Hotunan Maryam Booth da suka birge
Tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Booth kenan a wadannan kayatattun hotunan nata da suka birge, tasha kyau, muna mata fatan Alheri.



Ka yi hankali da wanda kake sharewa, wataran zaka bukaceshi>>Rino Omokri ya gayawa Kwankwaso bayan ziyarar da ya kaiwa Jonathan
A cikin satinnan da muke cikine tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kaiwa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ziyara, wani na hannun damar Jonathan din, Reno Omokri yawa Kwankwaso Shagube.
Rino ya dauko hoton da Kwankwaso da mukarrabansa lokacin yana gwamna suka share filin da Jonathan ya kai ziyara a jihar ta Kanon yace, kayi hankali da wanda kake sharewa, wataran zaka bukaceshi.

Ka yi hankali da wanda kake sharewa, wataran zaka bukaceshi>>Rino Omokri ya gayawa Kwankwaso bayan ziyarar da ya kaiwa Jonathan

Real Madrid zata sayi Kylian Mbappe idan...
Hukumar kula da kwallon kafa ta Duniya, FIFA na duba yiyuwar sakawa kungiyar kwallon kafa ta PSG takunkumi akan karya dokar kashe kudi da suka wuce kima wajan sayen 'yan wasa da albashin ma'aikata.
Idan FIFA din ta sakawa PSG wannan takunkumi zai zama dole a gareta ta sayar da daya daga cikin shahararrun 'yan kwallon ta. Lokacin aron Kylian Mbappe da suka amso daga Monaco zai kare ranar Litinin wanda zasu hadu da zabin kodai su sayi dan wasan akan kudi Yuro miliyan 180 wanda zaisa su kara karya wata dokar ta kashe kudi fiye da kima ko kuma su mayarwa da Monacon da shi, kamar yanda AS ta ruwaito.
Idan dai FIFA ta kakabawa PSG wannan takunkumi, to kungiyar Real Madrid ce ake tunanin zasu sayi dan wasan domin kuwa kasuwannin cinikin 'yan wasa a Ingila da Italiya duk a kulle suke.
Wannan zai baiwa Madrid din damar maye gurbin Cristiano Ronaldo da ta rasa.

Real Madrid zata sayi Kylian Mbappe idan...

Duniyarnan sai mutum yayi tunanin ya gama jin abin mamaki sai wani sabo ya fito, wani labarine daya fito daga kasar China ke bayyana wasu ma'aurata da sukayi aure sama da shekaru 4 amma matar tana nan a sabuwar budurwarta saboda sunata yin jima'ai ba ta daidaiba a rashin sani, damuwar rashin haihuwa da suka shiga ciki ce ta sa labarin ya bayyana.
Ma'auratan wanda ba'a bayyana sunayensu ba saidai shekaru, matar tana da shekaru 24 mijin kuwa yana da shekaru 26, kamar yanda kafar watsa labarai ta Mirror ta kasar Ingila ta ruwaito.
Sunje asibiti sukawa likita korafin cewa suna ta jima'ai akai-akai tun bayan aurensu, yanzu shekaru 4 kenan amma babu maganar daukar ciki. Likitar da suka samu me suna Liu Hongmei ta bayyana cewa ma'auratan matasane kuma suna da lafiya dan haka abin da ban mamaki.
Matar ta mata korafin cewa tana jin zafi sosai lokacin jima'in amma saboda son haihuwa take jurewa.
Likita Liu ta bayyana cewa, ta sa a bincika matar sai suka gano wani abu me matukar ban mamaki, abinda suka gano kuwa shine matar haryanzu budurcinta na nan kamar budurwar da bata san namiji ba.
Da bincike yayi tsanani sai aka gano ashe ta dubura suke jima'ai shiyasa bata dauki ciki ba.
Bayan gano hakane, likita Liu ta zaunar da ma'auratan ta musu hudubar yanda ake jima'ai sannan ta basu littafin dake koya ilimin jima'i.
Da take hira da manema labarai, likitar tace, abin mamakine kuma ba'a cika samun irin wannan lamari ba ace ma'aurata sunyi aure tsawon shekara 4 amma basu san yanda ake daukar ciki ba.
Bayan 'yan watanni kadan sai ga ma'auratan sun dawo da kyautar kwai 100 da kaza ga asibitin saboda matar ta dauki ciki.

