Domin kallon cigaban satin da yaga bata yau mun kawomuku na wannan satin domin cigaba da kallon inda kuka tsaya a wancan satin kawai ku biyomu
Da AYUBA ya yanke jiki ya fadi, ko me yake ciki a halin yanzu? NAZIR ya dira a garin Dadin Kowa, bamu san me ai sa a gab aba.
SALLAU ya fada cikin rudani tun da MAMUDA ABUJA ya damfare shi.
STEPHANIE na cikin tsaka mai wuya, ko ya matsayinsu da NASIR dan MAL. HASSAN? An sace ‘yar KAMAYE, bamu san me zai biyo bay aba.
Mutanen sun sako salon shiga watakil da sabon salon yin aika-aika, a yayin da ZAYYAD ya bayyana.
Domin kallon yadda zata kaya a wannan satin kawai kuyo donwload dinsa kusha kallo. Arewablog


Downlord Dadin Kowa 38 here

Dadin Kowa Sabon Salo Episode 38 | Arewa24

Mata masu rufe kawunansu da dan kwali da Hijabi, Allah ya san daku, Duniya ma ta fara baku Muhimmaci, a kwanakin bayane mukaji labarin wata ba'amurkiya da akayi 'yar tsana me Hijabi ta farko a Duniya dan karramata saboda saka Hijabi da take duk da cewa tana wasannin motsa jiki.
Haka kuma munji yanda kamfanin NIKE a shekarar data gabata shima yayi Hijabi ga mata musulmai masu motsa jiki . Anan ma wani kamfanin sayar da kayan kwalliya na matane da suka hada da Kayan Gyaran gashin kai na kasar Faransa me suna L'Oreal yayi abinda ba'a saba ganiba. Inda ya dauki wata me watsa labarai ta kafar Youtube kuma musulma me son rufe gashin kanta me suna Amina Khan ta zama daya daga cikin jakadunshi dake tallata kayan gyaran gashin kamfanin.
Abin ya dauki hankulan mutane da dama, dan an saba ganin masu tallar kayan gyaran gashi da kai a bude suna kwarkwasa amma gata ita kanta a rufe, ta bayyanawa manema labarai cewa rufe kansu da suke a matsayin musulmai bawai yana nufin basu damu da gyaran gashinsu bane, suma suna da matsalar gashi kamar kowace mace kuma suna kula dashi.
Anta yabawa Amina da kuma kara karfafamata gwiwa da kuma godemata da irin wannan namijin kokari datayi na karfafawa masu saka hijabi gwiwa, Duniya tayi dasu.
CNN.

Abin birgewa: An dauki musulma me rufe gashin kanta tallar man gyaran gashi: Itace ta Farko

Tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango kenan tare da matarshi(Amarya) da diyarshi da kuma mahaifiyarshi a gurin nuna sabon fim dinshi na Gwaska ya Dawo da akeyi a Ado Bayero Mall dake Kano, Adamun ya bayyana cewa iyalanshi ma sunzo kallon fim din.
Masoyanshi da dama sun yaba da wannan abu. Saidai wasu sun rika tamabayar wai ina uwargidan Adam A. Zangon?.


Adam A. Zango da mahaifiyarshi da matarshi da diyarshi a gurin nuna fim dinshi na Gwaska ya Dawo

A jiya, Asabarne, iyalan gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi suka kai kayan lefen diyar gwamnan jihar Kano, Fatima Abdullahi Umar Ganduje wanda za'a aurawa dansu Idris Ajimobi, Manyan mata daga Arewa da suka hada da, Uwargidan gwamnan jihar Kebbi da ta Kogi da Jigawa da sauransune suka halarci wannan hidima.
Anyi kwarkwaryan shagali inda har har sarkin Kano, Muhammad Sanusi na II ya shiga ciki, an kammala sun koma gida, muna fatan Allah yasa ayi wannan biki lafiya ya kuma basu zuri'a dayyiba. Amin.



Kalli kayan Lefen diyar gwamnan jihar Kano, Fatima Ganduje da dan gidan gwamnan Oyo Idris Ajimobi ya mata

Me kula da kafafen sada zumunta na yanar gizon gwamnatin jihar Kano, Salihu Tanko Yakasai kenan inda maganar saka jar hula ta shiga tsakaninshi da wani bawan Allah, Ashe dai abin da gaskene.
A karshe dai salihu shiru yayi wata kila yana gudun kada maganan 

Ashe dai abin da gaskene: Kalli yanda maganar saka jar hula ta kaya tsakanin ma'aikacin Ganduje da wani

Wani matashi kenan me suna Muhammad Kadade Sulaiman daya fito neman takarar gwamnan jihar Kaduna, a jiyane dai gwamnan jihar ta Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai yake baiwa matasa shawarar cewa idan fa sunaso su amshi mulki a kasarnan sai sun shiga(siyasar)an dama dasu, zage-zage a kafafen yanar gizo bazai canja komi ba.

Htotunan Matashin Da Yafito Neman Takarar Gwamnan Kaduna State

Allah me shirya wanda yaso, daya daga cikin jigon 'yan jam'iyyar kin jinin baki da musulmai a kasar Jamus watau AFD a takaice me suna Arthur Wagner ya musulunta, Jam'iyyar dai ta masu tsatstsauran ra'ayice akan baki da musulmai a kasar ta Jamus.
Kuma har ta samu shiga majalisar kasar ta Jamus saboda wani tsari data fito dashi na kin jinin musulunci da tsaurara dokokin shiga kasar ta Jamus dan maganin 'yan cirani da 'yan gudun hijira masu zuwa kasar sun ragu.
Jam'iyyar ta tabbatar da komawar Arthur Wagner Musulunci kuma tace ba wani abin damuwa bane a gareta domin dama a cikin jam'iyyar tasu akwai wakilan adinin musulunci da Kiristanci haddama 'yan Luwadi.
DailySabah

Jigo a jam'iyyar kin jinin addinin musulunci ya musulunta a kasar Jamus

Tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa, Abida Muhammad ta kusa zama Amarya, ranar Juma'a me zuwa, 26 ga watan Janairu za'a daura auren na Abida da Angota Mustafa, Muna fatan Allah ya basu zaman lafiya.
Muna musu fatan Allah yabada zaman lafiya.

Jarumar Hausa Film Abida Muhammed Zatayi Aure