Tauraron mawakin Hausa, Nazir Ahmad, Sarkin Waka, yayi suna wajan baiwa mutane hakuri akan lamurran dake faruwa musamman na harkar gwamnati, sau da dama idan ya wallafa hoto a dandalinshi na sada zumunta yakan rubuta cewa adai kara hakuri ko kuma a ci gaba da hakuri.
To da alamadai shima hakurin nashi ya kare, domin kuwa a wani sako da ya wallafa yace a gayawa APC cewa, an musu laifi, amma ba zasu bayyana lafin ba yanzu tukuna, irinshi matasan Arewa duk da gudummuwar da suka bayar amma anyi watsi dasu ba'a gode musu to zasu nuna cewa su haifaffune.
Bayan wallafa sakon sai ra'ayoyin jama'a ya fara kwarara inda wasu suka alakanta wannan magana da Nazir yayi da cewa, mukamin da aka baiwa Rarara ne ya mai zafi shi yasa yake wannan magana, wasu kuwa sun dauke ta da zafi inda suka rika mayarwa da Nazirdin kalamai, hadda zagi dake nuna cewa da Buhari yake kuma be kamata ya sa kanshi a siyasa ba.
Ga dai kadan daga cikin ra'ayoyin da wasu suka bayyana akan wannan sako:




Bayan wadannan ra'ayoyi da mutane suka bayyana, Nazir ya mayar da martani inda yace wai su dama haka suke?, shifa be kira sunan kowa ba yace dashi yake amma gashi sunzo sun zaginshi saboda Buhari.
Nazir ya bayar da misali da Bukhari wanda ya ruwaito hadisai daga manzon Allah(S.A.W) inda yace, shi kanshi malamai suna hada hadisinshi da ayar Qur'ani suce be ingantaba ballantana Buhari dake tare da Osinbajo ace ba za'a mai gayara ba idan yayi kuskure.
Ya kara da cewa, shin wai da mahafin masu zaginshi ya zaga yaya zasu yi kenan?, ga masu cewa Nazirun yana hassada ne saboda mukamin da aka baiwa Rarara, ya basu amsar cewa shi be ma san da wannan magana ba sai a bakinsu, kuma shi Allah ya tsareshi da yin hassada akan abinda zai kare a Duniya, yace, ga manyan mutane da zaiyi hassada akansu sai shi(Rarara)?, ya kara da cewa ko shekara dari zaiyi akan mukamin da aka bashi ba zai samu irin abinda gareshi ba.
Nazir ya kara da cewa kai duk me binshi a dandalinshi na sada zumunta saboda Buhari daga yau ya dena, sannan kuma zasu zaunama suyi shawara akan zamansu a cikin jam'iyyar tunda abin haka yake.
Ya kuma shawarci masu zagin nashi da cewa su gyara lamarinsu, ba'a haka.

