ya samu ya sake cin wata kwallon a wasan kusa dana karshe da zasu buga, zai wuce Eto'o inda zai zama dan Afrika da yafi yawan cin kwallaye a kakar gasar cin kofin zakarun turai.
Barcelona tasha kashi a hannun A.S Roma inda Roman suka yi musu cin goge raini, 3-0 wanda gaba daya har wasan farko da suka buga ya tashi 4-4 kenan, Barcelona dai zata hada komatsenta ta koma gida daga gasar cin kofin zakarun turai na bana kenan.

Liverpool ta cire Man City ta kuma kafa tarihi: Salah ya kamo Eto'o a yawan kwallaye: Roma ta cire Barcelona

Tauraron mawakin Mata, Ado Isah Gwanja kenan tare da dan uwanshi Musa Gwanja a wannan hoton nasu da suka haskaka. Muna musu fatan Alheri.

Kukalli Ado Isa Gwanja Tareda Dan Uwansa Musa Gwanja

 A wata hira da tayi da jaridar Daily Nigerian, tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Zeezee ta amsa tambayoyin da wakilin jaridar ya mata akan rayuwarta, ciki hadda soyayyar da tayi da mawaki Timaya ta kuma bayyana cewa ta siyawa dukkan masu aiki a karkashinta gidaje da motoci.
Ummi ta bayyana cewa tuni ta daina harkar fim saboda duka-duka nawa za'a biyata a aikin fim?.
Da take amsa tambaya akan gashin kanta da take yawan nunawa, kamar yanda wakilin jaridar ya tambayeta, ta bayyana cewa, ba gaskiya bane, duk da yake cewa ita Kanuri ce kuma suna da gashi kuma tana alfahari da hakan shiyasa take nunashi ga Duniya amma ba koda yaushe take yin hakan ba.
Ummi ta kara da cewa ita mutumce me riko da addini kuma takan karanta Qur'ani da Hadisi kuma tana kokarin bin dokokin addini daidai gwargwado. Ta kara da cewa shiyasa da zata mutu a dawo da ita zata so a dawo da ita a matsayin Ummi Ibrahim, musulma, 'yar Najeriya.
Da take amsa tambaya akan cewa mutane na ganin kudin da ake cewa tana dashi na karyane, Ummi ta bayyana cewa, Wallahi tana da kudi ta yanda koda za'a mata kyautar miliyoyin kudi bawai wani farin ciki zata yi sosai ba kamar yanda sauran mutane suke tunani, Ummi ta kara da cewa ta saiwa dukkan masu aiki a karkashinta gidaje da motocin hawa.
Da take amsa tambayar ko tana da wani abu data taba yi a rayuwarta wanda yanzu take danasanin yinshi?, Ummi ta bayyana cewa a kwanakin baya lokacin da tayi soyayya da mawakin Najeriya Timaya wasu sun rika cewa wai ta bar musulunci saboda Timayan, to wanna abu ba karamin bata mata rai yake ba duk lokacin da ta tunashi. Tace bata ga abinda zai sanya ta bar addinin musulunci ba.

Ni me arzikice sosai: Na saiwa dukkan masu aiki karkashina motocin hawa da gidaje: Nayi nadamar yin soyayya da Timaya>>Ummi Zeezee

Diyar attajirin dan kasuwa, Adama Indimi kenan a wadannan hotunan nata da suka kayatar wanda ta dauka a gurin wani taron nuna kawa da akayi, ta yi kyau.



           

Hotunan Adama Indimi Dasuka Burge

Shahararren Mawaki Na Kasar Hausa Adam A Zango Ya Sanya Dan Cikin A Harkar Waka Inda A Yanzu Mutane Suna Jiran Wakokin Yaron Nasa Wanda Zasu Fito Amma Karda Ku Damu Zamu Baku Video Wanda Yaron Ya Dauka Yana Waka.
Toh, Sunan Yaron Zango Din shine, Haidar Zango Wanda Yana Ma Kansa Lakabi Da Starboy Na White House Family.
Idan Kun Kalli Video Din Zaku Fahimci tsarin Yaron Ya So Ya Kwaikwayi Marigayi Lil Ameer Wanda Bayan Rasuwar Sa Yayi Suna Matuka ..
Sunan Wakar Haidar Zango Itace Mai Taken - Godiya.. sadikblog


Downlord haidar gadiya mp4

Bidiyon Wakar Yaron Zango Na Cikin Sa Wanda Ya Kwaikwayi Tsarin Mawaki Lil Ameer