Showing posts with label kannywood. Show all posts
Showing posts with label kannywood. Show all posts
Tauraron fina-finan Hausa, Sadiq Sani Sadiq yayi murnar cikqrshi shekaru 6 da yin aure, a matsayin murnar wannan rana ya saka sako a shafinshi na sada zumunta inda ya yabi matar tashi ya kuma sa mata Albarka sannan ya shaida cewa basu taba samun tashin hankali 

Sadiq Sani Sadiq na murnar cika shekaru 6 da yin aure>Htdl

 Tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau kenan a wadannan hotunan nata da ta sha kyau, tubarkallah, muna mata fatan Alheri.

SABABBIN HOTUNAN JARUMA RAHAMA SADAU NA WANNAN SATIN

Tauraron mawakin mata, Ado Isa Gwanja kenan a wannan hoton nashi inda yake tare da matarshi, ya rubuta cewa, Alhamdulillah zama yayi kama da takalmin kaza sai madallah.

Kayataccen hoton Ado Gwanja da matarshi>>HTDL

Tauraron mawakin Hausa, Aminu Alan Waka ya aikewa da abokin aikinshi, Adam A. Zango da sako na musamman bayan kammala zaben shugaban kasa da aka yi a makon jiya, ga sakon kamar haka:
Ina tuna Abubuwa da yawa da suka hadamu da kai Adamu kama daga kalmar shahada da yaren Hausa da zama a yanki daya ga Uwa Uba Sana'a Iri daya. Ina tuna haduwarmu a tarukan zumunci na waka ko Dandalin karbar kambum karramawa da makamantansu, ina tuna yarda mutane ke harsashenmu tamkar uwa daya uba daya dun abinda ya Sameka ai ta bugo waya ana so a ji dahir daga gareni don zaton ni da kai abu daya ne, Saboda Sana'ar Waka. Me zai sa muga baiken juna a yayin da ra'ayinmu ya banbanta a kasuwar Bukata?
Ina taya ka jaje na tallar abinda ka dauko baka kai ga nasara ba, Kuma ina yi maka bushara da hakuri da wautar masu wauta, Ina karfafa tunaninka da yabawa musamman yarda ka bayyana fatan Alkhairi ga wanda Allah ya baiwa Nasara. Akarshe Ina fatan zamu hadu karkashin kishin kasarmu Nigeri kasa Daya Al'umma Daya. Mu kuma dawo fagen Fama na Sana'armu don gani wanne tudu wanne gangare zamu kai ga ci, Don cigaba da Samarwa kanmu Mafita a harkar taro sisi. Allah ya baiwa kasarmu zaman lafiya da bunkasar arziki, ya baiwa shugabanmu jagoranmu lafiya da nisan kwanan da zai waiwayemu da ayyukan cigaba a arewa.

Sakon Alan Waka ga Adam A. Zango bayan kammala zaben shugaban kasa>>HTDL

Bayan da wani shafin watsa labaran fina-finan Hausa ya wallafa cewa, manyan taurari biyu, watau Nafisa Abdullahi da Rahama Sadau sun yi fada akan Saurayi, Nafisar ta mayar da martani akan wannan labari.
Nafisar tace, Da kuna bin yadda ya kamata wajan nemo labarai, na tabbata da kun wuce matsayin da kuke yanzu.
A wani martanin na daban kuma bayan da wata ta tambayi Nafisar wai kunyi fada akan Saurayi?
Sai Nafisar ta bata amsar cewa, Toh ban sani badai, gani na yi kawai, Ni so nake ma in tambaya, Chachan bakine, ko kuma gisha-gishane?
A makon da ya gabata dai mun ga wani rubutun Nafisar da take caccakar wata da ta bayyana a matsayin me kokarin bin samarin wasu duk da tana nuna cewa ita tana da Aji. Saidai Nafisar bata bayyana ko da wa take ba.

Nafisa Abdullahi ta mayar da martani akan 'Fadanta da Rahama Sadau akan Saurayi'

Rahama Sadau Gradiate
 Tauraruwar fina-finan Hausa dana Turanci wato jaruma Rahama Sadau ta kammala karatun jami'ar da take yi a Cyprus, wanda ta samu shaidar kammala karatu daga jami'ar Eastern Mediterranean, Rahama ta bayyana hakane a shafukanta na sada zumunta inda tace kamin a kammala kamar ba za'a gama ba.

Muna tayata murna da fatan Allah ya sawa karatu Albarka. #BBCHAUSA
Ta kammala jamia

Rahama sadau


Rahama sadau

Rahama Sadau ta kammala karatun jami'a: Muna Mata Fatan Alkairi.

Maryam booth
Tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Booth kenan a wannan hoton nata da ta sha kyau, tubarkallah, muna mata fatan Alheri.

