Wannan hoton wata kiristace da aka kama sanye da Hijabi da Nikabi tayi satar kayayyaki ta boye a ciki, bayan da aka kamata aka cire hijabin da nikabin data saka sai aka ga kros a wuyanta kuma ta tabbatar da cewa ita kiristace.
Lamarin ya farune a jihar Sakkwato kamar yanda wani me shafin Facebook ya bayyana, ya kara da cewa tana hannun 'yan sanda dan daukar hukuncin da ya dace a kanta.

Kalli wata kirista da akama kama tayi sata sanye da Hijabi da Nikabi

A yaune shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da shugaban kasar Amurka, Donald Trump a fadarshi ta Whitehouse, wanan hoton na daya daga cikin hotunan da aka dauka lokacin ganawar shuwagabannin kuma ya dauki hankulan jama'a, tauraruwar fina-finan Hausa, Hadiza Gabon ta bayyana cewa bata taba ganin Trump yayi irin wannan murmushinba, yaga tauraro shugaba Buhari.
Ga abinda ta bayyana kamar haka:

'Shugaban Amurka, Trump yayi murmushin da be taba yiba saboda murnar haduwa da shugaba Buhari'>>Hadiza Gabon

Sheikh Dahiru Usman Bauchi, yama ganin cewa za'a iya yin auren mut'ah, yayin da bukatar ýa mace ta kama mutum, kuma baya kusa da iyalinsa,
"Idan Tafiya Ta Kama Musulmi Yayi Nesa Da Iyalanshi, Sannan Sha'awar Mata Ta Kama Shi, To Da Yayi Zina Gara Yayi Auren Mut'ah" -
Sheikh Dahiru Bauchi ya fadi hakan ne A Karatun Littafin Muwaddah Wanda Ya Saba Gabatarwa A Gidan Rediyon Tarayya Na Kaduna.
Shin ko hakan ya dace da karantarwar addinin musulunci?
Ko kuma menene banbanci tsakanin zina da auren mut'ah????

Matafiyi zai iya yin auren mutua a maimakon zina, -Inji Sheikh Dahiru Bauchi

Albishirin ku yan uwa yau mun sake kawo muku Sabuwar wakar Rarara me suna Buhari 4+4 domin jindadin ku da nishadantar daku gaskiya wakar ya kayatar kada na cika ku da surutu ko sauke wakar kusha sauraro lafiya.

Downlord mp3 here

Sabuwar Wakar Rarara Buhari 4+4 New Song

 Tauraruwar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi ta mayarwa da wani mutum martani me zafi yayin da ya gaya mata cewa 'Gaskiya Nafi kin fara tsufan' , da alama Nafisa bata ji dadin wannan magana ba, ta mayar mishi da martanin cewa dodanniyace ni da bazan tsufa ba?.
Ta kara da cewa ko ta gidama yarinya take har yanzu?, in kuma yarinyace to zanzo ta bani abinda tasha nima insha.
Bayan wannan martani da Nafisa ta mayarwa da wannan bawan Allah be dai kara cewa uffan ba, kuma wasu sun bata shawarar cewa ta daina kula irin masu wadannan maganganun.


'ko ta gidama yarinya take haryanzu?'>>Nafisa Abdullahi ta mayarwa da wani daya ce mata ta fara tsufa martani

Tauraruwar fina-finan Hausa da turanci, Rahama Sadau ta karyata labarin da wasu kafafen sadarwa suka buga na cewa ta yiwa Atiku Abubakar kaca-kaca akan martanin da ya mayarwa da shugaba Buhari kan maganar da shugaba Buharin yayi akan matasa, Rahama tace bata fadi hakaba.
A cikin labarin an ruwaito cewa Rahama ta cewa Atiku sune suka bata Najeriya kuma In Allah ya yarda Shugaba Buhari ne zai ci zaben shekarar 2019.
Amma Rahamar tace bata fadi wannan magana ba kuma tayi Allah ya isa.
Rahama ta kara da cewa inda sun sameta da tana da labarai da dama da zata basu amma ba akan siyasa ko kuma wani dan siyasa ba.
Ga abinda ta rubuta a dandalinta na Facebook kamar haka:
"Who did this pls?!! Now this is one of the disadvantage of MEDIA!!! FAKE NEWS all over!!! I can’t remember when I had this interview with either of you... Dokin Karfe TV and Najeriyarmu A YAU....
You guys should have come to me if you’d ever need any news to carry on me!!! Trust me, I have plenty to share with you but NOT ON ANY POLITICIAN OR POLITICS. Why publish fake!! Meye ribar yin haka?!! Allah ya isa!!!!!"

Rahama Sadau ta karyata labarin da ake yadawa akan ta na cewa ta yiwa Atiku Kaca-kaca

 Tauraruwar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi kenan a wadannan hotunan nata da ta dauka a kasar Amurka, tasha kyau sosai, a cikin hotunan hadda wanda ta dauka a kafar sadarwar CNN.
Muna mata fatan Alheri.


Kukalli zafafan hotunan jaruma nafeesat abdullahi dasuka burge

Da alama maganar da shugaban kasa yayi akan matasa ta dauki wani sabon salo, musamman tsakanin masu sana'ar a daidaita sahu/keke Napep, inda wasu har sun fara rubutun kalmar 'Cima Zaune' a bayan keken nasu kamar yanda ake iya gani a jikin wannan hoton.

'Yan Adaidaita sahu sun fara rubuta kalmar 'Cima Zaune' a jikin kekensu