Tauraron mawakin Hausa, Nura M. Inuwa ya bayyana cewa shima Adam A. Zangone jaruminshi a cikin jaruman fina-finan Hausa, Bello Muhammad Bello(General BMB) ma ya bayyana Adam A. Zango a matsayin gwaninshi.
Ga sakon Nuran kamar haka:
"Giwa dabbar wahabu kena lokacin da tunani su ya tsaya daga nan namu yake farawa niba yaron kowa bane ba kuma dan aike bane an dade ana ruwa kasa na shanyewa ina kara fada muku sake shiri in kuma zaku iya ku fito fili mu gwabza tunda
haka kukeso koda laifi in naso wanda yake sona?"

Nima Adam A Zangone Gwanina >>Nura M Inuwa

 Budurwar mawakin mata, Ado Isa Gwanja kenan, Maimunatu a wadannan hotunan nata da tayi kyau, Adonne ya saka hotunan a dandalinshi na sada zumunta, da alama dai bikin nasu yana dada matsowa.
Muna musu fatan alkairi

Kalli budurwan ado gwanja dazai aura

 Jarumar fina-finan Hausa, Amina Amal kenan a wannan hoton nata na musamman, a satin daya gabatane Amina ta saka wani hoto da bai dace ba har masoyanta su ka yi Allah wadai dashi dalilin haka yasa ta cire hoton.
Watakila shiyasa da ta tashi saka wannan sai bata bayar da damar a fadai ra'ayi a kanshi ba.

Amina Amal Yar Kwalisa

Wani abin al'ajabi ya faru a Makurdi jihar Benue wanda ya daurewa mutane kai wasu suka rika fadin cewa karyane wasu kuma abin dariya ya basu. Wata ma'aikaciyar hukumar shirya jarabawar shiga jami'a, Jamb ce ta bayyana cewa kudin katin da take sayarwa da dalibai da yawansu yakai miliyan talatin da shida sun bace, kuma wai wani shu'umin macijine ya hadiye kudin.
Matar me suna Philomina Chieshe ta bayyanawa hukumar bincike da aka nada ta binciki yanda kudin suka bata cewa, idan ta sayar da katin jarabawar Jamb takan kai kudin banki amma sai take shan wahala wajan lissafi da bada ba'asin yawan kudin, dalilin hakane yasa ta koma ajiye kudin a gida.
Ta kara da cewa abin al'ajabi shine sai taga kudin suna bacewa a duk lokacin da taje zuba wasu, wannan dalilin yasa ta fara bincike kuma ta gano cewa yarinyar aikin gidanta ce da wani daga cikin ma'aikatar ta Jamb suka hada baki suke sace kudin ta hanyar sihiri inda suke aiko wani maciji yana hadiye kudin.
Matar ta bayyana cewa, me aikin natace da kanta ta gayamata yanda suke satar kudin kuma itama abin ya bata mamaki sosai.
Dailypost

Wata sabuwa; Maciji ya cinye kudin sayar da katin Jamb da yawansu yakai miliyan 36

A sakon data yiwa abokin aikinta, Umar M. Sharif na tayashi murnar zagayowar ranar haihuwarshi, Rahama Sadau ta bayyana cewa Umar din jinin jikintane, dama a kwanakin baya Rahama ta bayyana cewa Umar ne take so a cikin masana'antar ta fina-finan Hausa.
Ga abinda ta rubuta kamar haka:
Ina tayaka murnar zagayowan ranar haihuwarka jinin jikina.

"Umar M. Sharif jinin jikina ne">>Rahama Sadau

Tauraron mawakin Hausa, Umar M. Sharif na murnar zagayowar ranar haihuwarshi, muna tayashi murna da fatan Allah ya karo shekaru masu Albarka.

Umar M Sharif Na Murnar Zagayowan Ranar Haihuwanshi

Tauraron mawakin Hausa, Nura M. Inuwa ya bayyana cewa ya samu wani sako daga wani wanda be tantance ko wanene ba yana gayamai cewa shi yaron wani jarumin fina-finan Hausane kuma zasu karasa aikin da suka fara a kanshi.
Nura ya bayyana cewa me sakon yace mai a karshe yasan ya razana, amma Nuran yace ba ya jun tsoron kowa sai Allah kuma zai wallafa irin sakonnin da aka aikamai.
Ga sakon nashi kamar haka:
"
Ga duk wanda yaga hoton nan zai mamaki
Domin tunda nake bantaba dorashi a kowacce kafar sadarwa ba,sai dai nayi karo dashi kuma idan nayi karo dashi huceshi nake saboda bana bukatar ganin sa domin banaso ya dinga tunamin yadda nake a baya.duk da kalu balan da nake fuskanta daga jama a na goranta mini da suke akan halittata kuma bani da ikon yin magana dan gudun kada ace na fiya raki da habaice habaice,bana tuna matsalar data sameni sai an goranta mini sannan nake tuna nima ba haka ALLAH yayi niba kaddarace ta sameni kamar yadda nasan babu wanda yafi karfinta, ina kokarin jure abubuwan da ake mini a bayan fage domin nasan zan iya shanyewa,ana mini abubuwa daban daban da nufin tsoratarwa
Kamar yadda yanzu nake dauke da sakon daya daga cikin yaran wani jarumin kannywood cewa sai sun karasa aikinsu a kaina kuma wai shege ka fasa a cewarsa bansan ko waye ba amma nasan da akwai sunan jarumin tunda anfara wasan zan dora duka sakonnin da akayi mini da kuma number sannan a karshen yace yasan na tsorata to NURA M INUW ALLAH daya nake tsoro ba mutum ba."
Sai muce Allah ya kyauta.

Wanda suka watsawa Nura M Inuwa Acid sunce mai zasu zo su karasa aikinsu

Preorder Black Panther The Album http://smarturl.it/BlackPantherAlbum Directed by Dave Meyers & the little homies Black Panther The Album Music From And Inspired By Album on All Digital Platforms & In Stores 2/9 Music video by Kendrick Lamar, SZA performing All The Stars. (C) 2018 Aftermath Records


Downlord now

Kendrick Lamar, SZA - All The Stars