Wannan wata sabuwa waka wanda shahararren mawakin zamani na siyasa dauda kahutu rarara yayi Wanda a cikin wannan wakar nasan zata kayatar da ku.

Wanda nasan cewa duk masoyin baba buhari zaiyi murna jin wannan wakar ta rarara.

Gadan daga cikin baitoci
Kubani kidan da binne pdp

Baba buhari two times

Zabin talakawa Ikon Allah
Bazan baku zakin miyar ba.

Ayi sauraro lafiya.

Downlord mp3

Source: hausaloaded

Sabuwa Wakar Rarara - Kubani kidan Da Ɗa Binne PDP

Babban malamin addinin musulunci na kasar Masar, Shawki Ibrahim Abdel-Karim Allam, ya fitar da wata fatawa inda ya haramta amfani da kudin intanet na Bitcoin.
A fatawar da a ka wallafa ranar Litinin, Shawki Allam ya ce ba a yarda musulmai su siya ko su siyar ko kuma su biya haya da wannan tsari na Bitcoin ba.
Ya ce amfani da kudin intanet na da hadari domin zai iya haifar da zamba da yaudara, kuma kasancewar tsarin maras tabbas, ya na iya cutar da jama'a da ma kasashe.
Babban malamin ya ce sai da ya nemi taimakon masana tattalin arziki kafin ya yanke wannan hukunci.
Mene ne Bitcoin?
Bitcoin na da abubuwa biyu da suka bambanta shi: kudin intanet ne kuma ana ganinsa a matsayin wani abu da za a iya amfani da shi a madadin kudi.
kan intanet sabanin kudaden takarda ko sulalla da ke aljihunka
Duk da cewa akwai wasu na'urorin bayar da kudi (ATM) na musamman da ke bayar da Bitcoin, ya fi dacewa a yi tunaninsu kamar 'yan kudaden intanet.
Kuma babu gwamnati ko kuma bankin da ke buga Bitcoin.
Wannan na nufin "ba kudin da doka ta amince da shi ba ne, ba za ka iya biyan harajinka ko kuma ka yi amfani da shi wajen biyan bashi ba", in ji Dr Garrick Hileman na fannin koyar da kasuwanci a jami'ar Cambridge.
Ana samar da Bitcoins ne ta wata hanya mai sarkakiya da ake ce wa "haka" (wato "mining, a Ingilishi), sannan wasu komfuntoci da ke hade a fadin duniya za su saka ido kansa.
Ana samar da kimanin Bitcoin 3,600 a ko wace rana - kuma a halin yanzu akwai kimanin kudin miliyan 16.5 da ke yawo.
Sai dai kuma, kamar dukkan kudade, darajarsa ya dangata ne ga iya kudin da mutane suke son saye shi tare da sayar da shi.

bbchausa.

Haramcin Kudin Internet Bitcoin - Fatawa

Bayan da wani shafin watsa labaran fina-finan Hausa ya wallafa cewa, manyan taurari biyu, watau Nafisa Abdullahi da Rahama Sadau sun yi fada akan Saurayi, Nafisar ta mayar da martani akan wannan labari.
Nafisar tace, Da kuna bin yadda ya kamata wajan nemo labarai, na tabbata da kun wuce matsayin da kuke yanzu.
A wani martanin na daban kuma bayan da wata ta tambayi Nafisar wai kunyi fada akan Saurayi?
Sai Nafisar ta bata amsar cewa, Toh ban sani badai, gani na yi kawai, Ni so nake ma in tambaya, Chachan bakine, ko kuma gisha-gishane?
A makon da ya gabata dai mun ga wani rubutun Nafisar da take caccakar wata da ta bayyana a matsayin me kokarin bin samarin wasu duk da tana nuna cewa ita tana da Aji. Saidai Nafisar bata bayyana ko da wa take ba.

Nafisa Abdullahi ta mayar da martani akan 'Fadanta da Rahama Sadau akan Saurayi'

DA DUMIDUMINSA
Jami'an Tsaro Sun Cika Hannu Da Buba Galadima
Jami'an tsaro sun damke kakakin yakin neman zaben jam'iyyar PDP, Injinya Buba Galadima a yau Lahadi.
Majiyar ta DAILY NIGERIAN ta bayan cewa daya daga cikin 'ya'yan Buba Galadima ta tabbatarwa manema labarai cewa jami'an tsaro sun damke mahaifinta a unguwar Wuse 2 dake birnin tarayya Abuja.
Rariya

JAMI AN TSARO SUN DAMKE BUBA GALADIMA

Rahama Sadau Gradiate
 Tauraruwar fina-finan Hausa dana Turanci wato jaruma Rahama Sadau ta kammala karatun jami'ar da take yi a Cyprus, wanda ta samu shaidar kammala karatu daga jami'ar Eastern Mediterranean, Rahama ta bayyana hakane a shafukanta na sada zumunta inda tace kamin a kammala kamar ba za'a gama ba.

Muna tayata murna da fatan Allah ya sawa karatu Albarka. #BBCHAUSA
Ta kammala jamia

Rahama sadau


Rahama sadau

Rahama Sadau ta kammala karatun jami'a: Muna Mata Fatan Alkairi.

Wata halitta da jama'a suke tunanin Aljani ne ya bayyana cikin suffar dattijo 'WAI' ya sauko daga sararin samaniya a kan keke, lokacin da ake taron Kwankwasiyya a karamar hukumar Birni.

Da mutane suka tambaye shi, me ya kawo ka? Sai yace "Nazo ne domin naga Kwankwaso"

#Sarauniya.

KALLI ALJANIN DA AKE TUNANIN YA HALARCI TARON KWANKWASIYYA

Maryam booth
Tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Booth kenan a wannan hoton nata da ta sha kyau, tubarkallah, muna mata fatan Alheri.

#hutudole

Zaka kalli hotonnan ka kara kallo saboda kyan da tayi

Sakon godiya
 Tauraruwar fina-finan Hausa da turanci, Fati washa ta godewa masoyinta inda tace, Masoyi na musamman, nagode da shigowa rayuwata, nagode da sani farin ciki Da ka yi.
Sakon godiya

Sakon Godiya Daga Jaruman Kannnywood: Fati Washa