Home / All Post
Wani bawan Allah ya duba dandalin tauraruwar fina-finan Hausa, Hadiza Gabon inda yayi ikirarin gano kuskure a rubutun da tayi na cewa ita 'yar fim ce a turanci, watau Actor.
Saidai Hadizar ta nemo cikakkiyar ma'anar wannan kalma ta Actor ta nunawa wannan da ya mata gyara inda ta ce bari in taimakeka da wannan,kasan ilimi kogine.
A dazune muka ga wayar da aka fito da ita dan yi wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari kampe din takarar zaben 2019 wadda take dauke da hotonshi dana jam'iyyar APC, a wadannan hotunan shima abokin takarar Buharin, Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ne a wayar da shima zai yi kamfe da ita me dauke da hotonshi dana jam'iyyar PDP.
Lallai wannan karin 'yan Najeriya zasu samu kyautar wayoyi.

A wata hira da aka yi dashi a gidan talabijin na TVC News da wani shafin Instagram ya wallafa, dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana cewa tuni ya daina bin mata.
Me hirar dashi ta tambayeshi cewa, kasan a Afrika akan ce idan mutum baya shan taba ko giya to yana bin mata, kai wanne kake yi? Sai Atikun ya bayar da amsar cewa baya shan taba kuma baya shan giya sannan ya daina bin mata.
Me hirar dashi ta sake tambayarshi cewa, shin ka iya soyayya kuwa, kasan cewa matanka sun fi saninka fiye da kowa.
Sai ya bayar da amsar cewa, Eh na iya soyayya domin bana jin kunyar sumbatarsu, rungumar (matana) a bainar jama'a.
A kwanakinnan jaruman fina-finan Kasar Amurka mata sun fito da wani mataki da suka wa lakabi da Metoo wanda suke fallasa masu shirya fina-finai da kuma wasu manyan jarumai maza da suka yi lalata da su ba da son ransu ba dan su saka su a fim.
Abin bawai kan jaruman fim kadai ya tsaya ba hadda mawaka da wasu kadan daga cikin al'ummar gari.
Wannan abu ya tsallaka masana'antar fina-finan Indiya inda can ma wasu jarumai mata suka fara fallasa mazan da suka yi lalata da su ba da son ransu ba.
Tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau ta yi fatan cewa zata so ace suma a masana'antar fina-finan Hausa su kwaikwayi irin wancan tsari.
Rahama ta jinjina maganar, watau inda da za'a yi hakan ' Tabdijam!!!'
Wani daga cikin mabiyanta yace, wasu kam yana ganin sharri ake musu a irin wannan abu.
Saidai Rahamar ta bashi amsar cewa, duk wanda aka yiwa sharri ai yana da bakin karyatawa, kuma irin wannan abu yana faruwa a duk wata masana'antar shirya fim ta Duniya.

Tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango kenan a gurin liyafar cin abinci ta bikin Ado Gwanja da sahibarshi, Maimunatu, ya nishadantar da jama'ar gurin.
Itama dai jarumar fim din Hausa, Maryam Yahaya da sauran wasu abokan aikin Gwanja sun halarci wajan shagalin, muna fatan Allah yasa ayi a gama lafiya.

Tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango ya yi wani rubutu a dandalinshi na sada zumunta da ya dauki hankulan abokan aiki da masoyanshi.
Abinda Adamun ya rubuta shine, Gaskiya duk Duniyarnan babu macen da zata fahimceni.
A watan daya gabatane mujallar Fim ta wallafa labarin cewa, Adamun ya saki matarshi, labarin da shima ya jawo cece-kuce sosai akan Adamun.
Saidai kwanaki kadan bayan wancan labarin na mujallar fim, Adamu ya wallafa a shafinshi cewa ya saiwa matarshi sabuwar mota, hakan ya saka wasu masoyanshi cikin rudani da tunanin kodai wancan labari na Mujallar fim ba gaskiya bane?
Wani abu dai da za'a iya lura dashi shine tunda labarin sakin matar tashi ya watsu, ba'a sake ganin Adamun ya wallafa hotonta a dandalinshi na sada zumunta ba.
Yanzu dai wannan magana da yayi tasa da dama daga cikin masoya da wasu daga cikin abokan aikinshi suka rika bashi baki da cewa bai kamata ya rika fadin irin wannan magana ba.
Koma dai menene sai muce komai yayi zafi maganinshi Allah.

Subscribe to:
Posts (Atom)