Kalli wasu kayatattun hotunan Rahama Sadau da 'yan uwanta
 Tauraruwar fina-finan Hausa da turanci, Rahama Sadau kenan a wadannan kayatattun hotunan nata tare da 'yan uwanta, hotunan sun kayatar sosai, Rahamar sai ta koma kamar karamar yarinya 'yar shekaru kasa da ashirin.
Muna musu fatan Alheri.

Kalli wasu kayatattun hotunan Rahama Sadau da 'yan uwanta

Dr. Ahmad Gumi da sauran manyan malaman kirista sun jagoranci sasanta Atiku da Obasanjo: Obasanjon yace ya yafe kuma Atikun yafi Buhari
Shehin malamin addinin Islama, Dr. Ahmad Gumi da malamin addinin kirista, Bishop Mattew Hassan Kuka da Bishop David Oyedepo da sauransu ne suka wa tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar rakiya zuwa gidan Obasanjo.
Rahotannin dake fitowa daga shafin Sahara Reporters da Punch na cewa, a lokacin ganawar tasu, Obasanjo ya taya Atiku murna inda ya kirashi da shugaban kasa me jiran gado.
Obasanjo ya shaidawa manema labarai cewa, ya yafewa Atiku duk wani laifi da yayi mishi saboda shima yana neman gafarar Allah, ya kuma kara da cewa zaben fidda gwanin PDP da Atiku ya lashe ba magudi aka yi ba.
Obasanjo ya kara da cewa, Atikun yafi Shugaba Buhari kwarewa a fannin tattalin Arziki kuma idan ya samu shugabancin Najeriya zai kawo ci gaba sosai ta fannin kasuwanci

Dr. Ahmad Gumi da sauran manyan malaman kirista sun jagoranci sasanta Atiku da Obasanjo: Obasanjon yace ya yafe kuma Atikun yafi Buhari

Kalli wasu kayatattun hotunan Maryam Yahaya
 jarumar fina-finan Hausa, Maryam Yahaya kenan a wadannan hotunan nata da ta sha wandan sojoji, ta yi kyau,tubarkallah, muna mata fatan Alheri.




Kalli wasu kayatattun hotunan Maryam Yahaya

Domin Kallon cigaban shirin dadin kowa na satin da ya wuce to ku kasance tare damu.

Alawiyya ta yi wani yunkuri abin yabawa.

 Wani malamin boko, malam Danbala ya fara tabka tabara.

Kawun Dan Tani wato Kuma Manu ya dau zafi.

Adama da kyauta dillaliya sun warota.

Downlord video direct

Watch from Arewa24

#arewablog


Dadin Kowa Sabon Salo Episode 74 Arewa24

Duk da zargin fyade da ake mishi Ronaldo ya ciwa Juve kwallo a karawarsu da Udinese
Zargin da akewa tauraron kwallon kafar Juventus, Cristiano Ronaldo na yi wa wata mata 'yar kasar Amurka Fyade be sa yayi kasa a gwiwa ba wajan yin aikinshi yanda ya kamata ba dan kuwa a wasan da Juve ta buga jiya, Asabar da Udinese, Ronaldon ya ci kwallo.
Ronaldo ya ciwa Juve kwallo ta biyu wadda ta kaita ga samun nasara a wasan da ci 2-0.
A lokacin da ya shiga filin wasan, masoya kwallon kafa sun rika kiran sunanshi ana hargowa.

Duk da zargin fyade da ake mishi Ronaldo ya ciwa Juve kwallo a karawarsu da Udinese

Ali Nuhu yayi askin rabin miliyan: Abinda babu jarumin Kannywood da ya taba yi
Ali Nuhu, Sarki na daya daga cikin jigo a masana'antar fina-finan Hausa wanda ya bayar da gudummuwa matuka wajan ci gaban masana'antar, idan za'a kira sunayen taurarin masana'antar da suka fi yin fice tun kafuwarta to idan be zo a na daya ba, ba zai wuce na biyu ba.
A wannan karin wani tarihine da Alin ya kafa wanda ba'a taba samun wani jarumin masana'antar da irinshi ba.
Me shirya fina-finai, Alhaji Shehe na kan shirin wani sabon fim dinshi me suna Kazamin Shiri,  Ali Nuhu na daya daga cikin jaruman da zasu fito a wannan shiri to saidai ana bukatar ya aske gashin kanshi wanda watakila shi bashi da shirin yin hakan.
Amma Alhaji Sheshe ya janyo hankalin jarumin da makudan kudin da ya sakar mishi har 500,000 dandai kawai yayi wannan aski.
Sheshe ya saka wani hoton Ali Nuhu dake dauke da rubutun cewa, Aski mafi tsada a tarihin Kannywood furodusa Alhaji Sheshe ya biya Ali Nuhu naira 500,000 ya aske sumar sa don fitowa a shirin.
Lallai wannan abin tarihine wanda ba za'a taba mantawa dashi a masana'antar ba.

Ali Nuhu yayi askin rabin miliyan: Abinda babu jarumin Kannywood da ya taba yi

 Taurarin fina-finan Hausa, Maryam Yahaya da Amal Umar kenan a wadannan hotunan nasu da suka sha kaya kalar tutar Najeriya dan nuna farin ciki da cika shekaru 58 da samun 'yancin kai.
Sun sha kyau muna musu fatan Alheri.






Kalli kwalliyar ranar 'yanci ta Maryam Yahaya da Amal Umar

 Taurarin fina-finan Hausa, Fati Washa da Bilkisu Shema kenan a wadannan kayatattun hotunan nasu da suka kayatar, sun sha kyau, tubarkallah, muna musu fatan Alheri.

Kalli kayatattun hotunan Fati Washa da Bilkisu Shema