Labari me matukar ban mamaki: Shekaru 4 bayan aure sunata jima'ai amma har yanzu matar na nan da budurcinta

CANJA RANAR BABBAR SALLAH: Musulman Nijeriya Za Su Rana Azumi Daya>>Sheikh Dahiru Bauchi
Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan Sheikh dahiru Usman Bauchi ya ce idan ya tabbata an ga watan Ramadan da ya wuce a yammacin Talata amma aka ki bayyana labarin ga Musulmin Nijeriya don a yi daidai da Saudiyya wajen daukar azumi to Musulmin Nijeriya za su biya azumi daya na ranar Laraba.
Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana haka ne lokacin da majiyarmu ta Aminiya ta tuntubi Shehin Malamin game da takaddamar da ta taso kan jikirta ranar Babbar Sallar bana, inda watan Zul-kida yana da kwana 28 Kwamitin Ganin Wata ya bayyana washegari 1 ga Zul-Hajji, don komawa aiki da ganin watan Saudiyya.
Sheikh Dahiru Bauchi ya ce, saboda wadanda alhakin sanar da ganin wata ke hannunsu a Najeriya ba addini suka karanta ba shi ya sa suke ganin saukin hadarin abin. “Da a ce sun karanta addini ne da sun san akwai Yaumi Shakki a lokacin da duniya ba ta hadu wajen kafofin watsa labarai ba. Na biyu da a ce an karanta addini da an san madala’in ganin watan ’yan Najeriya ba daya ne da na Saudiyya ba, saboda haka akan iya yin azumi daya zuwa biyu wani sa’in, kafin Saudiyya ta dauki azumi,” inji shi.
Sheikh Dahiru Bauchi ya ce, abin da ya kamata a gane filin samaniya na ko’ina daban ne, “Mukan dauki azumi a Najeriya in mun je Kaulaha sai mu cika azumi 30 su ba su ga wata ba, sai mu fada wa Shehu Ibrahim (Radiyallahu anhu) mu ce masa yaya za a yi mu mun cika azumi 30 kuma a nan kasar Senegal ba a ga wata ba? Sai Shehu ya ce mana, Shehu ya ce a Najeriya ku sai da kuka ga wata kuka dauka muka ce masa ce.
Sai ya ce to gobe ku kada ku yi azumi kuma kada ku sha ruwa, wato sai a ajiye niyyar azumin kuma ba za ku ci abinci ba. Wato ya zama kamar kamun baki, wato kamar a garinku kai ba ka ga wata ba gari ya waye aka tashi da azumi ka ga kai da ba ka ga wata ba, ba za ka sha ruwa ba don ana azumi kai kuma ba ka yi niyyar azumi ba, sai ka kama baki.
Haka in azuminka ya cika amma inda kake ba a ga wata ba sai ka kama baki ba azumi ba cin abinci. Allah ne Yake da kowane filin sama da ake ganin wata kuma kowane filin sama na kowace kasa da lokacin ganin watansa da Allah Ya sa.”
Shehin ya ce sai a ji wadansu suna cewa a dauki na Makka, alhali saman ganin watan Makka daban da na ganin watan Najeriya. “Idan lokacin ganin watanku ba daya ba ne dole ku saba da su a samu bambanci. Amma na Idin Layya nan ne ake bin kasar Makka don ba inda ake da Arfa sai Makka din don haka ba za mu yi Layya ba, ba za mu yi Idin Layya ba sai bayan sun yi Arfa,” inji shi.
Ya ce addini nassi ne a farko sannan imani ya biyo baya, sai hankali ya biyo bayan imani. “Amma a ilimin zamani hankali ne a gaba a cikin duk sha’anonin rayuwa. Idan aka dawo kan abin da ya shafi Najeriya da Saudiyya a kan watan Zul-Hajji a nan ana amfani da lissafin ganin watan Saudiyya ne don ita take da Arfa a duk duniya. Saboda haka kowa zai bar lissafinsa ya bi na Saudiyya saboda su suke da filin Arfa domin ranar 8 ga lissafinsu ake fita filin Muna don fara aikin Hajji.
Idan alhazai suka kwana ranar 9 su tafi filin Arfa idan sun dawo Muzdalifa suka kwana wayewar garin 10, sai duk duniya a tashi da Sallar Layya. Saboda haka lissafinsu ne ake amfani da shi a watan Zul-Hajji, saboda su suke da filin Arfa, sabanin watan Ramadan wanda ba sai an jira ganin Saudiyya kafin a dauka ba,” inji Shehin.
Sheikh dahiru yace, Bauchi don haka idan aka yi Arfa ran 9 watan Zul-Hajji, ya zamo ke nan washegari dukan Musulmi su karrafa bakin Allah da suka yi Hajji suka hau Arfa, a yi yanka ranar goma ga watan Zul-Hajji, wannan yanka ana yin sa ne duk duniya don a karrama bakin Allah da suka yi Hajji sunan yankan Layya amma bakin Allah ake karramawa a yi Idi a gode wa Allah, ranar goma ga Zul-Hajji ranar Babbar Sallah.
Rariya.