Duk me bina saboda Buhari daga yau ya dena>>Nazir Ahmad Sarkin Waka

Dan tsohon shugaban Libiya Muammar Gaddafi, Saiful Islam ya fasa kwai game da batun wafatin gyatuminsa.
Kamar yadda wasu kafafan labaran kasar Ivory Coat suka rawaito,a watan da ya gabata, wata mata mai suna Zayraf Aya hafaffiyar kauyen Gaddafi ta bayyana cewa,tsohon shugaban kasar Libiya wanda aka ce an kashe a shekarar 2011, mahaifi ne na 'yarta, kuma da ransa,bai mutu.
Matar mai shekaru 35 da haifuwa ta ce Gaddafi na nan da ransa amma ya rasa kafa daya sakamakon hare-haren bama-baman da aka kai masa, a lokacin aka nemi hambarar da mulkinsa.
Ta kara da cewa, a yanzu Gaddafi yana jinya amma da zaran ya samu lafiya zai koma kasarsa don ceto al'umarsa.
Da maneman labaran jaridun na Ivory Coast suka nemi ganawa da Saiful Islam sai ya ce da su,
"A hakikannin gaskiya a shekarar 2011, mahaifina ya jikkata, amma bai mutu ba,yanzu haka yana ci gaba da jinya.Ba zan taba gaya muku takaimaime inda yake ba,don gudun kar a cutar da shi.An mika mana mahaifinmu yayin da zuciyarsa ke ci gaba da bugawa,sai muka garzaya da shi asibiti a wani wuri na sirri, inda kawo yanzu yake ci gaba da jinya".
Milyoyin mutane daga sassa daban-daban na duniya, sun kalli bidiyon yadda aka yi wa Muammar Gaddafi kisan wulakanci.An yada bidiyon a shafukan intanet da na sada zumunta.Amma da yawa daga cikin 'yan adawan tsohon shugaban kasar Libiya,sun tabbatar da cewa wannan ba komai ba ne face farfagandar magoya bayan Gaddafi da nufin shafa musu kashin kaji.
Lokaci zuwa Lokaci iren iren wadannan labarai kan Muammar Gaddafi na kunno kai a wasu shafukan farko na jaridun nahiyar Afirka da ma kasashen Yamma,amma kawo yanzu babu wanda ya taba tabbatar da sahihancinsu.
Ayar tambaya a nan ita ce, shin da gaske ne Gaddafi na raye ?
TRThausa.

Ashe tsohon shugaban kasar Libiya, Gaddafi na nan da ranshi be mutuba


Domin kallon cigaban shirin dadin kowa na satin da ya wuce ku kasance damu domin kalla.
A Cikin wannan Satin
Yayin da Adama ta ci gaba da tsintarkanta a tsaka mai wuya, Bayan daKamaye ya iy mata korar kare daga gidansa a yanu ta fara
laluben hanyar da zata bi domin ganin an sulhunta tsakaninsu sai dai yunkurin neman sulhun tana kokarin jefa kanta a cikin wata sabuwar
sarkakiyar mai wuyar fita.

Downlord here

Dadin Kowa Sabon Salo Episode 63 Arewa24

Jarumar fina-finan Hausa, me tashe, Maryam Yahaya kenan a wadannan kayatattun hotunan nata da suka birge, tasha kyau, tubarkallah, muna mata fatan Alheri.


Kukalli sababbin hotunan maryam yahaya dasuka birge

Wata jaririya da aka haifa a jihar Texas ta kasar Amurka ta shigo Duniya da kafar dama inda ta samu aikin yi ranar da mahaifiyarta ta haifeta, iyayen wannan yarinya, Robert Griffin da mahaifiyarta, Falon Griffin suna kan hanyarsune ta zuwa Asibiti sai Falon taji cewa tana bukatar shiga bandaki.
Mijin ya tsaya a kofar wani sananen gidan sayar da abinci me suna, Chick-Fil-A amma sun tashi aiki da yake cikin darene, haka dole ya kwankwasa musu suka bude, saboda matar tashi ta bayyana cewa abinda take ji, ba zata iya jira har sai sunje Asibitin ba, matar tashi ta shiga ban dakin gidan sayar da abincin.
Jiyo ihun Falon daga bandakin yasa Robert yayi gaggawar kaimata dauki, yana shiga sai yaga ai haihuwace zatayi, har kan jaririyar ya fara fitowa, kamar yanda ya bayyana a labarin daya bayar a shafinshi na Fcebook.
Robert yace ganin haka yasa ya tabbatar da cewa babu inda zasu iya zuwa daga nan, sai ya fara gaya mata maganganun kwarin gwiwa a haka har ta haihu a cikin bandakin, inda yayi amfani da rigarshi a matsayin zanin rike jaririyar, ya kuma lura cewa, cibiyar jaririyar ta nade mata wuya har sau biyu, anan ma yayi dabara a warware mata.
Ma'aikatan jiyya sun iso gurin daga baya sannan aka tafi da jaririyar da uwarta Asibiti, a wajan rubuta takardar haihuwarta, an rubuta sunan mahaifin nata Robert a matsayin wanda ya bayar da gudummuwa wajan haihuwarta.
Su kuwa gidan sayar da abincin wanda sanannene yayi alkawarin ba jaririyar abinci har tsawon rayuwarta sannan kuma da zarar takai shekaru 16 zai dauketa aiki.