#hutudole

Zaka kalli hotonnan ka kara kallo saboda kyan da tayi

Sakon godiya
 Tauraruwar fina-finan Hausa da turanci, Fati washa ta godewa masoyinta inda tace, Masoyi na musamman, nagode da shigowa rayuwata, nagode da sani farin ciki Da ka yi.
Sakon godiya

Sakon Godiya Daga Jaruman Kannnywood: Fati Washa

Tauraron fina-finan Hausa, Ali Nuhu, Sarki na murnar cika shekaru 20 da fara yin fim a masana'antar fina-finan Hausa ta Kannywood. Alin ya kasance a masana'antar fim din Hausa tun shekarar 1999.
Ali Nuhu ya fito a fina-finai da dama da kuma bayar da gudummawa sosai a masana'antar Kannywood wanda dalilin haka ne yasa ake kiranshi da sunan Sarki, ya kawo jarumai da dama masana'antar wanda kuma suka daukaka, jarumai mata irin su, Rahama Sadau, Nafisa Abdullahi, da sauransu duk sun bayyana cewa Alin ne ya kawosu masana'antar.
Kusan indai a fim da Ali zaka ga jama'a na matukar so su kalleshi saboda irin farin jinin da yake dashi da kuma kwarewa a iya aiki.
Ali Nuhu ne na daya idan za'a jero fitattun jarumai na masana'antar Kannywood, ya dade tauraruwarshi na haskaka wa kuma da alama bashi da niyyar daina yin fim nan kusa.
Ali Nuhu na da mabiya sama da miliyan 1.5 a shafin Facebook sannan yana da mabiya sama da dubu 800 a shafin Instagram, yana kuma da mabiya sama da dubu 150 a shafin Twitter.
Kusan kowane jarumi yayiwa Ali Nubu mubaya'a da cewa shine sarkin Kannywood.
Muna tayashi murna da fatan Allah ya kara daukaka.

Ali Nuhu ya cika shekaru 20 a masana'antar Kannywood

 Tauraruwar fina-finan Hausa da turanci, Rahama Sadau ta cika shekaru 25 da haihuwa, jarumar ta fara sakin wadannan kayatattun hotunan nata dan yin murnar wannan rana, muna tayata murna da fatan Allah ya karo shekaru masu Albarka.


Rahama Sadau na murnar cika shekaru 25

 Taurarin fina-finan Hausa, Samira Ahmad, Hauwa Waraka, da Maryan Yahaya kenan a wadannan hotunan nasu da suka haskaka, sun sha kyau, tubarkallah, muna musu fatan Alheri.





Kalli Kayatattun hotunan taurarin fina-finan Hausa

Tauraruwar fina-finan Hausa da turanci, Rahama Sadau ta nuna saukin kai tare da wani masoyinta da ya roke ta ta tayashi murnar zagayowar ranar haihuwarshi.
Masoyin na Rahama yace, ki taimaka ki farantamin rai ta hanyar tayani murnar zagayowar ranar haihuwata, ai kuma sai gashi Rahamar ta tayashi.

Karanta yanda Rahama Sadau farantawa wani masoyinta rai

Tauraruwar fina-finan Hausa, Fati Washa kenan a wannan hoton nata inda take tare da abokin aikinta, Mansur Makeup, sun haskaka, muna musu fatan Alheri.

Fati Washa tare da abokin aikinta

 Tauraruwar fina-finan Hausa, Hadiza Gabon kenan a wadannan kayatattun hotunan nata da ta sha kyau, tubarkallah, muna mata fatan Alheri.

Kalli kayatattun hotunan Hadiza Gabon

 Tauraron fina-finan Hausa, Bello Muhammad Bello, General BMB ya sake fitowa inda ya mayar da martani ga masu sukarshi akan hoton da ya dafa kafadar abokiyar aikinshi, Rahama Sadau.
Hoton da Bello ya saka a shafinshi na sada zumunta ya jawo cece-kuce sosai inda wasu suka rika fadin be dace ba, Bello ya mayar da martani, saidai kuma ya sake mayar da wani martanin da wani salo na daban.
Bello yace yana kalubalantar masu sukarshi akan dafa kafadar Rahama Sadau da su fito su rantse cewa basu taba aikata laifin da yafi na dafa kafadar mace ba ko kuma ma basu taba aikata zunubi ba.
Saidai mafi yawa da suka bayyana ra'ayi akan wannan magana ta Bello sun bashi shawarar cewa ya bar maganar ta wuce kawai in ba haka ba ranshine zai ta baci a banza, a cikin su hadda abokiyar aikinshi, Ummi Zeezee.





Duk wanda be taba aikata laifin da ya fi na dafa kafadar mace ba ya fito ya gayamin>>General BMB

Tauraron mawakin mata da yayi aure kwanannan, Ado Gwanja ya gayyaci abokai ciki hadda, Adam A. Zango cin abincin dare gidanshi.
Adam A. Zangonne ya bayyana haka a dandalinshi na sada zumunta.
Muna musu fatan Alheri.

Ado Gwanja ya shiryawa Adam A. Zango cin abincin dare a gidanshi