CANJA RANAR BABBAR SALLAH: Musulman Nijeriya Za Su Rana Azumi Daya>>Sheikh Dahiru Bauchi

Magidanci ya kasa hakuri: Yabi matarshi har gadon asibiti ya tara da ita a gaban sauran marasa lafiya
Wani mutumi dan kasar Zimbabwe na hannun hukuma sakamakon silalewa dakin marasa lafiya mata a asibitin Masyingo misalin karfe 3 na safe domin tarawa da matarsa dake kwance a asibitin.
Mutumin wanda shahrarren mai sayar da abinci a cikin garin yayi sa’insa da ma’aikatan asibiti cikin dare dan sun hanashi ganin matarsa.
Daga karshe ya samu shiga asibitin kuma ya tara da matarshi a gaban sauran marasa lafiya goma dake cikin dakin.
Shugaban asibitin, Amadeus Shamu, ya tabbatar da faruwan wannan abu ga jaridar iHarare kuma yace asibitin sun fara gudanar da bincike.
Shamu yace: “Misalin karfe 3 na dare marasa lafiya masu jinya suka fara damuwa da karan wasu masu Tarawa da juna. Sai ma’aikatan asibitin suka kira jami’an tsaro su fitar da mutumin daga asibitin.”
Binciken da aka gudanar na nuna cewa matar na tsoron mijin ne kuma idan taki yarda ya tara da ita zai iya dukanta cikin jama’a duk da rashin lafiyanta.
Naija.ng

Magidanci ya kasa hakuri: Yabi matarshi har gadon asibiti ya tara da ita a gaban sauran marasa lafiya

Modric, Ronaldo, Salah na takarar gwarzon Uefa
An bayyana sunayen Luka Modric, Cristiano Ronaldo da Mohamed Salah cikin jerin farko na 'yan wasan da ke takarar gwarzon dan wasan zakarun Turai, Uefa, na bana.
Kwamitin da ya kunshi alkalan wasa 80 da 'yan jarida 55 ne ya zabi dan wasan tsakiya na Real Madrid Modric, dan wasan gaba na Juventus Ronaldo da kuma dan wasan gaba na Liverpool Salah domin yin takarar.
Za a ba da kyautar gwarzon dan kwallon kafar ne lokacin da za a yi wasannin rukuni na gasar cin kofin zakarun Turai a Monaco ranar 30 ga watan Agusta.
An bayyana sunayen Pernille Harder, Ada Hegerberg da kuma Amandine Henry domin fafatawa don zama gwarzuwar 'yan kwallon kafar Uefa ta mata a bana.
'Yar wasan gaba ta Denmark Harder tana buga wa Wolfsburg wasa, yayin da 'yar wasan gaba ta Norway Hegerberg da 'yar wasan baya ta Faransa Henry ke buga wasa a Lyon.
Ronaldo, wanda ya koma Juventus daga Real Madrid a watan Yuli a kan £99.2m, ya taba lashe gasar a 2017, yayin da Lieke Martens ta lashe gasar jim kadan bayan ta koma Barcelona daga Rosengard.
BBChausa.

Modric, Ronaldo, Salah na takarar gwarzon Uefa

Labarin Zion ya taba zukatan mutane da dama domin kuwa duk da kalubalen da ya fuskanta a rayuwarshi be yadda ya zama nauyi akan mutane ba, ya tashi tsaye dan ganin ya zama abin alfahari ga jama'arshi.
Labari me taba zuciya na matashin da aka haifa babu kafa
 Allah me yin yadda yaso, wani sai yayishi da cikakkiyar halitta da lafiya, wani kuma yayishi da kudi amma ya kwace lafiyar, wani kuma yana cikin rayuwar za'a canjamai fasali, wannan bawan Allahn me suna Zion Clark dan kasar Amurkane da aka haifeshi babu kafa saidai kuma wannan be hanashi yin hobbasa dan cimma burin rayuwarshi ba.
Bayan kasancewar Zion bashi da kafa, kuma ya tasone a gidan riko, yanzu dai yana makarantar sakan direne kuma yana yin wasan kokawa wanda dama shine burinshi.






Labari me taba zuciya na matashin da aka haifa babu kafa

A yaune akayi hawan Arfa a kasa me tsarki inda kimanin mahajjata miliyan biyu da suka fito daga kasashen Duniya daban-daban suka halarci gurin wannan babbar Ibada, daga cikin jaruman fim din Hausa da suka samu zuwa aikin Hajjin bana suma anyi wannan Ibada tare dasu.
Daga cikin taurarin akwai mawaka irinsu, Ali Jita, Nazir Ahmad Sarkin waka sai kuma me bayar da umarni, Aminu Saira, Sai jarumai, Hafsat Idris da Rahama Sadau da tsaffin jarumai irinsu, Mansurah Isah da Samira Ahmad da Saratu Gidado, Daso dadai sauransu.
Muna fatan Allah ya amsa Ibada.


Wasu daga cikin jaruman fina-finan da aka yi hawan Arfa dasu a yau