Karanta labarin jaririyar da aka dauketa aiki ranar da aka haifeta

Mahaifin tauraron dan kwallon Najeriya, Mikel Obi, Michael Obi ya bayyana cewa dan nashi fiye da shekaru biyar kenan be kirashi a waya ba amma masu garkuwa da mutane sun kamashi suna tunanin Mikel din na turo mishi makudan kudi.
Micheal yayi hira da jaridar Daily Trust ne inda ya bayyana yanda aka sace shi da kuma irin dangantakar dake tsakaninshi da dan nashi, kwanannan dai masu garkuwa da mutane suka sakeshi, karo na biyu kenan ana garkuwa dashi.
Ya bayyanawa Daily Trust cewa, suna cikin tafiya da direbanshi zuwa wani taron Iyali da zasu yi a Enugu sai kawai suka ji harbin bindiga, direbanshi yayi kokarin komawa da baya amma sai wata motar ta taho daga baya ta tare su.
Sun fitar dasu daga cikin motar inda suka nufi daji dasu sukai ta tafiya har gari ya waye.
Daga baya ya tambayesu me suke so ya basu suka ce mai miliyan dari, sun ji labarin danshi, Mikel yana aikomai miliyan Hamsin duk sati, yace nan ya gaya musu cewa shi miliyan biyu kawai gareshi a asusun ajiyarshi na banki, sukai ta dai ja in ja har takai miliyan goma.
Sun kira danshi, Toni, ya gayamai yaje banki ya amso kudi amma sai manajan bankin bayanan, sai yawa dayan danshi magana, Ebele, shi kuma sai ya kira Mikel, ta yanda aka samu kudin da aka baiwa masu garkuwa da mutanen kenan.
Da aka tambayeshi yaya dangantakar shi da dan nashi Mikel take, sai ya bayyan cewa, shekaru fiye da biyar kenan ko a waya baya kiranshi, yace, yayi iya yinshi dan ganin ya warware wannan matsala amma abu yaci tura, yace amma yana kiran mahaifiyarshi, shi kuma da ya ga haka sai ya sawa ranshi dangana yace indai zai ganshi a talabijin yana koshin lafiya to hakan ya gamsar.
Da aka tambayeshi amma wasu na cewa Mikel din ya kiraka, sai yace, Eh suna waya da mahaifiyarshi, kwanaki kadan bayan gasar cin kodin Duniya, sai ta ce min gashi mu gaisa, anan na amshi wayar muka gaisa na mai addu'a.
Ya kara da cewa lokacin da dan nashi ya zama dan kwallon Chelsea mutanen garinsu sun yi ta tayashi murna da fadin cewa ya warke, nasu ya samu. Akwai lokacin da yazo Abuja, mutanen kauyensu sukai ta murna aka buga fastoci da shiri na musamman akan tunanin cewa Mikel din zai karasa garin amma sai bai jeba, yace wannan abu yasa yaji kunya kamar ya nutse kasa, mahaifin na Mikel ya bayyana cewa, Mikel din na gayawa 'yan uwanshi cewa, wani lokacin sai ya daga waya da niyyar ya kira mahaifin nashi amma sai ya fasa.
Ya kara da cewa ko 'ya'yan na Mikel har yanzi bai taba ganinsu ba

Fiye da shekaru 5 kenan dana ko a waya baya kirana amma masu satar mutane suna tunanin yana turomin kudi>>Inji mahifin Mikel Obi