YADDA AKE HADA KOSAN DANKALI DA NAMA

KAYAN HADI
  • Dankali
  • Nama
  • Kwai
  • Attaruhu
  • Albasa
  • Maggi
  • Gishiri
  • Man gyaďa
  • Fulawa ko garin busashen buredi
*YADDA AKE HADA WA*
Da farko ki wanke nama ki zuba a tukunya sai ki zuba maggi da gishiri ki tafasa sai ki kwashe ki zuba a turmi ki jajjaga tare da albasa da attaruhu idan yayi laushi sai ki kwashe a kwano ko roba,sannan ki dawo kan dankalin turawa ki tafasa yayi laushi sai ki murmushe shi ko kuma ki jajjaga a turmi sai ki kwashe shi a cikin kwanon da kika kwashe naman da kika jajjaga sai ki ďauko kwai ďanye ki fasa a kai, ki zuba fulawa ko garin busashen buredi a ciki ki sa gishiri da maggi ki juya sosai, ki ďauki farantin suya ki zuba man gyada ki ďora a kan wuta ki dinga ďiba kina zuba wa a cikin man gyada mai zafi idan ya soyu zaki ga yayi brown sai ki kwashe kiyi wa Oga yayi breakfast dashi.
KOSAN DANKALI
*KAYAN BUKATA*
  • Dankalin turawa 
  • Nama
  • Fulawa
  • Kwai 
  • Albasa 
  • Attarugu
  • Gishiri 
  • Maggi
  • Man gyada

*YADDA AKE YI*
Ki jajjaga albasa da attaruhu ki kwashe a kwano ko roba sai ki ďauki dankali ki tafasa ki zuba a turmi ki daka shi amma kar ya yi laushi sai ki kwashe a cikin kwanon da kika zuba jajjagen attaruhu da albasa ki tafasa nama shi ma ki daka a turmi duk ki hada da sauran kayan hadin ki juya, sai ki dinga mulmulawa kina tsomawa a ruwan kwai ki juya shi a cikin fulawa ki jefa a cikin man gyada mai zafi ki soya , akwai daďi matuka..

No comments